SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali take taku cike da nutsuwa har ta ƙaraso garesa, ɗan nesa dashi ta tsaya haɗe da yimasa sallama cikin sassanyar muryarta wadda bata fita sosai.
Lumshe idanunsa yayi haɗi da buɗesu a lokaci guda, badon komai ba sai don yanda sassanyar muryarta ta daki jiki da zuciyarsa.
“ZAHRAH!” yaƙira sunanta cikin murya marar fidda ƙaƙƙarfan sauti.
“Um!” Zahrah ta amasa masa batare da ta’iya motsa bakinta ba, haka kuma kanta a duƙe yake tunda tazo bata’iya ɗaga kai ta kallesa ba.
Kallonta yashiga yi tundaga ƙasanta har sama, tabbas duk da cewa a cikin hijab take, amma hakan bai hanasa hango rahamar da tayi ba, take yaji zuciyarsa tayi sanyi, tausayinta yasake kamasa.
“Inaso kimini iso cikin gida, inaga maganar mu acan zaifi, domin ina buƙatar zama!” yafaɗa cike da ƙosawa da tsayuwan da yakeyi.
Sumi sumi haka ta juya ta nufi cikin gida, harta shige cikin gidan bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, “Wallahi Zahrah ta haɗu, komai nata mai kyau ne!” yafaɗi hakan a fili, cike kuma da shauƙin soyayya.
Jim kaɗan Zahrah tafito, tana mai wasa da yatsun hanunta, “Kashigo!” kawai ta’iya furtawa cikin murya mai sanyi. Tana gaba yana biye da’ita haka suka doshi cikin gidan.
Katuwar tabarma tabaje musu a hanyar zaure, yayinda ta je ta zauna a can ƙarshen tabarman ta takure waje ɗaya, tamkar amaryar da aka kaita ɗakin miji yau yau, lol.
Murmushi Dr Sadeeq yayi bayan yayimawa kansa mazauni, dole dai shi zai ci gaba da zama jarumi ako da yaushe.
” Miye haka? ai ko da yanka naman jikin mutane nake, ya kamata ace kin matso kusa dani, balle ma kuma ni ba’abun da nakeyi, ko na taɓa miki wani abune ?” Dr yafaɗi hakan cike da kulawa.
Saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, domin yadawo mata asalin Likitan da tasani, kuma gaba ɗaya ya sauya wasu ɗabi’un nasa.
Giransa ɗaya yaɗage sama, haɗe da cewa “Yadai, ko nayi wani sabon laifi ne akan wancan banda labari?”
Girgiza kanta tashiga yi ita kaɗai tamkar ƙadan garuwa, domin ita tama rasa maizata ce dashi domin kuwa da wani salon yadawo.
“Matso kusa dani mana!” yafaɗa cikin sanyin murya, mai ɗauke da lallashi.
Cikin rashin kuzari, ta koma tsakiyar ta barman ta zauna, bayan ta haɗa jikinta duka ta takure waje ɗaya.
Ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe haɗe da sanya hanunsa yashafi ƙasumbar dake kwance akan fuskarsa.
“Maiyasa zakisa kanki a damuwa Zahrah? yawan kuka dakuma yawan tunani marassa amfani, basa haifar da komai sai gajiyar da ƙwaƙwalwa, please banso kina wahalar da ƙwaƙwalwarki, nasan cewa abaya banine sila ba, amma yanzu nine sila.!” ɗanjim yayi kana yaci gaba da cewa…” Kiyi haƙuri Zahrah, nasan bankyauta ba, amma inaso kimanta komai, inaso ki fuskanci karatunki, ki maida hankali sosai kinji ƙanwata, bawanda zaimiki dole, ke mutumce kuma kowani ɗan adam yana da ƴanci, kema kina da ƴanci, saboda haka ki daina kuka kinji ƙanwar Likita!” Yanayin yanda yaƙare maganar kaɗai ya’isa yasanya zuciya hucewa daga cikin fushi.
Kuka kawai Zahrah ta fashe dashi mai sauti, domin kuwa sai yanzu nadaman abun da ta’aikata a garesa yadawo mata sabo fil. A hankali ta ɗago idanunta da suke ɗigan hawaye tamaida kallonta garesa, wannan fuskar ta mara? ta tambayi kanta, tabbas batayiwa kanta adalci ba, Dr Sadeeq baicancan ci mari daga gareta ba. kukane yakuma ƙwace mata, don batasan tayanda zata soma basa haƙuri akan abun da tayi masa ba.
Cike da damuwa ya dawo kusa da’ita, har suna iya juyo ƙamshin turaren juna.
