NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Alhmdlh masha Allah! haƙiƙa naji daɗin wannan magana taka Likita, lallai kacika mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, Allah yasaka ma da gidan Aljanna, kuma idan dai Zahrah ce kada kaji komai natabbatar itama tana ƙaunarka, saboda haka nabaka izini ka turo magabatanka, don mu tsaida magana,kuma maganar bayarwa nabaka Zahrah!” Baffa yafaɗi haka cikin farinciki, duk da kuwa  cewa dama tun abaya yasan cewa Dr.Sadeeq yanason Zahrah, amma sake tabbatar masa da Dr. ɗin yayi yanzu, yasanyashi jin daɗi, domin shima yanzu burinsa shine ya inganta farincikin marainiyar Allah wato Zahrah..

Farinciki ne sosai yakama Dr.Sadeeq, yaji daɗin aminta dashi da Baffa yayi.

“Nagode da wannan dama da kabani Baffa, Allah yajiƙan magabata” Dr Sadeeq yafaɗa cike da girmamawa.

“Mune da godiya Likita, ai mu ba’abun da zamuce maka saidai fatan alkhairi” Baffa yafaɗa shima cikin jin daɗi, domin yasan Zahrah na auren Dr.Sadeeq wahalanta yaƙare da yardan Allah,saboda yana da tabbacin cewa Dr.Sadeeq zai bata kyakkyawan kulawa, duk da kuwa cewa Dr.Sadeeq ɗin yasanar dashi cewa ba Zahrah ita kaɗai zai auraba, yasanar dashi komai, kuma Baffa yayi na’am da hakan, saboda shi baimaga wani aibu acikin hakan ba, ai namiji mijin mace huɗu ne.
(Nima nace wannan gaskia ne, sbd haka duk me mace ɗaya ya ƙara????????)

Cike da farinciki Baffa da Likita sukayi sallama, yayinda Baffa yakoma cikin gida, ya kumace da Dr.Sadeeq zai turo masa Zahrah suyi sallama.

Tanajin Muryan Baffa a tsakar gida, tayi saurin share hawayenta, haɗe  da miƙewa tsaye, domin har Baffa yafara ƙwaɗa mata ƙira.

Fuska cike da fari’a Baffa yace “Likita ke yake jira, zai tafi”

Sumi sumi haka Zahrah ta fice yayinda tabar Baffa yana gayamawa Inna abun da ya wakana tsakaninsa da Likita.

Tun fitowarta yake ta zabga murmushi, kallo ɗaya zakai mawa fuskarsa ka gane cewa yanacikin farinciki.

“Kitayani murna My Princess saura ƴan kwanaki ƙalilan na mallake ki!” Dr Sadeeq yafaɗi haka cike da shauƙi.

Kunyane yakama Zahrah, don haka ta sanya duka hannayenta biyu ta rufe fuskarta, bayan ta ƙaƙalo murmushi ta aza akan fuskar ta..

“Baffa yabani daman naturo magabatana don asa mana ranan aure, kuma insha Allah, gobe magabatana zasu zo, za’asa ranan aurenmu nan bada jimawa ba,  so sai ki shirya domin kin kusa zama amaryata!” yanayin yanda ya ƙare maganar kaɗai ya isa taɓa zuciya..

Kunyane yasake kama Zahrah, har batasan sanda murmushi mai sauti ya kufce mata ba,  gaba ɗaya ta lura Dr.Sadeeq ya ƙosa da ayi aurensu bata kumasan dalilinsa nayin hakan ba..

“Kinyi shiru kodai bakya farinciki ne my princess?” yatambaya.

Ɗan satan kallonsa tayi haɗe da sakarmasa murmushi mai tsayawa a zuciya.

Ƙaran wayarsane ta katsesa daga kallonta da kuma zancen zucin da yakeyi.  Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin wacce take ƙiran nasa,  maida wayar tasa cikin aljihu yayi batare daya ɗaga ƙiran ba.

“Dare yayi Zahrah kishiga gida, zamuyi waya, kikulamin da kanki ”   yafaɗi hakan yana me ƙoƙarin shiga cikin motarsa.

Murmushin dole Zahrah tayi haɗe da yi masa saida safe, tajuya ta nufi cikin gida, hakanan taji wani iri a zuciyarta duk da batasan me yasa baiɗaga ƙiran da ake mai ba, amma tana da yaƙinin cewa matar da zai aura tare da itane ta ƙirasa. Saurin kawar da tunanin tayi aranta, domin tuna hakan ma bashida amfani a gareta.

Washe Gari….

Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakanne ya kasance da  da dare bayan sallan magriba Baffa Amadu shida amininsa suka zo gidansu Zahrah don tambayan aurenta, balaifi Baffa yayi musu tarba mai kyau, sunkuma ji daɗin hakan, duk da sun lura cewa suɗin  basuda wani  ƙarfi, ma’ana arziki…

Magana ta fahimta akayi tsakanin Baffa da kuma Baffa Amadu,  a taƙaice dai Baffa yabasu auren Zahrah, yayinda sukuma suka ɗau alƙawarin cewa a cikin satin za’akawo kayan tambaya dakuma na lefe, daga nan sai asa ranan aure, amma basason auren ya ɗau lokaci, saboda rana ɗaya suke so ayi dana Salima.. Da to kawai Baffa ya amsa musu domin shi baida wani abun cewa banda hakan, sai dai a ƙasan zuciyarsa tunani yake taya zai samu kuɗin da zaiyi mawa Zahrah kayan ɗaki, domin dai bayanda za’ayi ace anyi aure ba kayan ɗaki… Haka dai sukayi sallama cike da mutun ta juna…

Baffa ne Zaune akan tabarma ya yi jigum bakomai ke damunsa ba, kamar sha’anin auren Zahrah, Allah yasani ko abincin da za’aci abikin bai tanada ba, balle wata uwa uba kayan ɗakin da za akaita dashi..

“Wai tunanin mekakeyine haka tun ɗazu?” Inna dake zaune gefensa ta jefo masa tambaya.

“Ba dole nayi tunani ba Salame, kinga dai yau iyayen yaron nan Sadeeq suka zo, kuma da duk kan alama basa so aja auren nan yakai wani lokaci, kin kuma san halin dai da muke ciki na rashin kuɗi”

“Yo dama akan wannan kake ɗaga hankalinka? hmm Malam kenan to ai ni banga abun ɗaga hankali anan ba, ca nake shi Sadeeq ɗin yasan duk halin da muke ciki, kuma shi yakawo kansa yace ya na so, bawai mu makai masa dole ba,  saboda haka malam ka kwantar da hankalinka, Zahrah ya nema kuma Zahrah’n  zamu bashi” Inna tafaɗi haka da’iyaka gaskiyarta…

Kallon Inna kawai Baffa yayi haɗe da girgiza kansa,  yasan ma koda yayi ƙoƙarin fahimtar da’ita to fa bazata fahimta ba.


“What? Mom cewa fa kikayi wai bani kaɗai Sadeeq zai aura ba, anya kuwa Mom kinji abun da Hajiya Habiba tafaɗamiki da kyau?” Salima tatambayi mahaifiyarta Hajiya Furaira cike da mamakin jin abun da mahaifiyarta tace da’ita..

“Abun da na faɗa miki shi naji daga bakin Hajiya Habiba, Salima kicire Sadeeq a ranki, domin kuwa aurenki dashi bazai taɓa yiyuwa ba, da raina dakuma hankalina bazan taɓa bari ƴata taje kan kishiya ba!” Hajiya Furaira tafaɗi haka cikin ɓacin rai..

Kuka ne ya ƙwacemawa Salima cikin muryan kuka ta soma cewa “Wani irin cin amana ne wannan mom, sai da maganar aurena dashi ta kankama sannan wata banzar magana zata ɓullo,  wallahi bazan haƙura da shi ba, bakuma zan taɓa zama da wata a matsayin kishiyata ba, dole ne Sadeeq ya aureni ni ɗaya batare da wata ba, bazan iya jure rashin saba Mom, dan Allah kiyi wani abu” Salima ta ƙare maganar cikin shaɓe shaɓe da hawaye. 

“Mekikeso nayi Salima? so kike naje na basu haƙuri akan su sa Sadeeq ya aureki ke kaɗai? ko ko sokike na zubar miki da ƙima daƙuma ƴancinki?  Hajiya Habiba ƴar uwatace kuma ƙawata, bantaɓa tunanin haka daga gareta ba, amma bakomai, zanyi maganin abun, kuma ni banzauna da kishiya ba, ƴa tama bazata zuana da kishiya ba, wannan alƙawarine na ɗaukar mawa kaina” still cikin ɓacin rai Hajiya Furaira take maganan…

Cikin matsanancin ɓacin rai Salima ta juya ta koma ɗakinta, ji takeyi zuciyarta na tafarfasa, kamar ita ace ta haɗa miji da wata, sam bazai yi wuba, lallai ko da mahaifiyarta bazatayi wani abu ba yakamata ace ita tayi, wayarta da mayafinta ta ɗauka, a fusace ta fice daga ɗakin nata, tana son Sadeeq tun ba yau ba, zata kuma iyayin komai akan sa.

Ɓangaren Dr Sadeeq kuwa tuni yasoma haɗa mawa Zahrah kayan lefe, sosai yake iya ƙoƙarin sa wajen ganin yasanya duk wani abu da yasan zai burge Zahrah.
Ɓangaren Hajiyarsa da Aunty Raliya kuwa, sam basu wani damu da auren ba, hakanne ma yasa suka tura masa aniyarsa, su dai sunfi bada ƙarfi wajen ganin Salima tasamu abun da take so, yayinda Hajiya Furaira ta kafe kan cewa ƴarta bazata auri Sadeeq ba matuƙar ba’a fasa aurensa da Zahrah ba, ranta bai ƙara ɓaci ba ma, sai da taji labarin cewa Zahrah ƴar talakawa ne, sannan kuma bata da wani galihu, ai take ranta yaƙara ɓaci, tace sam bata amince ba, yayinda Salima kuwa ta kafe akan cewa lallai sai ta ruguza auren da Dr.Sadeeq yake nema bayan nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button