SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Editing is not allowed????
CHAPTER 59 to 60
Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi har saida ta sa hanu ta dafe kirjinta daya fara dukan uku uku…..
“Jekace tana zuwa” Inna tace da yaron,, bamusu yaron yajuya yafice daga cikin gidan…
“Yadai lafiyanki kuwa naga kinwani dafe ƙirji?” Inna tatambayi Zahrah, wacce lokaci ɗaya yanayinta ya sauya.
“Bakomai” Zahrah tafaɗa a taƙaice domin kuwa ko tayi ƙoƙarin ganar da Inna halin da take ciki tofa bazata gane ba…
“Tashi maza kije, ba kyau yin watsi da baƙo, wata ƙilama da alkhairi yazo miki, domin na lura keɗin baki da ƙashin tsiya” Inna tafaɗi hakan lokacin da ta miƙe daga zaunen da take.
Cikin sanyin jiki Zahrah takoma ɗaki ta ɗauko ƙaton hijab ɗinta ta sanya.
Tun kafun ta ƙarasa fita daga zauren gidannasu zuciyarta tasoma bugawa, wanda batasan dalilin hakan ba.
Wata mota ce tagani fake a ƙofar gidan nasu, kasancewar akwai hasken wuta, yasanya har kalan motar tana’iya hangowa.
Tsayawa tayi cak daga inda take, domin bazata sake tabka babban kuskuren da ta tabka a baya ba, batasan waye ba don haka bazata ƙarasa ba, idan wanda ke cikin motar yagaji ya fito, ya isketa daga inda take tsaye…
Cikin hanzari wani wanda baza’a ƙirasa da suna matashi ba, bakuma za’a ƙirasa da suna tsoho ba, yafito daga cikin motar hanunsa ɗauke da wani kwali, yayinda aka ɗaura wani kyakkyawan flower a saman kwalin… Ganin yanufota kaitsaye yasanya ta ɗan sake ja da baya..
“Sannu da fitowa ranki shi daɗe” mutumin nan yafaɗa..
“yauwa sannu” Zahrah ta bashi amsa a taƙaice…
” dama saƙone aka bani nakawomiki” wannan mutumin ya kuma faɗa cikin rusunawa haɗi da girmamawa, duk da kuwa cewa shiɗin ba yaro bane, domin yakusan haifar Zahrah’n ma, domin itama bawani yawan shekaru ne da’ita ba…
Cike da tsananin mamaki Zahrah, ta saki baki da hanci tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, yana miƙomata saƙon dake hanunsa…
“Wayekai?” shine kawai abun da ya iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya kanta ya kulle…
Murmushi mutumin yayi haɗe da cewa “Ba’a bani daman sanar dake koni waye ba, kawai dai an umarceni dana kawomiki wannan saƙon, sannan dan Allah kada kice bazaki ansaba, saƙone mai mahimmanci, yanada kyau ki karɓa, sannan daganinki ke mai ilimi ce, kinsan bakyau maida hanun kyauta baya!” mutumin yafaɗi haka still yana mai sake miƙo mata kwali da flowern dake riƙe a hanunsa…
Kai Zahrah tashiga gyaɗawa, cike da tsarguwa tace ” Kana da girma da kuma mutumcin da bazanyimaka gardama ba, amma kuma saidai kayi haƙuri, bazan karɓi abu daga wanda bansani ba, bankuma san menene nufinku a kai na ba” tafaɗi hakan da iyaka gaskiyarta….
“Hakane, amma ki ceci aikina, domin wanda ya ban saƙonnan nakawo zuwa gareki ya tabbatarmin da cewa, idan har baki karɓi saƙon ba, to abakin aikina, kitaimaka, ina da iyalai, kuma da aikina na dogara” mutumin yafaɗi haka cikin rauni.
Zaro idanu Zahrah tayi haɗe da jinjina maganar mutumin aranta, lallai kuwa kowaye ya aikosa yacika ɗan jin kai, ita kuma irin mutanen da tafi tsana kenan a rayuwarta wato mutum mai jin kansa….
Cike da kokonto haɗi da zullumi tasanya hanu ta karɓi abun da mutumin ke miƙomata.
“Zankarɓane kawai saboda kai, domin na fuskanci rashin karɓana zai iya sanyaka acikin matsala, amma koma waye ya turoka kace masa injini ya sanja hali, domin wannan ba hali mai kyau bane” daga haka tasakai tayi komawarta cikin gida..
Cike da murna’n cewa ta karɓi saƙon wannan mutumin yakoma mota haɗe da yi mata key yabar area’n unguwar tasu….
