NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Alhmdlh!” Zaid yafaɗa a taƙaice, bayan ya janye jikinsa daga na mahaifiyartasa.    Ƙoƙarin juyawa yakeyi, Mom tace “Inakuma zaka my son ba abinci kazo ciba?” cike da kulawa ta tambayesa.

Ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa “Banajin yunwa Mom, idan nadawo zanci!”  baijira jin maizasu ceba yasakai yafice daga cikin falon.

Da kallo kawai Mom tabisa har yafice, fuskarta ɗauke da damuwa, itakam ta rasa wani irin haline da Zaid, sam ba’a iya gane gabansa da bayansa.

“Miye abun shiga damuwa  Hajiya Safara’u? zuwa yanzu yakamata ace duk wani hali na yaronnan Zaid kin gama saninsa!”  Alhaji Ma’aruf yafaɗi hakan cike da nuna kulawa ga matar tasa.

“Nasan halinsa Alhaji, amma kuma ace mutum shi baya taɓa sanjawa, ko da yaushe fa Zaid bayason zama a cikin mu, sannan kuma sam baya sakewa damu!” Mom tafaɗi hakan cike da damuwa.

“Zauna muci abincin mu, aishi ba ƙaramin yaro bane, yasan me yakeyi!” Alhaji Ma’aruf yafaɗi hakan yana mai kama hanun Mom yazaunar da’ita a kusa dashi.

Zaid kuwa yana fita daga ɓangaren mahaifiyartasa, kai tsaye wajen motarsa yanufa,   koda driver yanemi da yabarsa ya tuƙasa, ɗaga masa hanu yayi alamar baya buƙata,  shida kansa yayimawa motar key, ya harbata zuwa kan titi.

Tafiya yake cikin nutsuwa yayinda airpiece ke saƙale a kunnuwansa,   wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira,   ganin cewa babban manager’n company’nsa dake nan gida Nigeria ne ke ƙiransa yasanya shi ɗaga ƙiran.   Banji mai Manager’n nasa yace masa ba, sai gani nayi ya’aje wayan, haɗe da buga dogon tsaki,   lokaci ɗaya yakarkata akalar motar tasa  zuwa wata hanya daban saɓanin hanayar daya nufa, wanda zai sadasa da unguwar su Zahrah.

Dr Sadeeq kuwa yana barin unguwar su Zahrah kaitsaye gidansu yanufa, acewarsa gwamma yayi maganin matsalarsa tunkafun tayi nisa.

Usaina mai aikin ɓangaren Hajiyarsa yasanya tane ma masa iso awajen Hajiyar tasa, domin kuwa bai isketa a falo ba.

Da sallama yashiga cikin ɗakin Hajiyar tasa,  fuskarta ɗauke da fari’a ta amsa masa sallaman da yakeyi. Zaune take akan gado, yayinda  take duba wasu kayayyaki dake zube a gabanta.

“Barka da huwatawa Hajiya!” yafaɗa cike da ladabi.

“Yauwa  barkanka, kamar kuwa kasan ina nemanka, wai me kake nufi da auren nan ne Sadeeq? har yanzufa banga kana wani cuku cuku ba, kayan lefe ma saini kabarmawa ɗawainiyar haɗasu, gashi kuma Salima tacemin tunda kaje sau ɗaya baka sake zuwa ba, mai ke damunka ne wai?” Hajiya tatambayesa cike da kulawa.

Kansa yashiga sosawa haɗe da sake yin ƙasa da kansa,   “Am…dama Am….” “Dakata banson wani kwana kwana, kafaɗi abunda zaka faɗa kai tsaye kawai” Hajiya ta katsesa daga kame kamen maganan dayake ƙoƙarin yi mata.

“Hajiya kamar dai yanda na faɗamiki ne,  wallahi Hajiya dagaske nake, yanzu nasamu wacce nakeso kuma idan harkin yarda aurenmu bazai wuce nan da Sati uku ba, kamar yanda kikeso!” yafaɗi hakan cike da ladabi.

Sororo haka Hajiya ta tsaya tana kallonsa,  “anya kuwa Sadeeq yana lafiya? ” tatambayi kanta.

“Inagadai bakasan mekake cewa ba Sadeeq, wato nikakeson watsamawa ƙasa a cikin idanu ko,  ya yi maka kyau, to inaso kabuɗe kunnuwanka da kyau ka saurareni, wallahi ko da wasa kakuma zuwamin da irin wannan zancen saina ɓata maka rai,  nagama baka duk wata dama dazan baka, bakuma zan sake baka wata daman ba, tashi kabani waje, tunda nalura kai baka da tunani!” Hajiya ta ƙare maganan cikin faɗa.

