NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kinason ganina?”  shima yamayar mata da tambaya, tahanyar tura mata saƙo.

Zahrah na karanta saƙon tasoma typing kamar haka….”Mezai hana idan zaka bayyana kanka”  tana gama rubutawa tayi sending..

“Kishirya ranan friday 8:00 pm zankawomiki ziyara, ina fatan zakiji daɗin ganina, sannan zan taho miki da kyakkyawan surprise”  yana tabbatar da cewa saƙon ya isa zuwa wayarta, yayi switch off na wayarsa,   sake gyara  kwanciyansa  yayi ajikin kujeran, haɗe da lumshe idanunsa,  jiyake mararsa tana yi masa ciwo, kusan kwana uku kenan da yake fama da wannan ciwon maran,  hakan kuma yasamo asali ne da wata irin sha’awa da ta damesa, sai alokacinne ma yake tuna cewa yajima baiyi sex ba, lallai akwai abun da yake damunsa, Zaid ɗin da baya iya kwana ɗaya baiyi sex da mace ba, wai shine yanzu yake iya kwanaki batare da yayi sex ba,  shida mace ɗayama bata isan sa, amma sai gashi, yau ɗayan ma, yakasa nutsuwa yakusanceta, lallai yanzu kam yayarda da cewa akwai abun dake damun jiki da zuciyarsa….

Ɗan jim Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon nasa,  idan bata mantaba yau Tuesday kenan saura kwana biyu jumma’a tayi, lallai tanaso taga wanene wannan wanda yaɗau lokaci yan ɓata tunaninta,  ta wani ɓangare na zuciyarta kuwa, ji takeyi tamkar akwai wani gagarumin abu dazai faru da’ita, yayinda idan ta tuna aurenta da Dr.Sadeeq  saitaji ta zama wani iri da’ita, bakuma aurenta da Dr. ɗinne bataso ba, a’a kawai dai tanaji ajikinta kamar basu dace da juna ba ita dashi…

Dariya sosai Salima tashiga yi, sakamakon labarin da ƙawarta kuma aminiyarta Laura tabata yanzun.     Wani irin daɗi taji haɗe da sanyi acikin zuciyarta,  gaba ɗaya labarin Zahrah Laura ta kwashe ta sanar da Salima, wanda Laura ta samo asalin labarin Zahrah ne daga bakin wata Asma da take unguwarsu Zahrah’n kuma har school ɗinsu ɗayama da Zahrah..

“Dama akan sauran wani Doctor yake wulaƙantani hadda jamin aji, hmm lallai kuwa bazanyi kishi da mai aji bama ballentana marar aji” Salima ta faɗi haka cike da kunfar baki…

“Ae magana taƙare Salima, kamar yanda na faɗamiki, tashi kawai zamuyi muje hargidansu, muci mata mutunci mukuma gargaɗeta da tafita hanyar Doctor Sadeeq” Laura tafaɗi haka cike da son zuga Salima.

“Gaskiya ne nima ina bayan maganarki Laura” wata wacce take zaune gefen Laura ta faɗi haka, tana me taɓe baki..

Kallonta Salima tayi haɗe da cewa “Shiyasa nake sonki ƙawata, bakida wasa, wajen sawa ayi rashin mutumci, idan kinshirya muje gidan nasu yanzu, domin akan Doctor sai inda ƙarfina ya ƙare” Salima tafaɗi haka tana maitashi daga zaunen da take.
Motar Salima suka shiga su duka ukun yayinda Laura ke tuƙasu, domin itace jagoran tafiyan kasancewa har gidansu Zahrah ta sani, saboda tasa Asma ta nuna mata….

Zahrah ce zaune a tsakar gida bisa kan tabarma, kwanon abincine aje a gabanta, gaba ɗaya ta kasa tsayawa taci abincin yanda yakamata domin kuwa yau Thursday gobe ne kuma haɗuwarsu da mutumin dayake ɓoye mata kansa, duka nutsuwarta baya gareta, hakanan takejin babu alkhairi a haɗuwarta da mutumin…

Wani irin bangaja da aka mawa ƙofar gidansu shiyasanyata ɗago kanta takai kallonta zuwaga ƙofar gidan nasu..

Wasu tsalan tsalan ƴan mata su uku ta gani, tsaye ko wacce ta kafa makeken glass akan idonta, yayinda suke taunar cingam cike da iyawa haɗi da salo……

(Manage please???? rasuwa akai mana shiyasa banyi posting da wuri ba)

21/December/2019

Follow me on Whatsapp and Wattpad

Wattpad user name fatymasardauna

10:4 pm
????????????????????????????????????????

            SHU’UMIN NAMIJI !!

  
      Written By
Phatymasardauna
(shalelen kainuwa)

Dedicated To My Brother KHABIER

             WATTPAD
       @fatymasardauna

(Wannan page ɗin gaba ɗayansa kyautane a gareku Members na BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION haƙiƙa kuɗin na daban ne, sannan kuma kuna da ƙoƙari sosai da sosai wajen sanbaɗomana comment, muna godia Allah yabar ƙauna)

Editing is not allowed????

