NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba ɗaya Zahrah jitayi jikinta yayi laƙwas,  take marin da ta shararawa Dr Sadeeq akan fuskarsa ya dawo mata, wani irin faɗuwar gaba taji, ko kaɗan batayi tunanin zata iya kai hanunta jikinsa da sunan duka ba, amma a daren jiya ɓacin rai yasanya idanunta rufewa, harta iya ta mare sa batare da tayi tunanin komai ba, tabbas komai yayi mata bai cancanci mari daga gareta ba.

Gaba ɗaya kasa sakewa a cikin makarantar Zahrah tayi a wannan ranan, dole ta tattara yanata yanata ta dawo gida.

Zaune take jigum akan tabarma yayinda hannuwanta ke dafe da ƙuncinta,  idan  da za’a ce za’a kasheta idan bata faɗi, tunanin me take ba, to tabbas da sai dai a kashetan, amma ita kanta batasan  tunanin mai take ba.

Inna da fitowarta kenan daga bayi, hanunta riƙe da buta, kama ƙugu tayi,  haɗe da maida  kallon ta zuwaga  inda Zahrah ke zaune tayi jigum.
  “Wai lafiyanki kuwa Zahrah? meke damunki ne? tun safe haka kike sukuku, yanzu kuma kinyi tagumi tamkar wacce akamawa mutuwa, kodai halinki na da, kike son dawowa dashi ne? to wallahi bazan ɗau wannan iskancin ba, tun wuri ma kisani!” Inna taƙare maganar cikin faɗa faɗa.

“Ko ɗaya bahaka bane Inna, narasa taya zan ɓullowa matsala ta ne!” Zahrah tafaɗa cike da sanyin murya.

“Matsala! wace irin matsala kuma?” Inna ta tambaya cike da son jin gulma.

“Inna wai Likita ne yace zai aure ni !” Zahrah tafaɗi hakan cikin sarƙewar murya.

“Likita yace zai aure ki!”  Inna ta maimaita maganan  cikin ƙaraji haɗe da sanya duka hannayenta biyu ta dafe ƙirjinta. 

Kai kawai Zahrah ta’iya gyaɗa mata domin zuwa lokacin har ƙwalla sun soma cika mata ido.

Wani irin guɗa Inna tasa, haɗe da sake kama ƙuƙu,  “Lallai kuwa, wannan babban al’amari ne, mai ɗauke da tarin farinciki, Allah yasa dai kin amince masa?” cike da zaƙuwa inna taƙare maganar.

“Bazan iya ba Inna, kuma ma ni yanzu babu batun aure a tsarina,zan zauna kawai naƙare rayuwata cikin ƙaddarata!” Zahrah tafaɗa lokacin da hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa.

Salati Inna ta sanya, haɗe da soma tafa hannaye.
“Amma kedai Zahrah anyi shashar banza, sokuwa marar wayo, ashe dai baki da hankali,  yanzu a yanda kike ɗin nan, kin samu ance za’a aure ki a haka, kice wai baki amince ba, lallai yau nasake tabbatar mawa da kaina cewa ke wawuyace,  to wlh baki isa ba, baki isa ɓarar mana da alkhairan da zamu samu ba, aure dole ko kina so ko bakya so, wato kinfiso kita zama damu, goɗo goɗo dake  ba aure ko, to kisa aranki cewa aurenki da likita ba fashi, dole!”

“Babu wanda zai mata dole!” Muryan Baffa dake shigowa cikin gidan yakaraɗe kunnuwansu.

“Maikake shirin faɗa ne malam, kakosan me ta aikata kuwa, Likita fa yace yanason aurenta amma taƙi?”

“Ƙwarai kuwa duk na saurari zancen ku, magana ta gaskia Salame, baza’ayiwa yarinyar nan dole ba, yanzu lokacin ta ne, yakamata a bar rayuwarta tasha iska hakanan!” Baffa yafaɗi maganar sanda yayi mawa kansa masauƙi akan wani ɗan dakali dake tsakiyar gidan.

“Laaaa shikenan kuma, kakosan abun da kake cewa? kana nufin zuba mata idanu zamuyi, ba mu isa mu sata dole ba? wani shan iska kake ƙoƙarin samawa rayuwarta, sanin kankane cewa babu wani wanda zaizo yace zai jajiɓeta a yanda taken nan, don kawai likita ya rufa mata asiri yace zai aureta, saikayi ƙoƙarin hure mata kunne.”

