NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

23/December/2019

Follow me on Whatsapp and Wattpad

Wattpad user name fatymasardauna
????????????????????????????????????????

            SHU’UMIN NAMIJI!!

        Written By
  Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

          WATTPAD
    @fatymasardauna

Editing is not allowed????

   CHAPTER 66 to 67

Lokaci ɗaya hankalin Dr.Sadeeq yayi wani irin mummunan tashi, take ƙwaƙwalwar kansa tashiga charge, a iya tsawon sanin da ya yi mawa Zahrah, ita ba mace bace meson fitar dare, balle har tayi nisa da gida, sai dai kuma abun mamaki gashi yau annemeta an rasa, bayan ko ɗazu  suna tare a waya shida ita, baikuma ji wani sauyi a tattare da’ita ba, sai dai kawai muryarta da yaji cikin sanyi.  “To ina Zahrah taje?”
Yayi mawa kansa tambayar da bayi da amsa.. “Kodai Zahrah tayi hakane don batason aurena da’ita?” yakuma tambayar kansa, sai da zuciyarsa ta buga, shi kansa yatambayi kansa abun daya faɗar masa da gaba,  kai amma Zahrah bazatayi haka ba, saboda ita da kanta ta tabbatar masa cewa ta amince da auren sa, saboda haka bazata bar gida saboda batason auren sa ba..
Kallonsa yamaida ga Inna wacce tayi tsuru tsuru da ido tamkar wata munafuka…”Da tazo fita bakiga wani alaman damuwa ko tashin hankali akan fuskarta ba?” Dr yatambaya cike da kulawa.

“Ƙwarai kuwa da damuwa tafita, saboda kwana biyun nan gaba ɗaya   da damuwa take wuni sakamakon waƴansu tsinannun ƴan mata da suka zo, acewar ɗaya daga cikin su wai ita zaka aura Samira take ko Salma oho, haka nan suka zo hargida suka zagemu kaf, tamkar ma zasu mana luguden duka, to tundaga tafiyarsu dai take fama da ƙuncin rai har kawo yau, Allah dai yasa ma basune sukai mata wani abun ba” Inna tafaɗi haka cike da jimami..

Cike da mamaki Dr.Sadeeq yace “What Salima tazo har gidan nan taci muku mutunci?”

“Ƙwarai kuwa ashe dagaske kasanta, tabbas haka tace sunanta wai Salima, ita da waƴansu masu ƙoƙaƙƙun fuska, kamar an gasa nama”

Hanu Dr.Sadeeq yasanya yadafe kansa, lallai idan de har Salima bata ji kunyar zuwa ta zagar masa abar sonsa ba, to tabbas shima bazaiji kunyar zuwa har gidansu  yaci mata mutumci ba,  Uwa mahaifiyarsa kaɗai ze iya ɗagawa ƙafa akan Zahrah, amma duk wacce tace zata ci mutumcin Zahrah tofa shima zaici nata mutuncin, lallai yakamata ne yafara nemo inda Zahrah take  kafun yasan matakin da zai ɗauka akan Salima. Sake dialing number’n Zahrah yayi amma still ce masa  ake wai wayar akashe take, tun ɗazu yake ƙiran wayar anacemasa akashe wayarta ta take.. Tunanin ƙiran abokinsa inspector Adam ne ya faɗo masa, saboda yalura lamarin dole sai anshigo da hukuma ciki, tunkan suyi sake lokaci ya ƙure musu. Nan yashiga dialing Number’n inspector Adam amma har wayar ta katse bai ɗauka ba, sake ƙira yayi amma still bai ɗauki wayar ba, tsuka Dr.Sadeeq yayi haɗe da maida wayarsa cikin aljihunsa….

Asibiti

Sai yanzu tunanin halin da iyayen Zahrah zasu shiga yafaɗo masa arai,  tabbas yakamata ne yasanar dasu halin da ake ciki,  wayarsa yaɗauka haɗe da soma rubuta saƙo, domin bayason wayar da zaiyi yatashi Zahrah a baccin da takeyi, saboda haka gwamma yatura saƙo,a ganinsa hakan zaifi… wata number yaturawa saƙon, batare da yajira amsar da wanda yaturawa saƙon zai basa ba, ya maida wayarsa cikin  aljihu…..

Dr.Sadeq ne yadubi Baffa dake a halin damuwa. “Banaje nasanarmawa ƴan sanda, akwai abokina inspector, inaga kawai gwamma naje gidansa na sanar dashi abunda ke faruwa, ina ga zaifi akan tsayuwan damuke” yafaɗi maganar yana me duba  agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, ƙarfe sha ɗaya na dare kenan agogon sa yanuna masa..

