NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Hadari ne yahaɗu sosai acikin garin, yayinda sama tayi baƙi, ruwa ake tsammata yanzu ko anjima, yau amakare suka fito da ga exam, duk yanda Husnah taso Zahrah tashiga su rage mata hanya ƙiyawa tayi dole yasa Husnah ta ƙyaleta, tana fitowa daga cikin makaranta, ruwa ya ɓarke tamkar dama jira ake tafito, duk adaidaita sahun da Zahrah tatare baya tsayuwa, domin ruwan ƙara ƙarfi yake, jikin wata bishiya Zahrah ta lafe, duk da kuwa cewa ruwan baifasa dukanta ba, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe jagwab, ba abun da kayanta suke sai ɗigan ruwa, rigace irin rover gown ɗinnan ajikinta, saikuma rover hijab da taɗaura akan rigan, sanadin jiƙewan da sukayi yasanya, kayan lafewa acikin jikinta, take komai najikinta ya bayyana, hatta shatin breast ɗinta saida yabayyana, domin rigar ce kaɗai ajikinta, batasa breziya ba,, abu kamar wasa haka aka share 1 hour ana tafka ruwan sama, gashi duk bayan minti ɗaya dare ƙarayi yake, sanin cewa tsayuwarta a wajen kan iya haifar mata da matsala, yasanya ta shiga tafiya a cikin ruwan duk da cewa bata ko iya ganin gabanta,, gudu kawai yake shararawa akan titin batare da yayi tunanin komaiba, daidai Zahrah tahau kan tsakiyar titin, dai dai shikuma yaƙaraso wajen,,, wani irin burki Zaid yataka da ƙarfin tsiya, domin ƙiris yarage yabita kanta,, Zahrah kuwa tsabar firgici kasa motsawa tayi daga wajen, hannayenta taɗaura akan kunnenta haɗe da rumtse idanunta gam,, tundaga ƙasanta yasoma kallonta harzuwa samanta, saurin rumtse idanunsa yayi alokcin da idanunsa suka hasko masa shatin nipples ɗinta daya bayyana tacikin hijabinta, ” wayyo Allah na !!” yafaɗa a hankali, yayinda ya sanya hanunsa yariƙe bananarsa da alokaci guda tayi wani irin harbawa,, cikin rashin ƙarfin jiki da kuzari yafito daga cikin motar haɗe da nufar inda take,, kallon fuskarta yashiga yi, jin hucin numfashin mutum akusa da’ita yasanyata buɗe idanunta ahankali, sake waro idanunta tayi domin ganemawa kanta shin abun data gani gaskiya ne ko ƙarya, kyakkyawar fuskarsa tashiga ƙaremawa kallo, tamkar taga baƙon halitta, waishin aljanine ko mutum ? tatambayi zuciyarta, kallon kallo Zaid da Zahrah suka shiga yimawa juna, yayinda ruwan sama keta dukansu, tsareshi tayi da idanunta, bata ko ƙyaftawa, ahankali yakai hanunsa zuwa kan fuskarta yashafa kumatunta, saurin ja da baya Zahrah tayi, haɗe da ƙwalalo idanunta waje, abun da wani ɗa namiji baitaɓa yi mata ba aduniya kenan wato taɓa jikinta, saidai ko muharraminta,, wani irin munafukin murmushi daya ƙawata zallan kyauwunsa yayi haɗe da komawa cikin motarsa yazauna, ƙofan dake gefen mai zaman banza ya buɗe, haɗe dayi mata nuni da hanunsa alamar tashigo, tsoro ne yakama Zahrah, amma tabbas bata da wani dama dayawuce tashiga motar tasa, domin idan ta tsaya tofa saidai ta bushe amma bazata samu abun hawaba gashi dare sai ƙarayi yake,, sumi sumi haka tashige cikin motar tazauna haɗe da takure jikinta waje ɗaya,, kallonta yayi tagefen ido haɗe dayi mawa motar tasa key, batare daya ce da’ita ƙalaba suka soma tafiya,, cike da tsananin mamaki take kallonsa ganin da tayi kaitsaye yanufi hanyar Suleja da’ita batare da ya tambayeta ba, saida suka kawo daidai inda yataɓa ganinta kafun yayi parking motar tasa haɗe da juyo da kallonsa gareta wani irin shu’umin kallo yajefeta dashi haɗe da cewa ” inane gidan ?” kasa amsa masa tayi saima baki da tasake tana kallonsa kamar tasamu statue (gunki), a hankali ya hura mata iskan bakinsa akan fuskarta, take tayi saurin kawar da kanta gefe, “kabarni anan ma ya’isa nagode ” tafaɗa a taƙaice haɗe da yunƙurin fita daga cikin motar, saurin riƙo hanunta yayi haɗe da cewa “Kifaɗamin inane gidan ?” yayi maganar cikin wata irin cool voice maisanya nutsuwa,, “kwanancan ne ” tabasa amsa a taƙaice,,, a dai dai ƙofar gidan su yayi parking motar tasa, saurin buɗe murfin motar Zahrah tayi haɗe da ficewa, hartana jin tuntuɓe wajen shiga gida, tsabar sauri,, wani irin murmushi Zaid yayi, haɗe da fito da harshensa ya lashe pink ɗin laɓɓansa, “Sugar Baby !!” yafaɗa in a low voice, yakai kusan 2 minutes aƙofar gidan kafun yaja motarsa yatafi…….

