SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin sanyin daɗi yaji a zuciyarsa, badon komai ba, saidon kulawa da yasamu daga gareta.
Gyara zamansa yayi haɗe da bata duka nutsuwarsa….”Bazan ɓoyemiki ba Zahrah, tabbas inacikin damuwa, kuma duk akan kine, Ina tsananin sonki Zahrah, ina da burin baki farinciki a cikin rayuwarki, amma sai dai na haɗu dake a ƙurarren lokaci, inafata zaki fahimci abun da zance dake?”
Cike da ɗaurewar kai Zahrah take kallon Dr Sadeeq, domin kuwa sam ita bata fahimci inda kalamansa suka dosa ba.
“Mahaifiyata ta zaɓamin matar da zan aura, yanzu haka maganar da nakeyi miki, har ansanya mana rana, saura sati uku”
dummm haka Zahrah taji ƙirjinta yabuga, duk da cewa bata wani jin son Dr Sadeeq a ranta, amma bazata taɓa so kyakkyawan namiji mai nagarta kamarsa ya kuɓuce mata ba, take idanunta suka ciko da ƙwalla wanda batasan na menene ba.
“Dan Allah kada kiyi kuka kinji Zahrah na, nafaɗamiki hakane don kisan halin da nake ciki, amma bawai hakan nanufin bazan aureki bane ba”
Cike da kulawa yakama duka hannayenta biyu, haɗe da kafeta da idanu. Gaba ɗaya abun da yake wakana ya kwashe ya faɗa mata, hatta maganarsa da Baffa Amadu, saida ya sanar da’ita, sai dai ya ɓoye mata ƙiyayya dakuma maganganun da yayarsa da kuma mahaifiyarsa suka faɗa akan ta na ɓatanci.
Cigaba yayi da cewa “Ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawari nan bada jimawa ba, zaki zamo mallaki a gareni, insha Allah zanzamo mijinki Zahrah!”
Hawayene suka shiga zirya akan fuskan Zahrah, cikin murya mai rauni tace ” Dama nasan cewa nayi ganganci, domin kuwa kai ba sa’an aure na bane, nagode sosai da irin kulawa da kuma ƙoƙarin da kayi a kaina, bakuma zan taɓa mantawa da hakan ba, na yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, idan aurena dakai baiyi wu ba, na yarda haka Allah yatsara, tun da fari shiya gurɓatamin rayuwa, ya cutar dani, cuta mafi muni, ta yanda babu wani wanda zai lamuncewa haɗa zuri’a dani, tabbas daman nasan koda kai ka aminta da aurena, ba lallai iyayenka su aminta ba?….Kukane ya ƙwace mata sosai.
Sake damƙe hannayenta yayi acikin nasa, haɗe da kafeta da idanu, sosai tausayinta ya sake kamasa.
“Kinaso nasake shiga cikin damuwa ne Zahrah?” yayi maganar cikin tausasa murya.
Bata iya amasa masa ba, sai gyaɗa masa kai da tayi alamar “A’a”
“To idan har bakyaso nasake shiga damuwa, ki daina kuka kinji Zahrah na, insha Allah, zamu rayu tare dake, harma ki haifamin kyawawan babies, masu kyau kamarki, masu irin idanunki, da bakinki, harma da irin hancinki, da kuma…” sai yayi shiru, yana mai dariya ƙasa ƙasa.
Kunyane ya kama Zahrah haɗe da dariya, duk da kuwa cewa tana cikin halin damuwa, sai kawai ta kawar da kanta gefe, gaba ɗaya jinta take a tsarge sakamakon hanunta da ke saƙale acikin nasa…
“Zantafi saboda naga dare yasoma yi, amma saikinmin alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma za kisa kanki a damuwa ba, idan kikayi haka zanji daɗi sosai”
Abune mai matuƙar wuya, a dake ka sannan a hanaka kuka, amma tabbas zata jarraba wajen daure zuciyarta.
“Bazanyi kuka ba” tafaɗa cikin muryar da bata fita sosai, da badon yana kusa da’ita sosai bana ma to tabbas da bazaiji maitace ba..
“Kinyi alƙawari?” yatambayeta
“Eh” tafaɗi haka bayan taɗanyi jim…..
“Yauwa Zahrah na, nasan ai kina da cika alƙawari, taso muje mota na baki magungunanki” babu musu ta miƙe daga zaunen da take, haɗe da rufa masa baya.
Murfin motar ya buɗe haɗe da fiddo wata ƙatuwar leda.
“Ungo magungunan suna ciki, akwai bayanin yanda zakisha a jiki, please ki kulamin da kanki kinji” yafaɗi haka cikin lallashi, haɗe da miƙa mata ledan dake hanunsa.
Kasa amsan ledar tayi, saima kawar da kanta gefe da tayi.
Murmushi Dr Sadeeq yayi, domin kuwa sarai ya fuskanci hakan da tayi metake nufi.
“Kiyi haƙuri ki karɓa kinji Zahrah na” yakuma faɗan hakan cikin lallashi.
