NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta ɓoye acikin kayanta.

Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani, amma kuma rainin hankalin yayi yawa, dole zataimawa tufkar hanci. Abun da ta ƙudurta kenan acikin zuciyarta domin iskancin yasoma isarta.

Ƙarfe 6:30 na yammaci Dr Sadeeq yayi wa gidansu Zahrah tsinke, bayan yasha adon sa cikin riga da wando na shadda ƴar bugu mai kyau. Zama yayi acikin motarsa yana mai jiran fitowar Zahrah, domin kuwa yamata waya yasanar da’ita cewa gashi nan, a ƙofar gidansu.

Kafeta da idanu yayi domin kuwa bakaɗan ba tayi masa kyau, cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, lallai Zahrah ƙarshe ce wajen haɗuwa dakuma kyau.

Fuskarta ɗauke da murmushi Zahrah ta ƙaraso wajen da motar tasa take fake.  Tsayawa tayi ajikin motar, batare da ta buɗe tashiga ba. Ganin haka yasa Dr Sadeeq buɗe murfin motar yafito.

“Yau kuma aji ake jamin  ne?” ya tambayeta cikin yanayin tsokana.

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da juya idanunta.    “Eh mana, ko bankai naja aji bane?” itama ta tambayesa cikin yanayi na shauƙi.

“Murmushi yayi haɗe da ɗage giransa sama “Kin isa har kinma wuce, ko bakisan cewa keɗin tamusamman bace?”

Hararan wasa Zahrah ta wurgamai haɗe da kawar da kanta gefe, batare da tace dashi komai ba. Haka take al’adar ta ne, bakoda wani lokaci take bada amsar tambaya ba, domin a cewarta shiru ma magana ne.

“Kona zagayo na buɗe miki murfin motar ne gimbiyata, saboda  naga kamar bazaki iya ba ?” yafaɗi hakan cike da kulawa.

“A’a ba buƙatar hakan, ni dakaina ma zan iya” taƙare maganar tana mai buɗe murfin motar, haɗe da shiga tayi mawa kanta mazauni.

Shima komawa yayi cikin motar ya zauna. Bayan ya ɗaura duka idanunsa a kanta.

“Kinyi kyau sosai, fiye da ko yaushe” yafaɗi haka yanamai kashe idanunsa.

Ɗanguntun murmushi Zahrah tayi “Nagode” tace dashi ataƙaice

Jinjina kansa yayi azuciyarsa kuwa cewa yayi “Lallai Zahrah tana da aji, duk da ta rasa Virginity ɗinta hakan baisanya ta zama wata sakaka da’ita ba, yanason mace wacce ta’iya takunta, wacce bata sakar baki tayita dariya like mental problem, wasu matan da zaran kace dasu sunyi kyau tofa take zasu wage baki suita ƙyaƙyata dariya,  babu wani ɗan jan aji ba komai.  nima shaida ce irin su Sister Munubiya idan kace dasu sunyi kyau ae har kyautan kuɗi zasu baka tsabar daɗi????”

Sake gyara zamansa yayi haɗe da dawo da nutsuwarsa zuwa gareta.

“Zaki’iya zama dani a ko wani irin hali Zahrah?”
Ya jefomata tambayar da bata tsammaci jinsa ba.

Cikin yanayin mamaki Zahrah ta dawo da kallonta garesa, haɗe da cewa “Banfahimci maikake nufi ba”

“Inanufin zaki iya rayuwa dani ako wani irin hali na tsinci kaina? sannan zaki iya yarda na haɗaku ku biyu na aura?” yakuma maimaita tambayar tasa.

Dummm haka Zahrah taji ƙirjinta ya buga, idan da badon kada yace ta rainasa ba, to tabbas da zatace dashi yasake maimaita maganar da yayi. Domin idan kunnuwanta sunjiye mata dai dai, to kuwa bata da amsar da zata basa, domin koda ta basa amsa zata iya faɗuwa, saboda balallai ta bashi amsa dai dai da abun da ya tambaya ba.

Idanunsa duka ya tsura mata,  amsa kawai yakeson ji daga bakinta.

Kasa ce dashi komai tayi, domin kuwa haryanzu bata gama haɗa amsar da zata basa ba.

“Nasani dama ba lallaine ki amince ba, Hajiya na ta amince da aurena dake, amma kuma kamar yanda nafaɗamiki a baya, tun tuni akwai zaɓin da tayimin, takuma umarceni da na aureku duka biyu, shin zaki iya aurena a haka, zaki iya zama da wata a matsayin kishiyar ki?”  yafaɗi hakan cike da zaƙuwan son jin amsa daga gareta.

Jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, take taji zuciyarta ta karaya, batasan ya’ake zama da kishiya ba,  haryanzu ita yarinyace, bakomai tasani  na game da al’amarin duniya ba, tanaji a labarai irin illan da kishiyoyi suke mawa junansu saboda kishi, amma ita yanzu ba wannan bane a gabanta,  makomarta na gaba take tunawa, shinya zata kasance?” ta tambayi zuciyarta…

“Kinyi shiru kice wani abu  mana zahrah ko zuciyata zata daina bugawan da takeyi” Dr yafaɗi hakan cikin yanayin damuwa.

“Bazan taɓa ƙin aurenka ba, sai dai idan har kaine kace kafasa aurena, sai dai kuma inajin tsoro, bansan mene zai kasance dani gaba ba, dan Allah kada soyayyar matarka ta ruɗeka, ka wulaƙantani, banda wani madogari sai ALLAH sai kuma kai” taƙare maganar cikin rawar murya, yayinda idanunta sukayi rau rau dasu, alamar zasu zubda ƙwalla.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, haɗe da sakin ɗan taƙaitaccen murmushi.   “Har abada kada kitaɓa tunanin zan wulaƙantaki Zahrah, inasonki da gaske bada wasa ba,  namiki alƙwari zan kamanta adalci a tsakaninku, bazan juya miki bayaba insha Allah!” Doctor Sadeeq ya faɗi haka cike da lallashi.

Tuni idanun Zahrah suncika da ƙwalla, amma idan ta tuno cewa bata da zaɓi sai taji gwamma kawai ta daure zuciyarta, haka ta ta ƙaddaran take.

“Kada kiyi kuka kinji My Princess, ina tare dake ako wani lokaci,  zankuma share miki dukkanin hawayenki nan bada jimawa ba namiki alƙawari”

Saurin maida hawayenta tayi haɗe da ƙaƙalo murmushin dole ta’aza akan fuskarta, wan nan damuwarta ne ita kaɗai, baikamata ace tabari Dr Sadeeq yagane ba, lallai tun yanzu yakamata ta zama mai juriya.

“Baffa yana gida kuwa?” Dr. Sadeeq ya tambaya.

Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da kaɗa masa kai alamar “Eh”

Kai yajinjina haɗi  da cewa “Yanaga duk jikinki yayi sanyi? banace kada kisa damuwa a ranki ba” cikin kulawa yayi maganar.

Cike da shagwaɓa Zahrah ta langwaɓar  da kanta gefe haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba,  “Nibansa damuwa a raina ba”  tace haka cikin sanyayewar jiki.

Wani irin kallo maiɗauke da ma’anoni masu yawa Dr.Sadeeq yashiga yi mata, ji yake tamkar yajawota jikinsa ya rungumeta tsam acikin ƙirjinsa,   saboda ako da yaushe idan yana tare da’ita wani irin feeling yakeji a jikinsa.

“Kije kimin sallama da Baffa inaso zamuyi magana” 

“To” kawai tace dashi haɗi da buɗe murfin motar tafita. Dakallo kawai ya bita harta shige  gida.

Tana shiga cikin gida ta iske Baffa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinsa.

“Zahrah har kindawo? badai likitan yatafi ba?” Baffa yajeromata tambayoyi alokaci ɗaya.

“A’a baitafi ba Baffa, shine ma yace nace ma yana son magana dakai” Zahrah tafaɗi haka ga Baffa cikin girmamawa.

“To Allah yasa lafiya, yanzu kuwa zanje na sa mesa”   ya faɗi  maganar yana mai nufar hanyar fita daga gidan.

Zahrah kuwa ɗakinta takoma.
Sosai maganar Dr.Sadeeq yataɓa mata zuciya,  bakomai take hangomawa kanta ba, sai yanda makomarta zai kasance acikin gidansa, tabbas ta tabbatar wacce zai aura, ba irin ta bane, tasan tana da galihu, saɓanin ita da take ko oho, sannan kuma dole zata ga banbanci daga ƴan uwansa,  haka ma Dr.Sadeeq ɗin dole zai banbantasu, saboda waccar zai sameta a budurwa, saɓanin ita da zai sameta ba’a budurwa ba,  kukane yaƙwace mata  mai sauti,  cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tashiga rera kukanta,  har abada cutar da Zaid yayi mata bazai  taɓa gushewa ba…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button