NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ƙwarai kina da gaskiya ta wani wajen, amma kuma bamu iya ja da haɗin Allah, yanzu zansanar da Sadeeq ɗin duk yanda mukayi dake, zan kuma faɗa masa amincewarki,   nasan shi ɗinma zai amince da umarninki, amma inaga zaifi kyau ayi bikin nasu a rana ɗaya, domin babu amfanin jan lokaci”

“Eh duk yanda kukace shikenan” Hajiya tafaɗi haka badon ranta yaso ba.

“Shikenan to duk dai yanda ake ciki, zai zo yasanar dake” Baffa Amadu yafaɗi haka bayan yamiƙe tsaye ya gyara zaman garen dake jikinsa…

Cike da mutun ta juna sukayi sallama shida Hajiya…

Zama Hajiya tayi afalon haɗe da yin jigum, tabbas ba’ason ranta ta amince da wannan auren ba, saboda ita gani take tamkar yarinyar ba kimtsatstsiya bace,  ta amince ne kawai saboda Baffa Amadu yashigo cikin maganar, kuma tana matuƙar darajasa haɗe da basa girma, domin tana masa kallo ne tamkar marigayi mijinta,  amma da ba haka ba da bazata taɓa amincewa ba, yanzu dai kawai sai dai tayi addu’an Allah yabasu zaman lafiya, amma ta wani ɓangare na zuciyarta, tunani take taya zataje ta tunkari ƴar uwarta Hajiya Furaira da wannan maganar, tasan Hajiya Furaira macece mai zafi,  bazata taɓa son hakan ba, domin saboda bala’inta da zafin kishin ta, ne ma yasanya mijinta haryau yakasa ƙara aure bawai kuma don baya so ba, to ina kuma da idan taji cewa ƴarta ɗaya tilo zata haɗa miji  da wata daban wacce bata da galihu, gaskiya zaiyi wuya ta amince… Haka dai Hajiya tadinga saƙawa da kuncewa daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakinta….

Cikin matsanancin farinciki Dr S.S ke kallon Baffa Amadu sakamakon jin cewa wai mahaifiyarsa ta amince da aurensa da Zahrah, masha Allah ashe  dai mafarkinsa zai zamanto gaskia, sai dai kuma farincikin nasa bai zama cikakke ba, domin kuwa sosai maganar haɗa auren Zahrah da Salima ya daki zuciyarsa, saboda shi a tsarin sa baida burin aje mata biyu acikin gidansa.

“Yanaji kayi shiru ne Sadeeq, ko baka amince da sharaɗin mahaifiyartaka bane?” Baffa Amadu yatambayeshi cike da kulawa.

Kansa yashiga sosawa yamakasa ce da Baffan nasa komai..

Murmushi Baffa Amadu yayi domin yafahimci halin da Sadeeq ɗin yake ciki.    “Kada ka ɗaga hankalinka Sadeeq,  atunanina ka kai namiji wanda zai iya riƙe mace sama da biyu, don haka wannan ba abun damuwa bane, kayarda da sharaɗin mahaifiyartaka, addu’anmu shine Allah yatayaka riƙo, yakuma baka dama da ikon yin adalci a tsakaninsu, yanzu yaushe kakeso muje gidansu ita yarinyar?”

Gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa kuwa jiyayi tayi masa wani iri. “Zansanarda Baffan yarinyar idan yafaɗamin ranan da zakuzo, saina faɗa maka” inji cewar Dr Sadeeq..

“To shikenan Allah yakaimu” daga haka sukayi sallama, Dr S.S yabaro gidan Baffa Amadu zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala, yana farincikin cewa Zahrah zata zamo matarsa, amma kuma ta wani ɓangare na zuciyarsa kwata kwata bayajin daɗi.   Zahrah tana buƙatar farinciki da kuma kulawa mai kyau, baikamata ace anraba mata farinciki ita da wata ba, to amma “Miye mafita?” yatambayi kansa, bayan yasan baida amsar tambayan nasa, amma koma dai mene ayau zaije yasamu Baffa yasanar dashi cewa yana neman abashi izini yaturo magabatansa don abasa auren Zahrah, yakuma ƙudurta aransa cewa, dakansa zai bada order a Dubai, na kayan lefen Zahrah, domin kuwa zaiyi rawar gani sosai, wajen ganin komai na Zahrah yafita da ban….

