NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yasauƙe sakamakon ji dayayi ta ɗaga wayan.

“Wani irin laifi me girma na’aikata haka da aka ƙi amasa wayata?” Dr.Sadeeq yatambaya.

Cikin sanyin murya Zahrah tace dashi “Bana kusa ne shiyasa”

Wata ajiyar zuciya yakuma sauƙewa  cike da kulawa yace “Naji muryarki ta sauya ina fata dai kina halin lafiya?” cikin kulawa ya ƙare maganar.

“Lafiya ƙalau” tabasa amasa a taƙaice.

“Yakamata nazo muyi magana domin inaso nasan irin shirye shiryen da zakiyi, idan lokacin auren mu ya gabato, kinsan yakamata ace anfarayin komai akan lokaci, yanzu ina tuƙi ne idan na tsaya zanƙiraki”

“To” kawai ta’iya cewa dashi, har ya katse ƙiran.

Tanacire wayar akan kunnenta saƙo yashigo cikin wayar.

“Nakan ji wani iri a jikina idan har kina cikin wani irin yanayi, ki daina sa kanki a damuwa, saboda zaki iya cutar da zuciyarki, nikuma bazan so haka ba, saboda kece muradina”  abun da saƙon yaƙunsa kenan..

Tsuka Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon, haɗe da kashe wayarta ta baki ɗaya,  jira take kawai Allah yakaita gobe taga wayane yake raina mata hankali haka, daga goben kuma zata takamawa komaye birki, domin kuwa ko ma wayene bazai taɓa burgeta ba, zuwa yanzu babu wani ɗa Namiji da zaiyi tasiri acikin zuciyarta.

Zaid ne kwance akan makeken gadonsa wanda yasha bedsheet na alfarma,    kwanciyar nan yayi irin wanda ba kyau, wato rufda ciki,    wata doguwar takarda ne riƙe a hanunsa, wanda take ƙunshe da duk wani abu daya ƙunshi Dr.Sadeeq daga kan sunansa aikinsa har zuwa mazauninsa, dakuma a halinsa, kyakkyawan bincike Zaid yasa a kayi masa akan Doctor ɗin,  saboda a cewarsa babu wanda ya’isa ya shiga huruminsa, saboda Zahrah tasace shi kaɗai, saboda haka dole ne zaitakawa Dr.Sadeeq  birki..

Murmushine ya bayyana akan fuskarsa bayan yasanya duka hanunsa biyu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa,, shi kansa yaƙosa gobe tayi yaga Zahrah’n sa, duk da kuwa cewa yana biye da duk wani shiga da ficenta, amma  kwata kwata baya gajiyawa da ganinta, sam baisan meke damunsa ba,  zuwa yanzu yafara kokonto dakuma tunani anya ba wannan abun da yakeji shi ake ƙira soyayya ba kuwa? Idan kuwa harda gaske abun nan da yakeji a game da Zahrah shi ake ƙira soyayya, to tabbas yakamu da so matsananci, sai dai kuma bayida ikon tabbatarwa kansa cewa so yake, hakanne ma ya hanasa gane wanni hali yake ciki,  ko da wasa bai taɓa tunanin cewa Zahrah zata ƙisa ba, saboda haka ako da yaushe cikin ƙarawa kansa ƙwarin guiwa yake….

FRIDAY

Rana bata ƙarya,  ranan yau ta kasance Friday kuma yaune Ɓoyayyen mutumin ta yayi mata alƙawarin baiyana kansa gareta,  sai dai kuma baƙon al’amarin da ta wayi gari dashi yasoma tsinkar mata da zuciya, haɗe da sanyayewar jiki, domin kuwa yau ta tashi tana me jin faɗuwar gaba, haɗe da bugawan zuciya da akai akai, hakan kuwa baƙaramin tsoro yajefata ciki ba, saboda bata taɓa mantawa irin wannan faɗuwar gaban ta dinga ji a ranan da mummunar ƙaddaranta zata rusketa,, sai dai kuma babu abun da yagagari Allah, don haka ta shiga yin addu’o’i acikin zuciyarta, saboda ta samu salama..

Ƙarfe Uku na yammaci de de suka fito a lecture’n ƙarshe da suke dashi na wannan ranan,  gaba ɗaya sukuku haka ta wuni a cikin school ɗin,  Husnah tayi tambayan har ta gaji, akan ta faɗa mata meke damunta amma tace ba komai, to me zatace mata? ita kanta batasan meyake damunta ba.

