NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yanashiga gida Inna da takasa zaune takasa tsaye, ta ƙaraso wajensa da sauri tana me cewa “Lafiya naga ka jima, har nafara jin tsoro naɗauka irin mutanen nan ne masu garkuwa da mutane suka kamaka, domin na leƙa naga wasu fankama fankaman motoci a waje”

Harara Baffa ya wurgamata, haɗe da jan tsuka “Bazaki taɓa sanja halinki ba ko Salame, wato ke dai koda yaushe kai da kuma idanunki sunaga ƙofar gida, kullum cikin leƙe kike, wato dai har dare ma yanzu leƙe kikeyi, Allah ya kyauta” yafaɗi haka yana mai nufar hanyar ɗakinsa…

Fuska Inna ta ɓata haɗe da kafe aljihunsa da idanu, domin kuwa tuni idanunta sun ƙyallaro mata tudun da aljihunnasa yayi, ƙwafa tayi haɗe da rufa masa baya, koma mene sai
taje taganema idanunta, idan ma abuncine aci da’ita..

Sake gwalo idanu Inna tayi, ganin kuɗin da Baffa ya’aje akan gadonsa,   “Malam kace farar fita kayi, a shema baƙin arziki ne, nayi musu mummunar fahimta, ae irinsu muke fatan suta zuwa” washe da baki ta ƙare maganar…

“Akwai matsala Salame, amma jeki ƙiramin Zahrah” Baffa yafaɗa bayan yayimawa kansa mazauni, a bakin gadonsa.

“Yanzu kuwa” Inna tafaɗa tana me fita daga ɗakin..

Zahrah ce zaune akan gadonta, game take bugawa a cikin wayarta, da’alama dai game ɗin yayi mata daɗi, domin kuwa ita kaɗai sai murmushi take.

Inna ce tashigo cikin ɗakin haɗe sa shaida mata ƙiran da Baffa keyi mata,  haka nan taji gabanta yafaɗi. Tare suka fito da Inna, dukansu suka ɗunguma zuwa ɗakin Baffa’n…

Gyara zama Baffa yayi haɗe da maida kallonsa ga Zahrah, wacce ta duƙar da kanta ƙasa.

“Bayan Likita akwai wani wanda kikasan yanasonki, ko kuma kika basa dama ya turo magabatansa wajena?”  Baffa yatambayeta cike da kulawa.

“A’A Baffa bana mu’amala da kowa sai likita, bankuma bawa kowa izinin zuwa wajenka ba” tafaɗi haka cike da girmamawa, duk da kuwa cewa kanta ya ɗaure da jin tambayar da Baffa’n yayi mata…

Kai Baffa yajinjina haɗe da cewa “Ƙiran da akai min ɗazu wani ne yazo nemawa ɗansa aurenki, shine nayi tunanin ko kinsan da zuwansa”

Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, har batasan sanda ta ɗago da idanunta ta kalli Baffa ba.

Baffane yacigaba da cewa “Bansan ko su ɗin suwaye bane, amma ban ɓoyemusu komai ba, nasanar dasu cewa nabada aurenki ga wani, amma mahaifin yaron yace yabani lokaci nayi tunani,  saboda hakane ma naƙiraki domin ni bazan miki dole ba,  zanbaki dama ne ki zaɓi wanda kikeso”

Take idanun Zahrah suka kawo ƙwalla, sakamakon jin wani baƙon al’amari dayake shirin kunno kansa cikin rayuwarta.

“Kinyi shiru, ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba Zahrah, kema kina da ƴan ci, zan kuma baki ƴancin ki, sai dai abun da nakeson sani  shine wanene yaron nasa, saboda bai yiwuwa a haɗaki aure  da wanda  bamusani ba, amma idan ke kinsan sa shikenan ba damuwa”

“Bansan saba Baffa, kuma ma koda nasansa bazan aminta dashi ba, saboda idan nayi haka ban yi mawa Dr.Sadeeq adalci ba” Zahrah tafaɗi haka cikin sanyayewar murya…

“Adalci, kaji shirmen banza don Allah Malam, wani adalcine yarage miki, wanda yawuce ki kai kanki cikin arziki kicisa yanda yakamata,  saidai ko inkuma baƙin ciki kike mana”
Inna ta tsomo bakinta cikin maganar batare da angayyaceta ba…

“Tashi kije Zahrah, idan suka sake zuwa zan sanar dasu cewa hakan da sukeso bazai yi wuba” Baffa yafaɗa, yana mai wurgamawa Inna harara..

