NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannayensa yasanya duka biyu ya tallafi kansa,  lallai akwai babban ƙalubale a gareshi,  agun Aunty Raliya ma kaɗai ga’irin ɓacin ran daya fuskanta, inaga Hajiyarsa kuma.?

Miƙewa yayi daga zaunen da yake tamkar wanda ƙwai ya fashewa a jiki haka yake tafiya, gaba ɗaya ƙwaƙwalwarsa tasake dagulewa, yazone don yasamu mafita amma sai gashi abubuwa sun sake dagulewa.

Da ƙyar yake iya tuƙa motar tasa. Haka yanufi gida cikin rashin kuzari, sai dai fa haryanzu bai saduda da maganar Auren Zahrah ba, yanaji ajikinsa cewa Zahrah zata zamo matarsa Insha Allah.

Gagarumin meeting su ZAID suka gudanar mai zafi, a babban hotel ɗin nan wato SHERATON, sosai aka samu riba dakuma ƙarin buɗi a ɗaya daga cikin  company’n nasa da suke Nigeria, hakan yasa yaƙarawa gaba ɗaƴa ma’akatansa albashi.

Sunjima suna meeting ɗin dan haka amatuƙar gajiye suka fito dukansu, lokacin har dare yasoma rufawa.    Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, yayi yaga karfe 6 daidai na yammaci, ɗan ƙaramin tsuka yayi haɗe da soma yunƙurin cire rigan suit ɗin jikinsa wada yaɗaura akan kayan dake jikinsa, 
saboda gajiyan da yayi bai iya tuƙi da kansa ba, sai  driver’nsa yaƙira yayi driving ɗinsa.

Gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sarawa kansa keyi masa,  daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa sosai meeting ɗinnan ya ɓata masa rai, domin kuwa ya hanasa ƙarasawa ga ZAHRAH’nsa,  wacce saboda itane ma gaba ki ɗaya yadawo ƙasar, yayi missing din Zahrah sosai,  yayi missing kyakkyawan murmushinta haɗi da kyawawan idanunta, yayi missing kallon kyawawan laɓɓanta masu daɗin tsotso. Gaskiya dole  ya killace Zahrah tayanda zata zama nasa shi kaɗai.

Suna isa gida kai tsaye ɓangarensa ya wuce, a gajiye yashiga bathroom yayi wanka,  koda yafito a wankan, direct masallaci ya wuce donyin sallan magriba. Sai da yajira aka yi sallan isha tare dashi a masallaci, kafun  ya siɗaɗo yadawo ɗaki ya kwanta, yau ko abar ƙaunar tasa wato wine baisha ba bacci ɓarawo yayi gaba dashi.

Zahrah ce kwance akan katifarta sai juyi take ta kasa bacci, gaba ɗaya kanta ya kulle zuciyarta cike take da tarin tunanuka kala kala. “Anya banyi sauri kokuma gangancin yarda da kuma amincewa da soyayyar Dr da nayi ba?” zuciyarta ta tambayeta.
Zumbur haka ta miƙe zaune, haɗe da soma girgiza kanta
” A’a banyi kuskure ba, tabbas bayan shi babu wani maiso da nuna tausayi gareni!” tabawa kanta amsa a bayyane.

Wayartace takawo haske alamar shigowar ƙira, kasancewar ta sanya wayar a silent hakan yasanya wayar batayi ƙaraba.

“Doctor” shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar.

“Shima baiyi bacci ba kenan” tafaɗi hakan a bayyane.

Saida wayar ta kusa katsewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran haɗe da kara wayan akan kunnenta.

“My princess bakiyi bacci ba kenan?” Dr Sadeeq yatambayeta cikin muryarsa mai ɗauke da damuwa.

“Um, kaifa me yahanaka bacci” Zahrah itama  tatambayeshi.

“So da ƙauna dakuma tunaninki susuka hanani bacci! kefa mai yahanaki bacci?” yatambaya cike da son jin amsar da zata fito daga bakinta, “Allah yasa itama tunani na ne ya hanata bacci” yafaɗi hakan a zuciyarsa.

Kunyane yaɗan kamata amma sai ta basar haɗe da sauƙe ajiyar zuciya “A’a nikam karatu nake, shiyasanya banyi bacci ba, amma yanzuma zanyi baccin.” tafaɗi hakan a taƙaice.

Ko kaɗan baiji daɗin amsar da ta basa ba, amma yasan cewa wataran dole zatayi tunaninsa kamar yanda shima yake nata tunanin.

“Naji daɗi sosai da kika amince dani Zahrah na! hakan yasa na ƙara jin sonki sosai da sosai a cikin zuciyata!!”  cikin shauƙin so yafaɗi maganar.