Zahrah tana shiga gida kaitsaye ɗakinta ta wuce, yayinda Inna ta rakata da idanu…
Zama tayi akan katifa, haɗe da tsurawa kyakykyawan kwalin nan idanu, ba iya shi kaɗai bane, abun ɗaukar hankali, hadda wannan haɗaɗɗen flower’n dake samansa ma abun burgewane, alal haƙiƙa ma ita flower’n ne yafi ɗaukar hankalinta….
Cikin sanyin jiki tasa hanu ta ɗauki flower’n haɗe da matso dashi kusa da fuskarta….lokaci ɗaya ta zabura haɗe da wurgi da flower’n gefe, take idanunta suka kaɗa sukai jajur dasu, jitayi kanta yafara juyawa, tabbas bazata taɓa mantawa da wannan ƙamshinba har abada kuwa, ajikin mutum ɗaya tasan wannan ƙamshi, bayan shi kuma batasakejin ƙamshin a jikin kowa ba,, hannayenta ta sanya duka biyu haɗe da dafe kanta dayake sara mata,, tabbas irin ƙamshinsa fulawar nan keyi, take taji wani irin tsanar flower’n ya cika mata zuciya, san nan kuma tsanarsa tasake dawo mata sabuwa fil, cike da ɓacin rai ta ɗauki flowern haɗe da fita waje da’ita, ko son ganinta ma batason yi, kai tsaye wajen da suke aje shara ta nufa, cike da tsanar flower’n ta jefa ta cikin kwandon shara, haɗe da furzar da yawu akan flower’n duk wani abu da zai tuna mata da Zaid ta tsanesa…
Ranta a ɓace takoma ɗaki, ita dai Inna dake zaune a tsakar gidan haka ta saki baki galala tana ganin ikon Allah..
“Wallahi na tsaneka, tsana mafi muni, bantaɓajin tsanar wani a raina sama da wanda nakeyi maka ba, ya Allah kada ka sake haɗa fuskata da tasa!” tafaɗi hakan a bayyane, kuma cikin tuƙewar murya…
Gaba ɗaya ƙamshin da taji flower’n nan nayi ya ɗaga mata hankali, sabuwar tsanar Zaid yasake ɗarsuwa acikin zuciyarta…
Lallai da zataga wanda yasanya akawo mata flower’n nan da ta gargaɗesa da kada ya sake kawo mata komai nasa, don bata so, domin kuwa duk wani abu da zai sanya tayi tunanin Zaid bata ƙaunarsa, koda sunansa nema batason ji”
Kwanciya tayi lamo akan gado, tana mai da numfashi, ji takeyi gaba ɗaya ta tsani ɗakin nata, domin kuwa ɗakin gaba ɗaya ya ɗau ƙamshin turaren dake jikin flower’ ɗin nan….
Wayartace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin Dr Sadeeq ne me ƙira yasanya ta ɗaga wayan, cikin son ɓoye damuwarta..
“Inaƙofar gida” abun da Dr Sadeeq yafaɗa kenan, a cikin wayar, domin kuwa shima dai yauɗin yana cikin damuwa….
Babban tabarma ta shumfuɗa musu a tsakar gida, kafun tanufi ƙofar gida don yi masa iso..
Kusan tare suka shigo cikin gidan, tana gaba yana biye da’ita a baya.. Gaba ɗaya yagama karantar yanayinta, ya kuma gane cewa tana cikin damuwa.
Zama yayi akan tabarman da ta shumfuɗa musu, haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa.. Gaba ɗaya nutsuwarsa ya miƙa zuwa gareta, ta hanyar zuba mata idanu….
Gyara zama Zahrah tayi haɗe da ɗaga idanunta ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan na juna.. Cikin son basarwa tace ” Sannu da zuwa, ya hanya?”
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da lumshe idanu…”Hanya ba daɗi duk nagaji da tuƙin ma, i hope you will find a driver that will take me home” cikin zolaya yaƙare maganar..
Kallonsa tayi kawai, haɗe da yin ɗan murmushi, shiru tayi batare da tace dashi komai ba…
“Meke damunki naganki haka, ko dai ciwon kanne?” Yatambayeta cike da kulawa..
“No bashi bane, ka wai dai gajiya ne, baisakeni ba haryanzu” tafaɗi hakan a taƙaice…
“Kansa yajinjina, haɗe da sake lumshe idanunsa, shi ɗinma ƙarfin haline kawai yasa sa yazo, amma tabbas damuwar dake damunsa tana da yawa.
“Meke damunka, naga gaba ɗaya kamar baka cikin farinciki?” Zahrah ta tambaya cikin siga da yanayi na nuna damuwa..