NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wani uzuri yatasomin, zantafi kikula da kanki!”  yafaɗi maganar yana me miƙewa tsaye.

Miƙewa itama Zahrah tayi batare da tace dashi komai ba tashiga naɗe tabarman da suka tashi akai.

Wani irin kallo haɗe da murmushi mai tsayawa a zuciya yayi mata, kana yasa kai yafice daga zauren gidan nasu, yana fita yafaɗa motarsa yayi mata key.

Tanajin ƙaran tashin motarsa ta sauƙe a jiyar zuciya haɗe da komawa cikin gida.

Kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa hakan yayi domin kuwa yaje gidan su Salima sungana da’ita, yarinyar bata da wani aibu, amma kwata kwata jininsa danata baizo ɗaya ba, domin kuwa sam bata burgesa kasancewarta mace mai rawan kai da shegen girman kan tsiya, har gwamma masa Zabba’u akan Salima,  domin dai shikam Salima batayi masa ba. Haka dai suka gaisa sama sama,  ko minti 20 baiyiba yabaro gidan nasu..

Bayan Sati Ɗaya.

Kusan ko da yaushe sai Doctor Sadeeq yazo gidan su Zahrah, amma kuma tundaga wannan lokacin baisake koda ɗago wani zance makamancin wancan ba, sai dai yana’iya ƙoƙarinsa wajen bata kyakkyawan kulawa. Sannan  kuma dake ita ɗin me raunin zuciya ce take ta sake  bashi yardanta akaro na biyu.

Ɓangaren gidansu Dr Sadeeq kuwa harsun fara shirye shiryen bikinsa, domin kuwa Hajiyarsa wannan karon bada wasa take ba,  tace acikin 3 weeks takeso ayi bikin. Shi dai Dr Sadeeq idanu kawai ya zuba musu, domin kwata kwata baijin auren a jikinsa, da za’afasa auren to dazai fi kowa murna,  saboda Zahrah yakeso Zahrah ce muradinsa, amma kuma haryanzu yakasa samun wani gamsashshiyar amsa daga gareta.

Ƙarfe 3 dai dai jirginsu ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin garin Abuja, motoci ne iri da kala har guda shida suka zo tarbansa, ciki kuwa hadda Dad ɗinsa, a hankali yake sauƙowa daga cikin matakalar jirgin sanyen yake da kayan sanyi hadda hula, yayinda fuskarsa ke ɗauƙe da wani haɗaɗɗen baƙin glass na maza,   sosai yaƙara kyau da fari,  kallo ɗaya zakai masa katabbatar da cewa yakai cikekke kuma gwarzon namiji, a gaskia yana da kyau da kuma kwarjini, uwa uba kuɗaɗe sun samu mazauni a jikinsa. Bakowacce mace bace zatayi tozali da haɗaɗɗen  namiji kamar Zaid, kuma takau da idanunta ba, saboda Zaid yahaɗa duk wani abu da kowacce mace zata so awajen ɗa namiji, shidai matsalan sa ɗaya munanan  halaiyansa.    Yanda yake tafiya cike da izza shiyafi komai ɗaukar hankali, dakuma jan hankali zuwa garesa.    Cike da farinciki Alhaji Ma’aruf yarungume ɗa’nnasa, duk da cewa babu wani shaƙuwa me ƙarfi a tsakaninsu amma yana matuƙar son Zaid.   
Mota ɗaya suka shiga shida Dad ɗinsa, yayinda guard ɗinsu suka mara musu baya a cikin sauran motocin.      Kwanciya yayi lamo ajikin kujeran motar  haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sanyi yakeji acikin zuciyarsa,  koda wasa baitaɓa tunanin haka zai kasance dashi ba, kamarshi Zaid ace tunanin mace yahanasa sukuni harsaida yabaro duka abun da yakeyi ya dawo zuwa gareta,  amma zaiyi maganin abun a yau bawai sai gobe ba yake da buƙatar ganin sugar baby’nsa, sai dai kuma wannan lokacin bada wasa yazo ba…

Zahrah ne keta kai kawo a tsakiyar ɗakinta, tabbas tayarda da duk wani shawara da zuciyarta ta bata, zuwa yanzu yakamata ace tayi abunda ya dace. Wayarta ne yasoma ƙara alamar shigowar ƙira, tana ɗaga wayar Dr Sadeeq yace “Gani na’iso ina ƙofar gida!”

“To” tace haɗe da aje wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗi da cije lips ɗinta, dama ɗaya kawai take dashi kuma tabbas idan tarasa wannan daman to zaiyi mata wahala tasake samun wani daman.

Hijib ɗinta ta sanya, koda tafito tsakar gida bata taradda Inna ba tana kuma da tabbacin cewa bama ta gidan.

