SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba ɗaya Zahrah ta ruɗe, zuwa yanzu wanda yake turo mata saƙo ya uzurawa rayuwarta, a yanda ta fahimta shine duk inda tayi yana biye da’ita, wani babban tashin hankali daya kunnu mata shine, sabbin saƙonnin da yafara turo mata a cikin wayarta, tagama iya hasashenta ko zata gano a ina yasamu number’n ta amma takasa samun daman sanin inda yasamu number’nta, gaba ɗaya yanzu salon saƙonnin nasa sun sauya salo, domin kuwa yanzu saƙon kalamai yaƙe turo mata masu daɗi, wanda kuma duk rabin saƙon yaba kyawunta yake, babban abun daya ƙara ruɗata shine irin maƙudan kuɗaɗen dayake turomata ta waya. sannan kuma idan ta gwada ƙiran number’n da yake turo mata saƙo dashi, bata samu domin da zaran taƙira wayan za’ace mata a kashe wayar take, hakan yasa tafara tunanin cewa kodai gamo tayi…
Ɗan ƙara wayarta tayi alamar shigowar saƙo, take taji gabanta yafaɗi, zuwa yanzu har tsoro take taji wayarta tayi ƙara, domin kuwa tasan idan har wayanta tayi ƙara to ko ƙiran Dr.Sadeeq ko kuma saƙon mutumin da batasan shiba…
Number’n nan ce dai, da aka saba turo mata saƙo dashi, yauma saƙonne aka kuma turowa..
Tunaninki ya hanani sukuni My Zahrah, ina fatan dai kina lafiya, ina kuma fatan zuwa yanzu kindaina tsoro da kuma mummunan tunanin da kikeyi akaina, kina da kyau My Zahrah, komai naki me kyau da burgewa ne.
Abun da saƙon ya ƙunsa kenan.
Zahrah ta karanta saƙon nan yafi sau biyar, kwata kwata ta kasa fahimtar abun da saƙon yake nufi.
Saurin yin Deleting saƙon tayi haɗe dayin switch off ɗin wayar tata, bazata taɓa yarda wan nan mai saƙon ya haukata mata tunanin ta ba, yazama dole a gareta ta sanja layi.. Kwanciya tayi lamo tana mai addu’an Allah yasa bacci ya ɗauketa. domin bacci ne kaɗai zai kawo mata sauƙi a zuciyarta.
Zaune suke dukansu a ɗan madai dai cin tsakar gidan nasu, domin dama idan dare yayi sukan zauna a tsakar gida su ɗan taɓa hira, haka al’adarsu take..
Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, haɗa baki sukayi wajen amsa masa sallaman.
“Wai ana sallama da mai gidan nan” yaron yafaɗa.
“To kace inazuwa” Baffa yafaɗi haka yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
Kusan tare suka fita shida yaron sai da Baffa yaji wani irin faɗuwar gaba sakamakon wasu irin danƙara danƙaran motoci guda biyu da yagani fake a ƙofar gidansa.
Ja Baffa yayi ya tsaya turus yana me mamakin ganin waƴan nan rantsatstsun motocin a ƙofar gidansa, “Allah yasa da alkhairi suka zo” Baffa yafaɗi haka a cikin zuciyarsa.
Buɗe murfin motar Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da sako ƙafarsa waje.
Sake waro idanu Baffa yayi haɗe da kafe Alhaji Ma’aruf dake ƙoƙarin fitowa daga cikin mota da ido.
Fuska cike da annuri Alhaji Ma’aruf ya ƙaraso wajen Baffa, haɗe da miƙa masa hanu alamar su gaisa.
Cikin ɗari ɗari Baffa ya ɗago hanunsa haɗe da miƙamawa Alhaji Ma’aruf suka gaisa.
“Inafatan kaine ma mallakin wannan gida, kuma Baffa ga Zahrah?” Alhaji Ma’aruf ya tambaya.
Saida Baffa yaji zuciyarsa tayi tsalle sakamakon jin an ambaci Zahrah, Allah yasa ba wani abun Zahrah tajawo musu ba.
“Eh nine ranka ya daɗe, Allah yasa lafiya?” cikin dar ɗar Baffa yafaɗi hakan.
Murmushi irin nasu na manya Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da kallon Baffa…”Nazo da magana mai mahimmanci, inaga zaifi kyautuwa kabiyoni cikin mota mu tattauna, don maganar bata tsaye bace”
Kallon Alhaji Ma’aruf Baffa yashiga yi, haɗe da excort ɗin da suke bayan Alhaji’n, tabbas Alhaji Ma’aruf baiyi masa kama da irin mugayen mutanen nan ba, domin daga ka gansa zaka fahimci cewa dattijon arziki ne, hakanne yasa Baffa bai musa masa ba, yabisa zuwa mota..