“Subahanallah Zahrah kuka kuma? kinfasan banaso, kidaina kuka kinji, ki faɗamin idan ganina ne bakiso, yanzu zantafi Zahrah, nazo ne dama nabaki haƙuri akan abun da yafaru tsakanina dake, kiyi haƙuri Zahrah haka bazata….” Kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon Zahrah da ta sanya duka hannayenta biyu ta toshe masa baki.
“Dan Allah kada ka ƙasƙantar da kanka awajen wacce bata dace ba, bata kuma cancanta ba, bakaine yakamata kabani haƙuri ba, nice yakamata na baka haƙuri, bai kyautu ace na mareka ba, nayi nadama Doctor, dan Allah kayi haƙuri, bansan yanda zanyi ba ne banda zaɓi, kayafemin!” Zahrah ta ƙare maganar cikin kuka, haɗe da karyewar zuciya.
Take yaji tausayinta yasake ninkuwa acikin zuciyarsa.
A hankali ya sanya hanu yazame hannayenta dake kan bakinsa, domin kuwa hakan da tayi masa har ya sanya tsikar jikinsa sun soma motsawa.
“Kinaso nayi haƙuri?” Dr yatambayeta.
Kaitashiga kaɗawa cikin kuka alamar “Eh”
“To kidaina kuka, domin kuwa daina kukanki shikaɗaine zaisanya nayi haƙuri nakuma manta da komai, kuma ko dama ni Zahrah batayi mini laifi ba, ƙanwata bata laifi a wajena, saboda haka share hawayenki kinji!” yaƙare maganar yana me miƙomata wani farin handkerchief wanda yafito dashi daga cikin aljihun wandonsa.
Karɓan handkerchief ɗin Zahrah tayi, cike da shagwaɓa tashiga share hawayen dake gudana akan fuskarta, ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai akai domin kuwa ko ba komai tarage wani nauyi dake maƙare a gefen zuciyarta.
“Yauwa ƙanwata, kinga kinfi kyau idan kina murmushi dakuma dariya, inaso akoda yaushe kikasance cikin farinciki!” Dr yafaɗa cikin nishaɗi, domin kuwa sosai yaji daɗin yanda Zahrah ta sauƙo daga fushin da takeyi dashi.
Tana gama share hawayen nata ta miƙamasa handkerchief ɗinnasa.
Kai yagirgiza alamar a’a haɗe da gyara zamansa “Nabaki kyauta, ki ajiye a wajenki, ko saboda gaba, domin naga ke kuka baya baki wahala, kinga duk lokacin da kika soma koke koken ki saiki share hawayenki da shi!”
Hararan wasa ta jefesa dashi, haɗe da murguɗa masa ɗan ƙaramin bakinta.
Dariya yayi domin sarai yana lure da’ita kuma yaga abun da tayi masa.
“Inazakije kikaci uban kwalliya haka? gashi kuma kinzo kinɓata shi da kuka.” Yafaɗi maganar alokacin dayake ciro wayarsa daga cikin aljihunsa.
Turo bakinta tayi gaba, cike da ƙunƙuni tasoma motsa bakinta, da’alama wani abu takeson faɗa, “wai a hakanne nayi kwalliya, kawai dai yace banyi masa kyau ba” Zahrah tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.
“Wayace miki hakane a zuciyata? ni na’isa nace kyakkyawar ƙanwata batayi kyau ba, to ma duk cikin garin Abuja wayakai ki kyau ne? babu fa!”
Dariya tasanya, wanda tajima batayi shiba, cab aikuwa ko da acikin makarantarsu akwai waƴanda suka fita kyau dayawa, balle kuma duka garin Abujan baki ɗaya.
Tsayawa yayi yana kallon yanda take dariyan, komai tayi ƙara kyau take.
Hanunsa ya sanya acikin aljihun wandonsa haɗe da ciro wani haɗaɗɗen choculate, ɓare ledan choculate ɗin yayi haɗe da miƙo ma ta. Kyawawan idanunta ta ɗago haɗe da watsa masa su, girgiza kanta tayi, alamar bata buƙata.
Kwaɓe fuska Dr Sadeeq yayi haɗe da marairaice idanunsa, take taji tsikar jikinta ya zuba, yayinda gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, domin kuwa hakan da yayi yasanya fuskarsa ta koma yanayi da fuskar Zaid, saurin ɗauke kanta tayi daga garesa, haɗe da sauƙe idanunta ƙasa, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, alamar shigowar ƙira, cike da girmamawa yaɗauki ƙiran ganin cewa ƙiran daga Hajiyarsa ce.
“Kana’ina?” Hajiya tatambaya a kausashe.
Baikai ga bata amsaba taci gaba da cewa “Koma mekakeyi kabari, Inaso kaje gidansu Salima yanzu, umarni ne ba shawaraba!” ƙit takashe wayan batare da tajira taji mai zai ceba.
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga Zahrah.