Zaune yake acikin motar tasa, dagani kasan cewa yana cikin damuwa, domin gaba ɗaya har rama tasoma bayyana a jikinsa. Murfin motar tabuɗe tashiga, bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallaman nata yayi haɗe da gyara zamansa yafuskance ta ” Baki taɓa min irin wannan ƙiran ba, naƙosa naji wace maganace zaki faɗamin mai matuƙar mahimmanci haka” gaba ɗaya hankalinsa ya tattara zuwa gareta.

“Dagaske kake Zaka aure ni?” Zahrah tajefo masa tambayar
dabai taɓa zata ba balle tsammani.

Kansa yashiga kaɗawa muryarsa har rawa take yace “Dagaske nake Zahrah, wallahi auren ki nakeso nayi, samunki a matsayin mata shine babban burina a yanzu.” yafaɗi hakan da iya gaskiya’rsa

“So na kakeyi kokuma tausayina?” Zahrah takuma jifansa da wata tambayar.

“Sonki nake Zahrah, inamiki so mai tsanani, wlh inasonki da duka zuciyata!” Dr Sadeeq yabata amsa, cike da kulawa.

“Nayarda na Amince Zan aureka, muyi zama na har abada!”  Abun da yafito daga bakin Zahrah kenan bayan tagamajin amsar da take buƙata daga garesa, cikin tsananin mamaki Dr Sadeeq yashiga kallonta, jin sauƙar maganarta yayi tamkar daga sama, kodai kunnuwan sa basu jiye masa dakyau bane?….

(To fa readers Ga Baba Zaidu yashigo Gari, ga kuma Zahrah ta amince da auren Dr Sadeeq, gashi kuma ɓangaren gidansu Dr anatashirye shiryen bikin Dr da Salima, koya zata kaya ????‍♀, please kusani a addu’anku wlh cikina ke ciwo sosai???? idan kunga typing eror kuyi haƙuri gaba ɗaya banda wata isashshen nutsuwa ne ????)

   10/December/2019

Voted,Comment,and Share please…. Follow me on Wattpad @fatymasardauna
????????????????????????????????????????

           SHU’UMIN NAMIJI!!

    
         Written by
  Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

”'{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & mitivate the mind of readers}”’

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

     
          WATTPAD
    @fatymasardauna

Editing is not allowed????

(This  page is Dedicated  to you  HAROUN UMAR (H Umar) admin of ????✍️BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION, inajinjinamawa ƙoƙarinka ako da yaushe haroun, kuma inagodia a gareka marar iyaka.)

    CHAPTER 53 to 54

Kasa motsa koda laɓɓansa yayi balle har yakai ga furta wata kalman, “dagaske ne abun da kunnuwansa suka jiye masa kokuwa mafarki yake?” yafaɗi hakan a  cikin zuciyarsa.

“Kada kayi kokonto kokuma shakka, dagaske nake, na amince da aurenka, amma ina mai roƙon wata alfarma a gareka”….”Dan Allah kada ka wulaƙantani aduk yanda kasameni, kada kuma ka tozartani, nasan cewa tausayina yafi yawa acikin zuciyarka fiye da soyayya ta, saboda haka ina da tabbacin cewa ko gaba zaka iya sake samun wata mace,wacce itace zata kasance zaɓinka, kada haka yasa ka wulaƙantani dan Allah, kada kuma kacutar da rayuwata!” cikin sanyin murya ta ƙare maganarta ta, yayinda hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta,suna sauƙa akan ƙuncinta.

Jiyayi gaba ɗaya wani irin matsanancin farinciki ya lulluɓesa, gani yake tamkar wasa Zahrah take masa, amma kuma ba’abun mamaki bane, saboda babu abun da yagagari Allah.

“Bansan ta’ina kokuma tayaya zan fara godemiki ba Zahrah,  kin gusarmin da duk wata damuwa dake damuna, kinbani farinciki cikin ƴan mintuna ƙalilan,  kiyarda dani Zahrah, inamiki Soyayyace ta gaskiya bawai, irin soyayyarnan tako oho ba, zan’iya sadaukar da duk wani abu nawa akanki Zahrah,   soyayyar da nake miki, yasanya bana ganin laifi ko kuma aibun duk wani abun da kikamin,   burina da fatana shine murayu tare dani dake amatsayin miji da mata, kuma aƙarƙashin inuwa ɗaya,  Inasonki Zahrah, kuma namiki alƙawari komai wuya komai tsanani bazan taɓa gujemiki ba, ZANRAYU DAKE Zahrah!!” Dr Sadeeq yafaɗa cike da matsanancin farinciki, jiyake tamkar yajawo Zahrah jikinsa yabata kyakkyawan runguma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button