SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Cigaban Labari
Adai dai bakin titin yayi parking motarsa, domin sam shikam baijin cewa zai iya shiga, wannan unguwar talakawan da tsadaddiyar motarsa, shi sam baisan ma uban me yasa Bash yayi guest house ɗinsa a wannan unguwar ba,, zama yayi a cikin motarsa haɗe da ɗaukar wayarsa yadanna mawa lambar (Number) Bash ƙira, ringing biyu kawai wayar tayi Bash da ke kwance jikin wata ƴar iskan sa ya ɗaga,, “Ina bakin titi ” yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar tasa,, baiwani ɗau lokaci ba saiga Bash ya ƙaraso,
“kaga SHU’UMIN NAMIJI maifirgita ƴan mata, Shu’umi mai sace zuciyar duk wacce yaso, ko shaiɗan yana tsoron shu’umancin ka !!” Bash yafaɗa dai dai lokacin dayakema kansa masauƙi acikin motar, ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa ” Kai ni duk ba wannan ba waishin meyasa ka tsalleki ko wani unguwa kazo nan kayi guest house ɗinka ?, ka duba fa gidajen area’nnan gaba ɗaya na talaka wane ” Zaid yaƙare maganar yana maibin gidajen da kallon ƙyama,, murmushi Bash yayi haɗe da cewa
” Bazaka gane bane my man, amma wallahi ƴan mata nake samu a arean nan bana wasaba, kai bana ta ƙaice maka, yarinya sai ta kawomaka budurci (virginity) ɗinta a ɓagas, badon komai ba sai don tsananin talauci daya adda beta, yanzu haka akwai ƴan mata a ƙasa idan kana buƙata..” Bash yaƙare maganar yana murmushi mai ɗauke da nuna shi tantirin ɗan iska ne,,
taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa “Bazan iya iskanci da low class ba gaskia, kudai kuyita fama harku ɗaukomawa kanku wata cutar, yaƙare maganar yana ƴar dariyan mugunta,,
gyara zama Zaid yayi haɗe da cewa ” Nazo maka da wani babban harka ne idan zakayi ” shima Bash gyara zama yayi da kyau haɗe da cewa “Inajinka abokina “
Zaid ya buɗe baki zaiyi magana kenan idanunsa suka sauƙa akan wata kyakkyawar budurwa, wacce ke sanye da hijab iyaka guiwarta, hijab ɗin irin mai roba ɗinnan ne, hakan yasa ya bayyana duk wata sura na jikinta, wani irin abu Zaid yaji daga ƙasan ƙafarsa harzuwa cikin kansa, yayinda tsikar jikinsa yashuga zubawa, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa, da alokaci guda suka kaɗa sukai ja, koda yabuɗe su don sake kallon wannan halittar da’idanunsa sukai masa to zali da’ita, sai yaga saɓanin haka, domin ko a alamar gilma wanta baigani ba, saurin fita daga motar yayi haɗe da soma waige waige ko Allah zaisa yaganta, amma ko alamar ta bai gani ba……..
(Tofa readers waishin wace budurwa ce Zaid ya gani ?)
14/October/2019
*MRS SARDAUNA*
????????????????????????????????????????
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written by*
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Lovely Brother Khabeer
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*WATTPAD*
@fatymasardauna
Editing is not allowed ????
Chapter 7
” Lafiya kuwa Zaid wakake nema ne ?” Bash yatambayeshi,, ɗan taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa ” bakomai kawai ina duba yanayin unguwar ne ” yaƙare maganar yana mai komawa cikin motarsa yazauna,,, sama sama Bash da Zaid sukayi magana, domin kwata kwata hankalin Zaid baya jikinsa, burinsa kawai shine idanunsa su sake yi masa to zali da wannar kyakkyawar fuska da jikin, daya gani…..