“Umm banji mai ka faɗa ba!” Zahrah tafaɗi hakan cikin wani irin salo wanda batasan ma tayi shi ba, duk da kuwa cewa taji mai yace, iskancine kawai irin nata.

Lumshe idanunsa yayi da suka soma sauya kala, sosai yanayin yanda tayi maganar ya sauƙar masa da kasala.

“Bacci kika farane Zahrah na?” yatambayeta cike da kulawa, domin kuwa shi anasa zaton dagaske batajisa ba.

“Um!” Zahrah ta basa amsa a taƙaice cikin ƙasa ƙasa da murya, domin kuwa tanaso yayarda cewa baccin takeji, saboda har yanzu, bata gama amanna dacewa sonsa take ba, kuma koda za’a kasheta tasan cewa ba sonsa take ba, kawai dai ta tsinci kantane da amince masa, amma batun soyayya kam babu shi.

“To kiyi bacci mai daɗi kinji My princess, inasonki sosai, ki kulamin da kanki, banson koda ɗigon wani a bune ya raɓe ki!”  Dr ya faɗi haka cikin shauƙin SO (Sisters kujisafa su likita ashe an iya kalaman love, lol.)

“Uhumm sai da safe.” Zahrah tafaɗa a taƙaice bayan ta zare wayar daga kunnenta.
  “Gaskiya abune mai matuƙar wahala koyawa zuciya So’n  abun da bata so, ya Allah kataimakeni, haƙiƙa banajin tsanarsa haka kuma banajin soyayyarsa a zuciyata, sannan kuma inaji ajikina cewa zan’iya rayuwa dashi, to me hakan ke nufi, ba so bane kuma ba ƙi bane to menene?” tatambayi kanta a bayya ne, saidai kuma bata da amsar da zata bawa kanta.

Komawa tayi ta kwanta bayan ta kashe wayarta ta gaba ɗaya.

Cike da saƙe saƙe bacci yayi awungaba da ita.

Ɓangaren Dr Sadeeq ma, sai da yajima yana saƙawa da kuncewa, ba abun da yake ɗaure masa kai, kamar yanda ya kasa fahimtar cewa Zahrah, na son sane ko bata sonsa. da ƙyar dai shima bacci ya’iya ɗaukarsa.

Washe Gari.
  
Yau tun saven thirty suke da lecture, dan haka da wuri tasoma shirya kanta, sosai tayi kyau cikin shigar jar abaya haɗe da jan hijab ɗin dake jikinta,   hand bag ɗinta ta rayata a bisa kafaɗanta. Kana tafice zuwa tsakar gida.  Zama tayi akan taburma haɗe da jawo farantin ƙosai da kuma kofin kunun da Inna ta aje mata tasoma sha.  Baffa ne yafito daga cikin ɗakin sa yanaganin Zahrah yace
“Yauwa  kinfito ko, tun ɗazu kuwa likita yake jiranki a waje” 

“Eh Baffa nafito” tabashi amsa cike da mamakin jin cewa wai Dr yajima da zuwa, yanama jiranta a waje, amma kuma bai ƙira ta a waya yasanar mata ba.

Aƙagauce taci abincin kasancewar har bakwai tayi.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushi, itama murmushin ta sakarmasa bayan tagama ƙaremawa kwalliyarsa ta yau kallo.

“Kinyi kyau my princess!” yafaɗa cike da nishaɗi, domin kuwa sosai tayi masa kyau, jan kayan da tasa ya karɓi kalan fatarta.

“Kaima haka” tabashi amsa a taƙaice.

Murmushi yakumayi haɗe da buɗe mata murfin motar nuni yayi mata da hanunsa alamar tashiga, wani murmushi mai tsayawa a zuciya tayi masa haɗe da shigewa cikin motar tayi mawa kanta mazauni.

Tafe suke suna hira cike da nishaɗi, wanda gaba ɗaya yawan hiran Dr ne maiyi mata shi.
A haka har suka iso cikin makarantar, ƙoƙarin buɗe murfin motar ta soma yi.

“Ya haka? baki sallameni ba fa, kike ƙoƙarin  tafiya” Dr Sadeeq yafaɗi hakan cikin sigar zolaya.

Murmushi Zahrah tayi masa haɗe da yin fari da’idanunta “Bangane ba” tafaɗi haka cikin salo.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanu yashafi  sajensa,  “Inanufin bakice kina sona ba”

Dariya haɗe da kunyane suka kama Zahrah sai kawai ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, domin kuwa bazata iya masa abun da yakeso ba.

Saida yaga shigewarta cikin hall kafun yaɗauke idanunsa daga kanta,  yanason mace mai kunya gashi Zahrah takasance me kunya. Cike da tarin tunaninta yabar cikin makarantar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button