SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba ɗaya tunanin Zahrah ya kulle, hartakai ta kawo ko makaranta taje ma bata da wani aiki saina tunani, ko karatun ma da ake koyar dasu bata fahimta, abubuwane sukai mata yawa, tayi matuƙar danasanin marin da tayi mawa Dr Sadeeq, haƙiƙa idanunta sun rufe, batare da tayi tunanin komai ba ta yanke hukunci, sai dai kuma har yanzu tunaninta daya gushe bai dawo gareta ba, takasa yanke hukunci, haka kuma takasayin tunani mai kyau, saidai tayarda da abu ɗaya. shine Doctor Sadeeq sam basa’an auren ta bane, yafi ƙarfinta. Yau kimanin kwana huɗu kenan da faruwar haka a tsakaninsu, tundaga wannan daren kuwa harzuwa yau, Dr baisake zuwa gareta ba, saidai fa kullum safiya, yana turo drivern sa akan yaɗauketa yakaita makaranta. amma zancen dai ɗayane, bata taɓa yarda tashiga motar, koma sauraran driver’n nasa batayi.
Dariya sosai Mahmud yashiga yi, a lokacin da yagama jin matsalolin abokin nasa, haƙiƙa Sadeeq yabasa dariya, ko da wasa bai taɓa tunanin wai Namiji kamar Sadeeq zaiji tsoron furtawa mace kalmar soyayya ba.
Tsuka Dr Sadeeq yaja haɗe da ɓata fuska cike da takaicin dariyan da Mahmud ɗin ke masa yace
” Bawai nafaɗa maka matsalata bane don kasani a gaba kayita min dariya ba, mafita nake nema Mahmud, gaba ɗaya kaina ya kulle, inasonta banakuma tunanin zan’iya barinta, amma kuma naga alamomin cewa zan rasata a fili!” Dr Sadeeq yafaɗi maganar cikin son abokinnasa ya ƙarfafa masa guiwa.
Ƙoƙari Mahmud yayi wajen tsaida dariyar tasa haɗe da gyara zama
“Yazama dole nayi maka dariya Sadeeq, a matsayinka na likita bokan turai, ka kasa jure zafin soyayya, amma kuma ko kaɗan banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai ƙalubale a gabanka!” Mahmud yaƙare maganar yana mai waina pen ɗin dake riƙe a hanunsa.
“Wani irin ƙalubale kenan Mahmud?” Dr Sadeeq yatambaya cike da zaƙuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.
“Nasara ko kuma akasinta, sune babban ƙalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaɗu sosai, saboda nasan abokina ya’iya zaɓe!” Mahmud yafaɗi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.
“Bazaka taɓa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki.” Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai shafa suman kansa.
Ƴar ƙaramar dariya Mahmud yayi haɗe da ɗaukan cup ɗin juice ɗin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.
“Babu amfanin ƙara tada zancen a gareta Sadeeq, tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake ɗago mata da zancen inaga haka zaifi!” Mahmud yafaɗi hakan cike da son ƙarfafamawa abokinsa guiwa.
Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe, haɗe da haɗiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa, domin kuwa da gaba ɗaya kansa ne ya kulle.
“Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taƙi amsata, sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!” Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin ɗar ɗar.
Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaɗai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma ɗar ɗar.
“Yanaga jikinka gaba ɗaya yaɗau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?” Mahmud yatambaya cike da shaƙiyanci.
Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja, haɗe da miƙewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baƙin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.
“Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka ƙoshi, ai nine nakawo kaina office ɗinka, kana da right ɗin da zaka iyamin komai” Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit ɗin dake jikinsa.
Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office ɗin Mahmud ɗin.
Cikin ɗan kuzarin da yasamu yake tuƙa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wani haɗaɗɗen riga da wando na jeans masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare. Makullin motarsa ya ɗauka haɗe dasakai yafice daga cikin ɗakin.
Zaune take akan ƴar katifarta, daga ita sai wata riga marar nauyi, jakan kayan shafanta ne aje a gabanta, da’alama daga wanka tafito, domin kuwa wani sashi na jikinta ɗauke yake da danshin ruwa. Kallo ɗaya zakai mata kafuskanci irin ramar da tayi lokaci guda, gaba ɗaya ta zabge ta faɗa, hips da breast ɗin tane kawai suke a cike a jikinta. A hankali take shafa Vaseline ɗin dake riƙe a hanunta, Yanayin yanda take shafa vaseline ɗin idan ka gani, kace dole akai mata. tana gama shafa mai ɗin, ta murza powder kaɗan akan fuskarta, haɗe da shafa kwalli a cikin idanunta, take fuskarta ta tasakeyin fayau, yayinda idanunta, suka sake bayyana girmansu a fili,kasancewar kwallin yana taimakawa wajen bayyana girman ido.
Kallonta tamayar kan ɗan ƙaramin agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe 5 na yamma kenan, kuma dai dai lokacin sukayi da Husnah cewa zataje ta sameta a gida. Cikin rashin kuzari, ta miƙe haɗe da ɗaukan kayanta riga da sket na atamfa tashiga sanyawa, duk da cewa atamfar mai sauƙin kuɗi ne, amma hakan baihana ta yi mata kyau a jikinta ba. Wani irin zazzaɓi takeji yana sanɗan jikin ta, idan ba don tariga da tamawa Husnah alƙawarin cewa zata zo yau ɗin ba, to tabbas da ta ɗage zuwa gidansu Husna’n saboda bata wani jin daɗin jikinta, takumasan cewa damuwace kurum tayi mata yawa.
Inna ce tashigo cikin ɗakin, adai dai sanda Zahrah ta gama sanya hijab ɗinta.
“Au ashema kinsan da zuwansa kenan?” Inna tatambaya tana mai ƙarewa Zahrah kallo.
“Banganeba Inna, zuwan waye kuma?” Zahrah taje fawa Inna tambaya cikin rashin fahimtan inda kalaman Inna’n suka dosa.
“Naga kinshirya tsab kamar kinsan da zuwansa, to koma dai menene kije yanajiranki a waje!” Inna tafaɗi hakan tana mai ƙoƙarin barin ɗakin.
“Waye Inna? kuma ni shirin nan da kika ga nayi, gidansu Husnah zani, amma waye ke nemana ?” Zahrah takuma tambaya cike da son ƙarin bayani.
“Waye kuwa zaizo neman ki a yanda kike ɗinnan, ai sai dai shiɗin da har ya yarda zaiyi JIHADI ya aure ki a haka, amma wai saboda son zuciya da butulci irin naki, kike neman watsa masa ƙasa a idanu!” Inna taƙare maganar dai dai sanda tayificewarta daga cikin ɗakin.
Wasu irin siraran hawayene suka samu nasaran gangarowa daga cikin idanun Zahrah, tabbas gaskia Inna ta faɗa, babu wani mai nemanta sai shi ɗin shi kaɗai, kuma tabbas tayadda shima JIHADI yayi kamar yadda Inna tafaɗa, ashe dagaske ne itakam ƙaddaranta tayi mata mummunan zane a goshinta, saurin share hawayenta tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin.
Tsaye yake a jikin motarsa yayinda kansa ke duƙe a ƙasa, ɗan makullin motarsa ce riƙe a hanunsa yana kaɗawa, wannan karon kam sosai yake yaƙi da zuciyarsa don bayaso tasake sanya masa tsoro kokuma ɗarɗar.