Cikin rashin ƙwarin jiki haɗe da ɗaurewar kai Zahrah tabar ɗakin..  Haushin Zahrah da Baffa ne yacika zuciyar Inna, amma ganin yanda Baffa yahaɗe fuska bai bata damar yin ƙorafi ba yasanya itama tafice daga ɗakin tana me ƙananan maganganunta wanda ita kaɗai tasan metake cewa..

Zama Zahrah tayi jigum haɗe da zurfafa tunanin ta,  ba’abun dake bata mamaki da ɗaure mata kai, kamar neman aurenta da Baffa yace anzo anyi,  “To waye zai zo neman aurenta batare da saninta ba? batare da ta kuma sanshiba, lallai koma waye baisan meyafaru da’ita ba, domin tasan daya sani, da baiyi gigin turo magabatansa nema masa aurenta ba” Haka dai tayita saƙawa da kuncewa har bacci ya ɗauketa……

Cike da tsananin mamaki Zaid yake kallon mahaifinsa, sakamakon ji da yayi mahaifin nasa nacewa “Wai anbada auren Zahrah’nsa ga wani”  ” Anya kuwa gidan su Zahrah Dad ɗinsa yaje? kodai yayi mistake ne yaje wani gidan amadadin nasu Zahrah?” duk wannan tambayar kansa ya mawa.

“Inaga zaifi kyautuwa kanemi wata My Son, domin kafasan nema cikin nema haramunne”  Alhaji Ma’aruf ya faɗa yana me kallon ɗan nasa.

“Inaga ba gidansu kaje ba Dad,
domin ni nasan Zahrah tawace, baza’a bawa wani ita ba bayanni” Zaid yafaɗi haka bayan yayi sipping holandia milk ɗin dake aje cikin  glass cup ɗin dake gabansa.

Kallon mamaki Alhaji Ma’aruf, yashiga yi mawa Zaid, sakamakon jin abun daya faɗa.
Baisan me yake shirin faruwa da ɗansa ba, amma tabbas ya hango wata irin soyayya acikin idanun Zaid ɗin me matuƙar zafi, wanda Zaid shikansa baisan da’ita ba…

“Akwai matan aure dayawa Zaid, zaifi kyau ka zaɓi wata, koda a cikin ƴan uwankane” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka cikin lallashi. 

Murmushi kawai Zaid yayi haɗe da kallon mahaifin nasa…

“Kai mahaifinane saboda haka bana iya ɓoye maka komai,  a gaskiya banjin zan iya zama da wata daban, idan ba Zahrah ba, zanyi komai da kaina kawai” yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye…  Da kallo kawai Alhaji Ma’aruf yabi sa dashi har ya fice daga cikin  falon nasa. Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa “wataƙila idan kuɗi na magani, to zasu maya Zaid, ta hanyar samo masa auren Zahrah”
(hmm bakomai ake nema a samu ba, bakuma komai kuɗi yake iya saya ba)

Kai kawo Zaid yashigayi a tsakiyar tankamemen aljannar duniyar falonsa, gaba ɗaƴa yarasa me yake masa daɗi, shin maganar da Dad ɗinsa ya faɗa masa cewa anbada Zahrah, gaskiya ne kokuwa Dad ɗinnasa ne yayi mistake wajen gano gidan su Zahrah,  dudduniya babu wani mahaluƙi daya isa yimasa shamaki da muradinsa,   lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyana kansa gareta,  baidamu da yanda zata ɗaukesa ba, shidai burinsa kawai shine ya mallaketa amatsayin matarsa,    lallai yanzune zai gudanar da babban takunsa, sannan kuma yazama dole yagano bayanshi wayake bibiyan Zahrah, har ake yunƙurin aura masa ita, dole yagano wannan, domin yayi imani cewa Zahrah tasa ce…


Fitowarsu daga lecture kenan, wayarta tayi ƙara alamar shigowar saƙo,, ko kaɗan batayi mamaki ba, domin zuwa yanzu tasaba da saƙonnin da’ake turo mata batakuma san waye yake mata hakan ba. 

Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta gama karanta saƙon, yau madai kalamaine masu tsayawa a zuciya, ɓoyayyen mutumin nata ƴarubuta mata, sai dai kuma duk sanda ya turo mata da saƙo, idan takaranta kalaman sukan tsaya mata arai suna kuma yawan yi mata yawo a ƙwaƙwalwarta,   koda sau ɗaya ne bata taɓa tunanin mayar masa da amsa ba, amma hakanan taji yau tanason tambayarsa ko shiɗin waye.

“Waye kai?” Abun da tarubuta tatura masa kenan.

Zaid dake kwance cikin wata luntsumemiyar kujera yana  sipping wine yaji wayarsa tayi ƙara alamar shigowar saƙo,   ɗaga wayartasa yayi yaduba, murmushinsa me kyau yayi bayan yagama karanta tambayar nata..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button