Tunda Zahrah tafito daga gidan su Husnah tafuskanci cewa da akwai mai binta a baya, hakan yasanya taji wani irin tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, don haka ta ƙara ɗaga ƙafufunta, “Assalamu Alaikum !!” muryan Namiji mai cike da kamala ya doki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya da tafiyan da takeyi batare da ta juyo ba,, cikin takunsa na burgewa ya ƙaraso gareta, kyakkyawan saurayi ne, mai ɗauke da launin fata choculate colour, dogo ne amma ba har canba, yanada faffaɗan jiki mai burgewa, sannan yana da kwarjini ba laifi,, murmushi yayi mata haɗe da cewa “Ƴan Mata bazaki amsa sallaman nawa bane ?” saurin sunkuyar da kanta ƙasa Zahrah tayi haɗe da cewa “Wa’alaikassalam”
Lumshe idanunsa yayi domin kuwa bakaɗan ba zazzaƙar muryarsa tadaki ƙahon zuciyarsa ” Sunana JABEER, Idan bazaki damuba, inaso kibani adireshi’n gidanku, sai nazo, domin a matsayinki na mace mai mutumci baikamata natsaidaki a bakin hanya ba ” Jabeer yafaɗa hakan yana mai kafeta da idanu,, gaba ɗaya kanta ɗaurewa yayi don haka, batare da tace dashi ƙala ba, tacigaba da tafiya, da sauri sauri,, roƙonta Jabeer yashiga yi akan ta tsaya ta saurareshi, amma ina Zahrah ƙara ɗaga ƙafanta tayi domin ita tsoro ma yabata, ganin da Jabeer yayi cewa bazata tsaya bane yasanya shi ƙyaleta kawai tayi tafiyarta, amma a zuciyarsa ya ƙudura aniyar nemota komai daren da ɗewa ….. Zahrah tana komawa cikin gida kaitsaye ɗakinta tawuce, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa a kai akai tamkar wacce tayi gudu, idanunta da suke lumshe ta buɗe su ahankali, haɗe da da sanya harshenta ta lashi lips ɗinta na ƙasa, Allah yasani gayen ya burgeta amma kuma tanajin tsoro gaskia, domin bata saba tsayuwa da samari ba……
Birgima kawai yakeyi akan makeken gadonsa, kwana huɗu kenan daganinta amma da ya rumtse idanunsa, hoton kyakkyawar surarta yake gani, baisanta ba, baisan wacece itaba, amma wani irin sha’awarta yakeji, tabbas yazama masa dole komawa unguwar Suleja ko Allah zaisa yasake ganinta,, wayarsa dake ringing ne yakatse masa tunanin da yakeyi, DADY shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayara, ɗaukar wayar yayi a kasalance haɗe da karawa akan kunnensa “To” kawai naji yace haɗe da cilli da wayartasa gefe, tashi yayi daga kwancen dayake haɗe da ɗaukan rigarsa yasanya, ya fice daga cikin ɗakin…..
Kai tsaye babban falon Dadyn nasa yanufa, can ya iske Dadyn nasa tare da Mom ɗinsa, zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, fuskarnan tasa babu yabo ba fallasa, yace “Dady gani ” Gyara zama Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa ” Banaƙira ka bane don muyi dogon magana, naƙiraka ne don na sanar maka cewa zuwa yanzu yakamata ace kafitar da matar aure, kagama karatunka, ga kuɗinan kana samu ba’adadi, to mai yarage maka idan banda Aure Zaid ? a gaskia banajin daɗin zamanka haka ba aure, saboda haka kafito da matar aure “
” Yauwa gaya masa dai Alhaji, tunda ni nayi maganar har nagaji bai ɗauka ba, ga Khausar ɗiyar ƙanwata nan ma, sai ayi tuwona mai na ” Mom tafaɗa tana murmushi,,,,
Dasauri Zaid yaɗago yakalli Mom ɗintasa, jin abun da take faɗa, wai Khausar, cab aiko mata sun ƙare a duniya bazai auri muciya da zani ba, yanda yasan mata ciki da bai, yana da tabbacin cewa Khausar tana ɗaya daga cikin irin matannan marassa ni’ima wanda idan kana sex dasu zakana jinsu kamar dusa, babu wani ɗanɗano,,
“Kayi shiru” Dad yakatsesa daga tunanin daya keyi,,
” ka ƙara bani lokaci Dad insha Allahu zan kawota nan bada jimawa ba, amma gaskia maganar Khausar Mom ki barshi, domin kwata kwata ni bana jinta acikin zuciyata ” yana kaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga cikin falon,, da idanu kawai Dad da Mom suka rakasa, har abada shidai Zaid bamai iya masa sai Allah, duk yanda ka ɓullo zaice ba haka ba…..
Koda yakoma ɗakinsa wanka yayi, haɗe da ficewa daga cikin gidan baki ɗaya,, baizarce ko’inaba sai babban gidan giya dake Abuja, can yaje yacika cikinsa yayi tatul, daganan yasamu abokiyar shaiɗanansa, suka yi watsewarsu…..
Zahrah sunfara Exam, don haka tuni kanta yaɗau zafi, karatu kawai takeyi baji ba gani, cikin ikon Allah kuwa komai nata yana tafiya adai dai, domin dai tana sa ran cewa zata samu kyakkyawan sakamako,,,