Su Husnah ne suka kawota har ƙofar gida, saboda yanzu Dr.Sadeeq aiki yamasa yawa sosai, ga aikin office ga kuma hidiman hada hadan biki, gaba ɗaya baya samun isashshen lokaci, hakan yasa idan sun tashi a school take shiga motar da ake zuwa ɗaukar Husnah su sauƙeta a gida…

Tun azaure take ta kwaɗa sallama harta shigo cikin gidan nasu, amma babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta tabbatar cewa bakowa acikin gidan,  har ɗaki ta leƙa amma babu Inna babu alamarta, saboda haka kai tsaye ta wuce ɗakinta.   Zama tayi jigum tamkar wacce aka mawa mutuwa, fargaban haɗuwa da ɓoyayyen mutumin nan take, hakanan takeji dama bata nemi ganinsa ba,  saboda gaba ɗaya jikinta yagaya mata babu alkhairi a haɗuwarsu, sai dai kuma babu yanda ta’iya tunda ya tabbatar mata da cewa yau ɗin zaizo, ganin da tayi tunani na shirin damunta,  yasa ta ɗauko alƙur’ani mai girma tasoma karantawa,  saboda hakan yana sauƙar da salama sosai acikin zuciyar wanda yake cikin ƙunci da fargaba….

Tana kai sujjadar ƙarshe ta sallan isha tafashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, hakan yafarune kuma saboda ta kasa control ɗin kanta, sosai faɗuwar gaban da takeji yake tsanan ta aduk bayan wasu mintuna.. Cikin kuka tasamu ta sallame sallan isha ɗin,  bayan ta gama faɗawa ALLAH buƙatunta, tana me kuma neman sauƙi a garesa, idanunta da suke cike da hawaye ta ɗaga haɗe da  maida kallon ta ga yagalgalellen agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe bakwai da arba’in, saura mintunan da basufi Ashirin ba yaƙaraso kenan, domin ƙarfe takwas yace mata zai zo…

Bugawan da agogo yayi 8:00 pm, yayi dai dai da bugawar zuciyar Zahrah, har saida taji cikinta yabada wani sauti. Kallon agogo takumayi akaro na barkatai,  bazata iya tantance me takeji ajikinta ba, tsoro ne kokuma ruɗewa ne, takasa banbancewa.

Idanun Zahrah nakan agogo har ƙarfe takwas da minti biyar, ko ƙyafta idanun ta batayi ba, azahiri agogon take kallo, amma a baɗini ba da idanunta take kallo ba, da ƙwaƙwalwarta take gani,  kallon agogon kawai take amma bata fahimta saboda tunaninta ba a kansa yake ba.

Saƙone yashigo cikin wayarta, wanda yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta.

“Inaƙofar gidan ku” bakinta na rawa haka takaranta saƙon saikace wanda aka turomata saƙon ranar mutuwarta.

Takai kusan minti huɗu tana sake maimaita karanta saƙon, sai kace wanda aka yo saƙon da wani harshe bana hausa ba, idan kaga yanda take karanta saƙon zakai tunanin bata iya hausa bane, kokuma bata  gane abun da saƙon yake nufi ba,  bakomai yasa hakan ba kuma face tsoro da taji ya daki zuciyar ta, yayinda gabanta yatsananta faɗuwa, tabbas wannan faɗuwar gaban bana haka kawai bane, lallai dole akwai abun da zai faru da ita,  amma kuma yazama dole taje taga wanda yake turomata saƙonni, hanunta na rawa haka ta ɗau hijib ɗinta ta sanya,  da ƙyar take iya jan ƙafanta ta fita daga ɗakin…
Inna ta iske zaune a tsakar gida, tana jin radio,    “Inada baƙo a waje Inna” Zahrah tafaɗa cikin wata irin murya me rauni. Yanayin yanda Inna taji muryan Zahrah yasanya ta ɗago da kanta ta kalle ta,     “Lafiyanki kuwa, meke damunki?” Inna tatambaya cike da mamakin yanda taga jikin Zahrah  a sanyaye.

“Babu komai Inna” Zahrah tafaɗi haka tana me nufar hanyar ƙofar fita daga gidan..

Kasancewar akwai wadataccen haske a ƙofar gidan nasu na ƙoyayen wuta wanda maƙotansu suka kukkuna hakan yasa wajen baida duhu, zaka iya hango duk wanda ke tsaye dakuma wanda ke tsugunne, kai harma wanda ke kwance zaka iya ganinsa. 

Bugun zuciyarta ne yaƙaru yayinda ƙafofinta suka soma yi mata nauyi, wani mutumi tagani tsaye ajikin wata mota da ta amsa sunanta mota, sai dai kuma yajuya baya, saboda haka bayansa kawai take iya hangowa, sanye yake da wandon jeans black dakuma black ɗin riga sannan kuma akwai hula irin fosin kaf ɗin nan akansa.  A hankali take taka ƙafafunta dasuka mata nauyi tanufi inda yake tsaye,  yayinda ta sanya hanunta ta cikin hijab ɗinta ta dafe ƙirjinta da takejinsa kamar zai daka tsalle yafito waje..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button