Sallaman da sukaji ana kwaɗawa a ƙofar gidan ne yaɗauki hankalinsu, ae ba shiri Baffa da Dr. Sadeeq suka ɗunguma zuwa ƙofar gidan, Inna ma ba’a barta a baya ba ta rufa musu baya.

Wani mutumi me shigar cute baƙaƙe suka gani tsaye a bakin ƙofar gidan, yayinda yarufe idanunsa da tabarau, da ganinsa dai zaka gane irin body guard ɗin nan ne.

“Waye kai?” Dr.Sadeeq yatambaya yana me ƙaremasa kallo.

“Saƙo aka bani  nasanar daku cewa Zahrah bata da lafiya, yanzu haka tana asibiti..” baikai ga idar da zancen nasa ba, Dr.Sadeeq yace “Meyasameta sannan kuma a wani asibiti take?” duka tambayar yayisune alokaci ɗaya, kuma
cikin ruɗewa..

“Zaku iya biyoni muje” Body guard ɗin nan yafaɗa yana me nufar wajen da motar da yazo da ita ke fake.
Kallon su Baffa Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa su shigo motarsa subi bayan body guard ɗin, hakan kuwa akayi  motar Dr.suka shiga yayinda Dr.yashiga bin bayan motar body guard ɗin. Gaba ɗaya ba acikin nutsuwarsa yake driving ɗin ba. Fargabane cike a zuciyarsa, bayi da wani buri da yawuce yaga Zahrah, yakuma ji meke damunta, har aka kawota asibiti batare da sanin su Baffa ba..
Suna shiga cikin asbitin wannan body guard ɗin  ya kalli  Dr.Sadeeq haɗe da cewa ya biyosa ciki, su Inna kuwa su jirasa,  da su Inna sunso ƙi, amma sai Dr. Sadeeq yace su yarda su jirasu anan ɗin, badon su Inna sun so ba, suka tsaya daga waje… Suna shiga cikin wani corridor  guard ɗin yaciro wayarsa, haɗe da karawa akan kunnensa.

“Oga na faɗa musu sunma biyoni, yanzu haka munatare da wani inazaton ɗan uwanta ne, iyayenta kuma suna waje” Abunda Body guard ɗin yafaɗa kenan cike da girmamawa.

Tsuka Zaid yayi sakamakon jin abunda guard ɗin nasa ya ce, shirmen banza, cewa yayi yafaɗamusu bawai ya taho masa dasu ba, to yanzu dayakawosu ina zai sasu, wata tsukan yakuma yi, haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin bayan ya sake rufe Zahrah da bargo..

Cakume kwalan guard ɗin nan Dr.Sadeeq yayi cike da ɓacin rai yace “Bamason iskancin banza kace tana asibiti bata da lafiya, gashi munzo kuma kana ƙoƙarin raina mana hankali, wlh idan wani abu yasameta saina ɗaureka” Cikin ɓacin rai Dr.Sadeeq yafaɗi maganan domin kuwa yulura guard ɗin nema yake ya raina masa hankali….

“Idan har ka’iya ɗauresa, to tabbas zan iya yarda na ƙiraka da suna jarumi !!”  muryar Zaid takaraɗe wajen, wanda yake ƙarasowa garesu cikin takunsa na isa..

Kallon Kallo aka shigayi tsakanin Zaid dakuma Dr.Sadeeq, wanda kowannensu da irin manufar tasa kallon.  

Sama da 5 minute Zaid da Dr.Sadeeq suka ɗauka suna kallon juna,  Zaid nayimawa Dr.Sadeeq kallon tsana, yayinda Dr.Sadeeq kuma kemawa Zaid kallon tuhuma, haɗe da son sanin koshi waye…

Kallon guard ɗin nan Zaid yayi haɗe da taɓe bakinsa cike da isa yanuna Dr.Sadeeq haɗi da cewa  “Wan nan kuma waye?” yayi tambayar cike da rainin hankali, yana me ɗage kai sama bayan yajefawa Dr.Sadeeq wani irin kallo..

“Hmm ba buƙatar kasan koni ɗin waye, kai de zaifi kyau kasanardani  ko kai waye, amma shishshigi baikamace kaba, saboda bakayi kama da me kula da lafiya ba, kafi kama da masu  shiga inda ba’a buƙatarsu” Dr.Sadeeq yafaɗi haka shima yana me ɗauke kansa daga kan Zaid.

Murmushi Zaid yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq daga sama har ƙasa. Kansa kawai ya girgiza “Lallai bana buƙatar kowa, kasan yanda zakayi dasu” Zaid yafaɗi haka ga Guard ɗinsa,  haɗe da juyawa yanufi ɗakin da aka kwantar da Zahrah,  lokacinsa bana me aikin duba lafiya bane, lokacinsa muhimmine kuma sai me mahimmanci yake bawa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button