Acikin mota kuwa bayan sun sake gaisawa, Alhaji Ma’aruf yayi gyaran murya haɗe da cewa…
“Sunana Alhaji Ma’aruf, kasancewar dare ne yasanya ka kasa shaida fuskata, domin ni ba ɓoyayyen mutum bane. Nazo gare ka ne domin nemawa ɗana Auren Ƴar Wajenka Zahrah, ina fatan bazaka watsa mini ƙasa a ido ba”…….
(Kowani amsa Baffa Zai bawa Alhaji Ma’aruf????)
19/December/2019
Follow me on Whatsapp and Wattpad
Wattpad user name fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
(shalelen kainuwa)
Dedicated To MY Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
(Wannan page ɗin gaba ɗayansa ƙyautane a gareku Maman Teemah, and Ummu Fateema, inaƙaunarku Momy’s ɗina)
Editing is not allowed????
CHAPTER 63 to 64
Shirune yashiga tsakanin Baffa dakuma Alhaji Ma’aruf, bakomai ne kuma yasa hakan ba face nazari da Baffa yashigayi, lallai wannan abu da mamaki yake, neman aure mace ɗaya duk alokaci guda.
“Naji kayi shiru, Allah yasa dai ba wata matsala bace ta faru” Alhaji Ma’aruf ya faɗa, domin ko kaɗan baya fatan wani abun da zai zo ya gifta har ya katsewa Zaid cikar burinsa..
Gyara zama Baffa yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya..
“A gaskiya Alhaji bazan ɓoyemaka ba, yanzu haka na bada auren Zahrah ga wani, wanda kuma tariga da ta aminta dashi, sai dai bazan yi saurin yanke hukunci ba, idan har Zahrah ta aminta dashi ɗan wajen naka, shikenan, saboda ni bazan mata dole ba, duk wanda takawo tace shitake so, to shi zan aura mata, amma kuma a iya sanina babu wani wanda yake zuwa wajenta, bayan likita’n dana bashi aurenta, sai dai kuma bansan shi ɗan wajen naka a ina yaganta har yaji yanada burin aurenta ba”
Ɗan jim Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. Lallai yakamata yayi duk abun da zaiyi, domin shikansa yanaso Zaid yayi aure, amma kuma yasan cewa nema cikin nema haramunne, tunda gashi har shi Baffan yarinyar ya ri ga daya shaida masa cewa yabada auren yarinyar ga wani, yazama dole suyi haƙuri kenan.
“Naji maganarka Malam Hayatu, nakuma gamsu, amma bayar da aurenta ga wani, ae bashi yake nufin anɗaura aurenta ba, koda yaushe ra’ayin mutane yana iya sanjawa, saboda haka zanbaka dama kayi tunani mai kyau” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka bayan yaciro wasu maƙudan kuɗi a cikin aljihun rigarsa ya ɗauramawa Baffa akan cinyarsa..
Ware idanu Baffa yayi sakamakon ganin maƙudan kuɗin da Alhaji Ma’aruf yaɗaura masa akan cinyarsa, badai yana nufin duk nasa bane.
Murmushi irin na manya Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa “Kada kadamu bawai nabaka kuɗinnan bane,don ka bawa ɗana auren ƴarka ba, nabaka ne kawai saboda shi meyin alkhairi ako da yaushe baya rasawa”
Cikin sanyin jiki Baffa yayi masa godiya haɗe da buɗe murfin motar yafita, zuciyarsa cike da ɗunbin mamaki…
Baffa na fita daga motar Alhaji Ma’aruf yamawa driver’nsa umarni akan cewa su tafi, aikuwa ba ɓata lokaci drivern yatada mota..
Saida suka ɓacewa ganinsa kafun Baffa ya iya ɗauke idanunsa daga kansu, kuɗin dake hanunsa yashiga juyawa, “Lallai wannan mutumi yanada ihsani, amma kuma yazo da babbar magana, da ace yanada dama to da a yanzu yabawa ɗan Alhaji Ma’aruf ɗin auren Zahrah, to saidai kuma yanzu ya saduda, sakamakon wa’azi mai tsoratarwa dayaji akan cutar da maraya, da kuma irin azabar da za’amawa mai cutar da maraya, tundaga wannan lokacin yaƙudurta aransa cewa bazai sake cutar da Zahrah ba, yanzu ma dolensa zai bata zaɓi, domin ita zatayi zaman auren ba shiba…