Amatuƙar mamakance Alhaji Ma’aruf ke kallon Zaid wanda yafaɗi maganar daya matuƙar basa mamaki…. “Aure fa kace Zaid, dagaske kake, yanzu kashirya zakayi aure?”

“Da gaske nake Dad aure zanyi, kuma inaso kaje da kanka ka tambayamin, banaso auren yawuce nan da sati biyu Dad”

Cike da tsananin farinciki Alhaji Ma’aruf yace “Alhmdlh! naji daɗi ƙwarai da gaske, domin zuwa yanzu yakamata ace ka aje iyali, insha Allah, zan je na tambaya maka aurenta, ƴar wayene kuma a ina take?”

“Ba ƴar kowa bace Dad, talakawa ne ma, amma ni ahaka naji na aminta ina kuma son na aureta” yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..

Jinjina kai Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa “Zan sa rana sainaje naga mahaifinta”

“To” kawai Zaid yace haɗe da tashi yabar falon Dad ɗinnasa….

Fitowarta amakaranta kenan, tana sauri ta samu abun hawa, don bata son tsayuwa a bakin makarantar, kasancewar Dr Sadeeq aiki yamasa yawa bazai samu daman  zuwa ɗauko ta ba…

Wani matashin saurayine yanufo wajenta, hanunsa ɗauke da wani babban kwali wanda aka rufesa da wani irin abu mai kyau, aka kuma ƙawatasa da flower mai walwali..

“Ranki ya daɗe barka da yammaci”  saurayin yafaɗa.

“Yauwa barkan ka dai” itama ta mayarmasa amsa cikin ɗari ɗari dashi..

“Saƙo aka bani nakawomiki” yafaɗi maganar yana me miƙa mata kwalin dake hanunsa..

Cikin mamaki Zahrah ta shiga kallon saurayin nan dake tsaye a gabanta..

Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake miƙo mata kyakkyawan gift ɗin dake hanunsa.

“Waye ya aikoka?” tayi masa tambayar cikin dakiya…

“amsar tambayarki duka suna cikin nan” yaƙare maganar yana me nuna mata kwalin dake hanunsa.

Hakanan taji zuciyarta ta aminta da ta karɓi saƙon.. Hanu biyu tasa ta karɓa,  batace dashi komai ba tayi wucewarta dai dai lokacin mai taxi ya ƙaraso tashiga.

Tsurawa  kyakkyawan kwalin  idanu tayi, sosai adon jikinsa yayi kyau haɗe da ɗaukar hankali, gaba ɗaya ta ƙosa, tabuɗe kwalin don ganin ko wanene yake son yin wasa da hankalinta, ta hanyar turo mata da saƙonni, batare da yabari tasan kowaye shiɗin ba.

Tana shiga gida direct ta wuce ɗakinta,  ko mayafinta bata cire ba, ta zauna haɗe da soma yaye ledan da akayimawa kwalinnan ado dashi,   tana buɗe kwalin tayi arba da wani ƙatuwar ta karda wanda aka naɗeta,  cikin sauri ta ɗago takardan haɗe da soma warwareta, amatuƙar razane tayi wurgi da takardan sakamakon idanunta da sukayi mata tozali da zanen hoton dake jikin takardan.

(????Ga Zaid ga Sadeeq ko waye cikinsu zai mallaki Zahrah????‍♀)

17/December/2019

Follow me …
Wattpad user name @fatymasardauna
????????????????????????????????????????

         SHU’UMIN NAMIJI!!

     
        Written By
  PHATYMASARDAUNA
   (Shalelen Kainuwa)

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            WATTPAD
      @fatymasardauna

Editing is not allowed????

     CHAPTER 61 to 62

Idanu ta ƙara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata.

Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raɗau ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durƙusa ƙasa, haɗe da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaɗince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani,   hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haɗe da ɗaurewar kai.

Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waƴan nan abubuwan,  kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saƙonni, bata kuma san daga waye bane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button