15/October/2019

 *MRS SARDAUNA*

????????????????????????????????????????

      *SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*

phatymasardauna
????Mrs Sardauna????

Dedicated To My Lovely Brother Khabeer

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
    *WATTPAD*

@fatymasardauna

Editing is not allowed ????

Chapter 8 то 9

Koda Zahrah tashiga gida bata iske kowa a tsakiyar gidan ba, don haka kai tsaye ɗakinta tawuce, kayanta dake ɗigan ruwa ta cire haɗe da ɗaura zani a ƙirjinta, fita tayi ta shanya jiƙaƙƙun kayan nata akan igiya, kana ta dawo ɗaki, wata doguwar riga mai kauri tasanya domin sosai takejin sanyi a cikin jikinta, zama tayi akan katifarta haɗe da lumshe idanu, saurin ware idanunta tayi, alokaci guda, bakomai yasa hakanba kuma face, kyakkyawar fuskar mutumin ɗazu dake yi mata gizo acikin idanunta, tsikar jikinta ne yashiga zubawa, sakamakon tunowa da yanayinsu naɗazu da tayi, “Yanada kyau !!” tafaɗi maganar a fili, amma anya ba gamo kikayiba kuwa Zahrah ?” zuciyarta taje fomata wannan tambayar, take kuma tsoro yashiga zuciyar Zahrah saikuma tafara addu’a idan Aljani ne ma Allah yarabata da sharrinsa…..

Zaid kuwa daga gidansu Zahrah nasu gidan yayi, koda yacire kayan dake jikinsa kwanciya yayi luf akan makeken gadonsa, yanamai sauƙe ajiyar zuciya, lallai yau yayi gamo da gamdakatar, ashe gaskia Bash keyi da ya ce masa a area’n akwai kyawawan ƴan mata, saidai a yanda ya fuskanta ita ɗin ba ƴar hannu bace, domin ya hango hakan acikin idanunta,, murmushi mai sauti Zaid yayi haɗe da cewa “Kisaurari dawowana gareki My Sugar Baby !!”…..

Bayan Sati Ɗaya da haɗuwan Zahrah da Zaid….

Tun randa Zahrah ta haɗu da wannan haɗaɗɗen gayen hankalinta ya kasa kwanciya, ko kwanciya bacci tayi, to fa shike zuwa mata a mafarkinta, dazaran tarufe idanunta kuwa kyakkyawan murmushinsa take gani, duk yanda taso yakice tunaninsa acikin zuciyarta hakan yacitura, saidai ako dayaushe tana mai gargaɗin zuciyarta da ta tsaya a iya matsayinta, kada ta haura matsayin da bata can can ci zuwa ba..

Ɓangaren Zaid kuwa iskancinsa yake bugawa son ransa, zina ƙara yaɗuwa takeyi a cikin jini da zuciyarsa,, yau yashirya cewa zaikai mawa Sugar Baby ɗinsa ziyara,,

Tsab yashirya kansa cikin wasu irin tsadaddun riga da wando, na blue jeans, bakaɗan ba kayan suka amshi kyakkyawan jikin Zaid, yayinda tulin gashin kansa yasha gyara sai sheƙi yake, agogon rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hanunsa, haɗi da baɗe jikinsa da shu’umin turarensa mai rikirkita ƴan mata,, haƙiƙa Zaid yana da kyau mai burgewa, Zaid haɗaɗɗen Namiji ne wanda kowacce mace idan tagansa saita ƙyasa, bazan iya misalta muku haɗuwar Zaid ba amma Zaid ya wuce duk inda kuke tunani,ga kuɗi ga kyau, shiyasa yake abun da yakeso,,, car key ɗinsa ya ɗauka haɗe da ficewa daga cikin ɗakin,, kaitsaye parking space ɗinsa ya nufa, haɗaɗɗiyar motarsa ƙirar Range Rover blue colour yashiga haɗe da bata wuta yafice daga cikin gidan,, yana tuƙi amma earpiece ne sanye a kunnensa yanashan ƙiɗa, kai tsaye Unguwar Suleja yanufa,,

Zahrah ce zaune a tsakar gida, tana wanke mawa inna kayanta, sanye take da wata atamfa irin mai sauƙin kuɗinnan amma, duk da haka atamfar tayi mata kyau ajiki, Inna kuwa nagefe akishingiɗe tana sana’artata cin goro,, wani yaro ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, Zahrah ce ta amsa masa Inna kuwa ko kallonsa batayi ba, domin a tunaninta baraka dake binta bashine ta aiko mata,, ” Wai Zahrah tazo inji wani a waje ” yaron yafaɗa, zuciyar Zahrah ce tayi wani irin tsalle tamkar zata fito waje, yayinda inna dake kishingiɗe tamiƙe zumbur haɗe da cewa ” Zahrah kuma ? kai yaro anya kaji da kyau kuwa ?” kai yaron yagyaɗa haɗe da cewa “Eh wani ne yace inkirata, kuma Zahrah yacemin,,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button