“Tashi ki koma ɗakinki kinji Zahrah, kiyi tunani mai kyau, idan kin yanke hukunci to kisanar dani!” Baffa yafaɗa cike da kulawa.

Cikin rashin ƙarfin jiki haka Zahrah ta koma cikin ɗakinta, yayinda take jiyo bala’in Inna a tsakar gida. 
  Jingina bayanta tayi da bango, haɗe da lumshe idanunta,    saiyanzu take jin cewa bata kyautawa Doctor Sadeeq ba, amma kuma shima baikyautu ace yazo mata da magana mai nauyi kamar wannan ba,  ko da wasa bata taɓa kawowa a ranta cewa wani zai sota anan kusa ba,  gaba ɗaya ta cire soyayya a tsari da jerin rayuwarta, tabbas sai dai ta yaudari kanta, amma tasan bazata taɓa ƙara son wani ɗa namiji ba a rayuwarta,   ta yarda da shawaran da Husnah ta bata, amma kuma abune mawuyaci, tarayyanta da Dr Sadeeq yazama mai ɗorewa, shin dagaske aurenta yakeso yayi koko shima wata manufartasa yakeson cimmawa? tatambayi kanta tambayar da  bata da amsa, “Idan bakiyi aure ba, haka zaki dawwama Zahrah?” wata zuciyarta tayi mata wannan tambayar.   hawayene suka shiga gudu akan fuskarta, lalllai akwai babban ƙalubale a gabanta.

Zaune yake akan derny table ɗin dake tangamemen falon Hajiyar tasa, plate ɗin abinci ne aje a gabansa,  yayinda yake juya spoon ɗin dake cikin abincin dake gaban nasa a  hankali,  kusan mintuna 10 kenan da kawo masa abincin, amma yakasa koda kai loma ɗaya ne na abincin  bakinsa, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya garesa.
Cike da  tuhuma Hajiya da tun ɗazu take kallon sa tace
“Wai meke damunka ne Sadeeq? gaba ɗaya yanayinka ya sauya, kowa yaganka yasan cewa kana cikin damuwa? gashi nace kaje gidan su Saleema, amma kayi banza da maganan bakaje ba har yau”

Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga mahaifiyar tasa.  
“Inada damuwa Hajiya!” yafaɗi hakan cikin sanyin murya.

“Subahanallah! damuwa kuma Sadeeq, damuwar me?”  Hajiya ta tambaya cike da kulawa, Allah yasani tana matuƙar son ɗan nata.

“Nasamu wacce nake so ne Hajiya!” Sadeeq yafaɗa cikin ɗar ɗar, don baisan ya Hajiyar tasa zata ɗauki al’amarin ba.

“Kasamu wacce kake so? wani irin magana ne wannan, wato so kakeyi kamai dani ƙaramar mace ko, to wallahi baka isaba, bazai taɓa yiwuwa ba, nariga dana gama magana da iyayen Saleema, har ƙanin mahaifinka yashigo cikin lamarin, saboda haka  wannan batun kama dainasa tun kafun ranka yakai ƙololuwa wajen ɓaci, banason shirme!” Hajiya tafaɗi maganar a fusace, haɗe da tashi tabar masa falon.

Tabbas dama yasani ko da Zahrah ta amincewa aurensa, to balalle ne Hajiyarsa ta amince masa ba, amma yasan cewa  yanamawa Zahrah so mai tsanani, kuma insha Allah, zai aure ta ya rayu da’ita har zuwa ƙarshen rayuwarsa, domin yaji hakan a jikinsa.

(Tofa readers kunji abun da Hajiyar Dr tace, shi kuma kunji abun da yace, koya zata kaya oho…. Kuyi haƙuri wlh yau ina busy! Shiyasa na muku kaɗan.)

        7/December/2019

*Voted,Comment, and Share please….. Follow me on Wattpad @fatymasardauna
????????????????????????????????????????

         SHU’UMIN NAMIJI !!

      Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

”'{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

    
        WATTPAD
   @fatymasardauna

Editing is not allowed????

  Chapter 50 to 51

Cikin rashin kuzari yamiƙe haɗe da nufar hanyar barin falon, ko kaɗan babu nutsuwa acikin zuciyarsa, ko sake bi takan abincin nasa baiyi ba, haka yafice daga cikin falon. kaitsaye ɓangarensa yanufa. Shirya kansa yayi cikin riga da wando na suit. kaitsaye asibiti ya wuce domin kuwa akwai wasu patient da zai gani. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button