NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Abu na farko daya fara hargitsa mata ƙwakwalwa bayan ta isa gareshi shine fitinannen ƙamshin turarensa wanda har gaban abada bazata taɓa manta wan nan ƙamshin ba,   wani irin killer smile Zaid yayi bayan yatabbatar da cewa ta karaso gab dashi,  fuskarsa ɗauke da murmushi ya juyo zuwa gareta, haɗe da sanya hanunsa ya cire hular dake kansa, take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, wacce take ɗauke da murmushi.

Jikinta ne yaɗauki rawa yayinda idanunta suka ƙara buɗewa take numfashinta yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, zuciyarta tashiga duka, ƙafafunta suka ƙage waje ɗaya, yayinda hawaye suka dinga fitowa daga idanunta tamkar anyi ambaliyan su.
Kallon yanda jikinta yake rawa Zaid yayi haɗe da dawo da kallonsa kan fuskarta jefa idanunsa  yayi cikin nata.    “ZAHRAH!” yaƙira sunanta da wata irin murya me sanyi,  sakamakon ganin da yayi  kamar cewa bata cikin hayyacinta…

“ZAHRAH” yasake ƙiran sunanta, de de lokacin ne kuma numfashin ta yashiga gudu yana neman ƙwace mata, aikuwa kasa fusgo numfashin nata tayi, lokaci ɗaya numfashinta yayi nasaran fita daga jikinta,  take ta yanki jiki tafaɗi warwas a ƙasa, cikin mugun tashin hankali Zaid yayi kanta, haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya ɗagota zuwa jikinsa,   sunanta yashiga ƙira cikin tashin hankali dakuma ruɗewa,  a matuƙar firgice ya sanyata acikin motarsa haɗe da shiga cikin motar da wani irin gudun gaske Zaid yafigi motar ya cillata kan titi…  Gaba ɗaya ya ruɗe wani irin gudu yake shararawa baburuwansa da wanda ke gabansa ko bayansa, gaba ɗaya ya ruɗe sunan Zahrah kawai yake ambata,  Allah yasa ba zuciyarta ta haɗiya ba..

Matsanancin gudun da Zaid yakeyi har ya wuce hankali,  da wani irin gudu yashigo cikin asibitin yayin da ya ɗauko Zahrah caɗak a hanunsa tamkar wata ƴar tsana, haka yashigo da’ita cikin asibitin, ganin haka yasa Doctors sukayo kansa da sauri,  hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙa ta ga doctors sukayi emergency da’ita kai tsaye.. Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bawa Zahrah domin kuwa bako maine ya haifar mata da ɗaukewar numfashin ba, face razana dakuma tsananin firgita haɗi da tsoro da suka rusketa alokaci guda, sannan yanayin yanda zuciyarta ke bugawa, yawuce mizani, idan har zuciyar tata tacigaba da bugawa da sauri sauri haka, tofa lalllai rayuwar Zahrah tana cikin haɗari…

(Niko nace idan Zaid yakashe mana Zahrah zamuci …. ko  fans????)

Iya ruɗewa Zaid ya ruɗe yakasa koda zamane, damuwarsa ɗaya shine Doctors ɗin da suke kan Zahrah, su sanar dashi meke faruwa, lallai idan har Zahrah tasamu wani matsala, to bazai taɓa yafewa kansa ba, sannan kuma babu uban da ya’isa yazauna lafiya, matuƙar likitocin nan suka kasa shawo kan matsalan Zahrah..

Kusan minti talatin likitocin nan sukayi suna ƙoƙarin shawo kan numfashin Zahrah, cikin ikon Allah kuwa sun samu komai yayi dai dai sai dai dole tana buƙatar hutu kodan zuciyarta ta samu salama…

Suna fitowa Zaid yayi kansu, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu.

Kallonsa ɗaya daga cikin manyan  likitocin dasuke kan Zahrah yayi haɗe da dafa kafaɗunsa,  “Ka kwantar da hankalinka, komai yayi dai dai, yanzu biyoni office ɗina”

Ba musu balle girman kai Zaid ya bi bayan liikitan.

Kasa zama akan kujeran da Dr ɗin yabasa yayi,  babban damuwarsa shine yasan wani hali Zahrah take ciki.

“Nace ka kwantar da hankalinka, kazauna saimuyi magana ko” likitan yafaɗa yana me nuna masa kujera..

“Kaga Doctor bazamane yadameni ba, babban damuwana  shine nasan wani hali take ciki” Zaid yafaɗi haka cikin damuwa..

“Zan faɗama ko wani hali take ciki, amma dole sai ka zauna”

Badon Zaid yasoba haka yazauna akan kujera haɗe da sanya duka hanunsa ya dafe kansa.