Cikin rashin kuzari haɗe da sanyayewar guiwa Dr Sadeeq yamiƙe daga gaban mahaifiyartasa, haɗe da nufar ƙofar fita daga cikin ɗakin,

Saida yakai ɓaƙin ƙofar fita  ckafun yatsaya cak, haɗe da juyo da kallonsa ga Hajiyar tasa cikin murya mai rauni yace “Hajiya dan Allah..” 
“Fita kabani waje nace!!” Hajiya takuma faɗa cikin ɓacin rai tanamai yi masa nuni da ƙofar fita daga ɗakin…

(Readers nifa Hajiyannan tasoma ban haushi yasin????????)

Kuyi manage da wannan ba lallai gobe nayi typing ba shiasa, namuku yau

11/December/2019

  Voted, Comment, and Share please….. Follow me on Wattpad @fatymasardauna

      
6:17 pm
????????????????????????????????????????

       SHU’UMIN NAMIJI !!

      Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

”'{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

          WATTPAD
    @fatymasardauna

Editing is not allowed????

(Kuyi haƙuri shekaran jiya nayi mistake ɗin number 52 to 53 zansa, sainasaka 53 to 54????)

CHAPTER 55 to 56

Cikin sanyin jiki  Dr Sadeeq yafita daga cikin ɗakin mahaifiyarta sa.    Gaba ɗaya jiyayi zuciyarsa ta cika da ƙunci. Yana isa ɓangarensa ya zube akan ɗaya daga cikin kujerun falonnasa,  “yanzu wazai je yasamu da wannan matsalar? tabbas yasan Hajiyarsa mutum ce mai kafiya, idan tace eh zai yi wuya ta dawo tace a’a”
  hanunsa yasanya cikin sumar dake kwance akansa haɗe da yamutsa ta,   sunan Aunty Raliya ce yafaɗo masa arai, tabbas ita kaɗaice ƴar uwarsa da zai kai mata matsalansa har ma ta tayasa magancewa, sai dai kuma yanatunanin itama ra’ayinta ɗayane da Hajiya, amma yasan idan yayi mata kyakkyawan bayani zata fahimcesa, zumbur yamiƙe daga zaunen dayake.
Ko bedroom baishiga ba yakuma ficewa daga cikin falon,  mota ya koma, haɗe da kunnata, mai gadi ne ya wangale masa gate ɗin gidan yafice.

Hajiya najin ƙarar ficewar motarsa daga cikin gidan ta sauƙe ajiyar zuciya.
“Gaba ɗaya tunaninta ya kulle, batasan wani irin abu Sadeeq keshirin shigo mata dashi cikin gida ba,  kusan sau uku kenan tana bashi dama, akan yafito da matar aure, amma dazaran lokacin da ta ibar masa yacika, sai ya farayi mata kame kame,  yanzu da tagaji da sakarcinsa ta zaɓa masa mata, sai yake nema yawatsa mata ƙasa a idanu, bakuma zata lamunci hakanba.

Direct Dr Sadeeq gidan Aunty Raliya yanufa, domin baida wata ƴar uwa da ta wuce ta a duniyar nan. 

Yanashiga gidan tunbai gama fitowa daga cikin motarsa ba, su Meenal da Affan ƴaƴan Aunty Raliya, suka rugo da gudu zuwa garesa, dama wasan ball suke a farfajiyan gidan nasu, hakan yasa duk wanda yashigo da kuma wanda zaifita zasu gansa.

Rungumesu yayi a jikinsa, haɗe da shafa kawunansu,     “Oyoyo  babies ɗina, ashe girma yazo muku,  har wasan ball kukeyi!” yafaɗi hakan cike da nishaɗi.

“Eh Uncle ai harma nafita iyawa!” Affan yafaɗi haka cike da zumuɗi.

“Ƙaryayake Uncle baifini iyawa ba” Meenal tafaɗi hakan tana mai kama ƙugu, alaman ƙarya Affan ɗin yakeyi.

Murmushi kawai Dr yayi haɗe da sake shafa kansu,  “kuyi wasa da kyau, idan nafito zan baku alewa!” yafaɗa yana mai nufar kofar da zata sadashi da babban falon gidan. Yayinda yabar su meenal sunata tsallen murna saboda yace zai basu alawa.

Da sallama  ɗauke a bakinsa yashiga cikin falon.

Aunty Raliya dake zaune tana kallon tv, ta amsa amsa masa sallamar tasa, fuskarta  ɗauke da  fari’a, haɗe da yi masa iso.

Ƙarasowa yayi yazauna akan kujera, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, gaba ɗaya a gajiye yakejinsa, domin tun safe yau baisamu nutsuwa ya huta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button