Baki Zahrah taturo gaba haɗe da cewa …
“Kasan tun ba yauba nafaɗama cewa banaso domin kuwa hidiman da kakemin yayi yawa, mai yasa bazaka bari haka ba!” ta tambayesa cike da sakalci..
“Saboda kina da mahimmanci, kinkuma cancani namiki fiye da haka, amma yanzu dai banso kice a’a ki karɓa kinji” still cikin lallashi yayi maganar.. Badon ranta yasoba haka ta karɓi ledan.
“Saida safe” tace dashi cikin sanyin murya haɗe da juyawa ta nufi hanyar shiga gida.
“Kada kimanta kin ɗauki alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma zaki shiga damuwa ba, kada ki karya alƙawari kinji mai kyau na!”
Murmushi kawai tayi masa haɗe da ɗaga masa kai alamar taji.
Yana ganin shigewarta cikin gida, shima yashiga motarsa haɗe da bata wuta yabar unguwar tasu..
Tanashiga cikin gida, Inna tayo kanta haɗe da fusge ledar dake hanunta, babu magana ba komai ta shiga zazzage ledan akan tabarma, kallonta kawai Zahrah ta tsayayi cike da takaici, sai yanzu take godewa Allah dayasanya ba Inna bace ta haifeta, domin kuwa da Innace ta haifeta to tabbas da nan gaba kaɗan zuciyarta zata fashe, saboda wannan halin da Inna keyi ba hali bane na iyayen ƙwarai, batama tsaya ganin menene acikin ledar ba, ta wuce cikin ɗakinta, domin ita dama ba wannan bane a gabanta, yanzu babban damuwarta shine, yanda zata samo maganin matsalarta.
Ɗaukan kwalin nan da aka kawo mata tayi, haɗe da soma kiciniyar buɗewa, kasancewar bakin kwalin a nane yake da wani gam me kyau..
Tana buɗe cikin kwalin wani tsadadde kuma kyayyawan agogo na mata ya bayya, gefen sa kuwa wani irin awarwarone haɗe da zobe masu kyaun gaske, wanda dagani kasan na gold ne, domin kuwa kyawunsu kaɗai ya’isa ya bayyana haka, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da mai da murfin kwalin ta rufe kamar yanda ta samu, ɗaukan kwalin tayi dukansa, haɗe da ɓoyesa a cikin kayanta, dawowa tayi kan katifarta ta kwanta zuciyarta cike tab da tunanin son gano wanda ya soma
bibiyar rayuwarta…
Hajiya Habiba (mahaifiyar Dr Sadeeq) ne zaune akan kujera gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta ta miƙasa ga Baffa Amadu dake zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon…
Baffa Amadu ne yaci gaba da cewa ” Banzo nan don na yi miki dole ba, amma Hajiya Habiba yana da kyau wasu lokutan muna ƙoƙari wajen bawa ƴaƴanmu dama akan abun da suka nuna zuciyarsu naso, musamman ma aɓangaren abun da yashafi aure, haƙiƙa Sadeeq yasameni da wannan maganar yakuma min bayani tayanda zan fahimta, Alhmdlh nakuma fahimta, yanzu saura ke, kada kice wai don ƙaddara ya taɓa faɗa mata, ɗanki bazai aure ta ba, kada kiyi haka, domin ita ƙaddara tanakan kowa mai kyau da marar kyau, sannan abu nagaba danakeso kisani, ko da ace alal misali yarinyar ta kasance karuwa ce, addini bai hana masa auren taba, wala Allah saboda auren saiki ga ta shiryu, balle kuma ma bahakan take ba, amma bazan miki dole akan cewa saikin amince ba, ɗan kine kuma kina da iko akansa”…
Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauƙe, haƙiƙa Baffa Amadu yazo mata da magana mai girma.
ɗan nisawa tayi haɗe da cewa “Bawai naƙi aurensa da ita bane, saboda wani abu ba ne, kawai dai inajiye masa yanda tarbiyan yaransa zai kasance ne matuƙar takasance tana cikin gidansa, domin na tabbatar rashin wadataccen tarbiyan da aka bata a gidansu, shiya jawo faruwar haka a kanta, kaga itama bata samu tarbiya mai kyau ba, balle tayi ƙoƙarin bawa nata yaran, haƙiƙa Sadeeq yarone mai biyayya agareni, kuma harcikin zuciyata na ƙudurta aniyar cewa bazai taɓa auren wannan yarinyar ba, amma tunda harka shigo cikin al’amarin shikenan na’amince, amma kuma fa sai dai idan su biyun duka zai haɗasu ya aura, kaga dai Salima ƴar wajen ƴar uwata ne, haka kuma mamarta aminiyata ce, bayanda za’ayi na watsa musu ƙasa a ido, tahanyar cewa Sadeeq bazai auri Salima ba, kuma kaga yanzu saura ƴan satika ne suka rage, har anriga da anfara shirye shiryen biki”