      CHAPTER 64 to 65

Baki da hanci Zahrah ta sake tana kallon waƴan nan ƴan matan  da suke tsaye suna me yimawa cikin gidannasu kallon wulaƙanci haɗe da ƙyama..

Cire glass ɗin dake idanunta Salima tayi, haɗe da watsamawa Zahrah wani irin kallo mai ɗauke da mugun tsana,    cike da ƙyama ta furzar da yawu, haɗe da kallon Laura  “Itace wan nan?” Salima ta tambaya tana me nuna Zahrah da hanunta cike da taƙama.

“Eh itace ƴar matsiyata” Laura ta faɗa tana yanatsina fuska.

“Lafiya kuwa bayin Allah? su waye ku? Zahrah ko kinsan sune?” Inna da fitowarta a ɗaki kenan ta tambaya, Tana me mamakin ganinsu haɗi da aljabi.

“Ba alkhairi bane ya kawomu, saboda baku kai matsayin da zamuzo muku da alkhairi ba,  sunana Salima, nazone domin najawa wannan matsiyaciya kuma karuwar ƴar taku kunne, koda wasa Doctor Sadeeq basa’an  aurenta bane, saboda yawuce ajin macen da taraba mutuncinta a titi”   takawa taci gaba da yi  cikin isa harta ƙarasa gaban Zahrah, da ta kasa ko motsi… “Banzo danna cutar dake ba, amma tabbas idan kika sake nakuma dawowa cikin gidan nan  to zanyi miki babban illa,  rabuwa dashi zai fi miki, idan kuma kika ƙi, hmmmm zakisan cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane,  bake kaɗaiba, hatta tsohon da yake riƙe dake sai ya ɗanɗana”  Salima tana kai ƙarshen zancen nata tamaida glass ɗin ta dake riƙe a hanunta, haɗe da kallon su Laura “Muje” tace dasu, babu musu kuwa suka rufa mata baya, suna tafiya suna kareraya…

Tamkar statue haka Zahrah tayi ƙasaƙe tana kallonsu, harsuka fice daga cikin gidan.

Sallallami Inna tashiga yi haɗe da tafa hannuwanta duka biyu,  “Lallai kuwa wa ƴan nan ƴan iska masu jajayen fuskar suncika marassa ta’ido, rashin kunya har cikin gida” Inna tafaɗi haka cike da mamaki.

Kai kawai Zahrah ta girgiza, haɗe da jawo kwanon abincinta ta ci gaba da ci,  batare da ta tankawa Inna da take ta ɓaɓatu ba,,  sai dai kuma sosai maganganun Salima suka daki zuciyarta,  har wani ɗaci takeji a cikin maƙoshinta.. Tura abincin takeyi amma jinsa take tamkar maɗacin dayafi kowanne ɗaci,  har wani zafi takeji a ƙirjinta. Tana gama cin abincin, ta kora da ruwa, haɗe da tashi kai tsaye tanufi ɗakinta.

“Karuwa” sunan da Salima taƙirata dashi yafiye mata komai ciwo, tunda take a duniya ba’a taɓa ƙiranta da sunan karuwa ba, sai a yau ɗin, wasu irin zafafan hawayene taji sunshiga gangarowa daga cikin idanunta,  durƙushewa tayi a ƙasa  haɗe da soma rusa kuka,  filla filla kalaman da Salima ta faɗa mata suke dawowa cikin kanta, koda wasa bata taɓa tunanin za’afaɗi kalma na ɓatanci masu muni irin haka akan ta ba.

“Kacuceni Zaid, Kacuceni, me yasa ka aikata haka agareni, shin koda sau ɗaya ne bakayi tunanin yanda rayuwata zata kasance ba,   bazan taɓa yafe maka ba Zaid har kuwa nakoma ga mahaliccina” cikin kuka ta ƙare maganar, domin kuwa sai yau tasake tabbatar da cewa Zaid ya cuceta,  takuma ƙara jin matsanancin zafi dakuma  ciwo akan fyaɗen da Zaid yayi mata.. Abu kamar wasa haka Zahrah tayita kuka tamkar ranta zai fita, sai gashi cikin mintuna ƙalilan ciwon kai yakawomata ziyara, wanda har sai da yakaita ga kwanciya..  Ƙiran Dr.Sadeeq ne yashigo cikin wayarta amma tanaji tana gani takasa picking call ɗin har wayan ta tsinke, taƙi ɗaga wayan ne kuma don bataso yafahimci cewa tana cikin damuwa.   Wani ƙiran nasa ne kuma yasake shigowa, still dai har wayan ta katse, Zahrah bata ɗauka ba, domin har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba..   Ƙira na uku ne yakuma shigowa cikin wayarta ta,  ƙoƙari tayi wajen ɓoye damuwarta haɗe da ɗaukan wayar ta kara akan kunnenta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button