“Bawani babban abubane yake damunta, akwai abun da yafirgita ta ne, kuma dama anasamun irin haka, sau da dama firgici da tsoro, yakansa mutum yasamu ɗaukewar numfashi naɗan wasu daƙiƙu, amma idan tadawo hayyacinta komai zaidawo dai dai, sai dai kuma tana buƙatar hutu sosai, saboda haka bayau zaku samu sallama ba, dole sai kunjira zuwa gobe da safe, saboda yanzu haka akwai alluran damuka mata kuma suna sa bacci sosai” 

Ajiyar zuciya me ƙarfi Zaid ya sauƙe, saboda jin bayanan Doctor da yayi, sun sauƙar masa da nutsuwa    “Amma dole sai anan zamu kwana? me zai hana kabani ita mutafi gida, idan yaso saitayi baccinta acan” Zaid yafaɗi haka fuskarsa ɗauke da damuwa.

Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa “Hakan bazai samu ba, saboda zata iya farkawa da kowani lokaci, bamu kuma san a wani hali zata tsinci kanta ba, bayan ta farka, saboda haka zamanku anan ɗin zaifi amfani” Doctor yafaɗi haka cike dason gamsar da Zaid.

Kai kawai Zaid yajinjina haɗe da kallon Doctor  “Zan’iya ganinta kuwa? sannan kuma inaso akaita ɗaki na musamman konawane kuɗin ɗakin zan biya”

“Wannan ba’abun damuwa bane, zamu kaita ɗaki na musamman sannan kuma zaka iya ganinta,  bana ƙira nurse sai a sanja mata ɗaki daganan saikaje ka ganta ko” Dr yafaɗi haka bayan yakara waya akan kunnensa.  Cikin mintuna ƙalilan aka sanjawa Zahrah ɗaki inda aka kaita ɗaki na musamman. 

Zaid ne tsaye akanta yana me ƙare mata kallo, karo na farko kenan daya farajin wani irin matsanancin tausayin ta acikin zuciyarsa, haɗe da wani shauƙi mai fisgar zuciya.  A hankali yaƙaraso dab da gadon nataz haɗe da ranƙwafo da kansa dakuma ƙirjinsa zuwa gaf da’ita, lumshe idanunsa yayi haɗi da kai bakinsa gefen kumatunta ya yi mata kiss, haɗe da sa hanu yashafi gefen fuskarta,  “I’m sorry Zahrah!” yafaɗi haka acikin maƙoshinsa. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya soma bawa wata mace haƙuri..  Zama yayi a  bakin gadon, haɗe da kama hanunta na dama yasanya acikin nasa hanun, a hankali yake murza hanunta haɗe da lumshe idanunsa.

Abu kamar wasa hankalin Inna ne yasoma tashi ganin Zahrah ta kwashe sama da awa ɗaya, a waje batare da ta shigo gida ba, gashi ta leƙa waje bataga ko da me kamannin Zahrah bane, kasa zama inna tayi gaba ɗaya hankalinta a tashe yake,  Baffa ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama,  ko amsa sallaman nasa Inna batayi ba tayo kansa tana cewa “Yau wa Malam gwamma da ka dawo, ko ka haɗu da Zahrah a waje kuwa?”

“Zahrah kuma, ina Zahrah’n take?” Baffa yatambaya cike da mamaki.

Nan Inna tashaida masa cewa tunɗazu tafita bata dawo ba,bayan tasanar mata cewa wani ne yaƙira ta a waje.

Take hankalin  Baffa yatashi, domin kuwa Zahrah bata taɓa irin haka ba,  har maƙota ya aika ko taje amma aka ce masa bata zoba, take Baffa da Inna suka zuba tagumi, sun marasa ta ina zasu fara,  Inna cema takawo shawara akan cewa aƙira Doctor Sadeeq koshine yazo ya ɗauketa, aikuwa Baffa yayi na’am take  yadannawa number’n Dr.Sadeeq ƙira, bugu biyu Dr.Sadeeq yaɗaga wayan,, shima bakaɗan ba hankalinsa yatashi jin dayayi cewa wai su Baffa basuga Zahrah ba, ae take yashiga motarsa yataho gidansu Zahrah’n duk da cewa dare yayi…

Kallon agogon hanunsa Zaid yayi a karo na barkatai, ƙarfe 10 na dare kenan,  ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na uku, haɗe da furzar da iska a bakinsa,  kallonsa yakuma mayarwa ga Zahrah, wacce take ta sharan bacci,  hakanan yatsinci kansa da sakin murmushi mai sauti,  komai na Zahrah me kyaune, tafiyin kyau ma idan tana bacci.
Zama yayi akan wata kujera dake kusa da gadon haɗe da jingina bayansa da jikin bango, lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa sai yanzu ƴake tunanin ya makomarsa zai kasance idan Zahrah tafarfaɗo, domin kuwa ya hango muguwar tsanarsa acikin idanunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button