NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Hasala Dr.Sadeeq yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarsa tana masa zafi, yana da sauƙi amma watarana abu kaɗan ke ɓata masa rai, a zuciye ya juya yafice daga cikin asibitin.. Su Inna dake tsaye a harabar asibitin suna ganinsa sukayo kansa da sauri suna tambayarsa ko Zahrah tana lafiya?

Kasa amsa musu yayi saima cewa da yayi, su shiga mota su yasauƙesu a gida… Bayanda suka iya haka suka shiga cikin motar jiki a sanyaye, saboda sunga gaba ɗaya  fuskar Dr.Sadeeq ɗin ɓacin raine shumfuɗe akanta, kenan akwai abun dake faruwa.. Da wani irin gudu yaja motar suka fice daga haraban asibitin…

Gyara zama Baffa yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq wanda da’alama tunaninsa baya jikinsa.

“Meyake faruwa ne Likita? kashiga kakuma fito da ɓacin rai, ina Zahrah’n takene me yasameta?” cikin damuwa Baffa yayi tambayar domin shi gaba ɗaya kansa ya kulle.

Daure zuciyarsa yayi haɗe da cewa “Tana nan lafiya, gobe da safe zamu zo mu ɗauketa” 

Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe me ƙarfi yagodewa Allah da ba wani abun bane yasamu Zahrah, to amma ae da anbarsu sun ganta…

A ƙofar gida Dr.Sadeeq ya sauƙesu haɗe dayi musu saida safe yaja motarsa yayi gaba..

Suna shiga gida Inna ta kalli Baffa haɗe da cewa “Anya kuwa Malam bakaganin cewa akwai matsala?”

“Bawai gani nakeba, tabbas ma nasan akwai matsala Salame, sai dai fatana ɗaya shine Allah yatsare Zahrah, amma tunda Likita yace gobe da safe zamu koma asibitin, saimu jira zuwa goben idan Allah yakaimu”

“To Allah yakaimu” Inna tafaɗa jiki a sanyaye… Da “Ameen” kawai Baffa ya amsa.

Kamar yanda Zaid ya kwana a zaune, haka Dr.Sadeeq yakwana juyi, gaba ɗaya kansa ya kulle, yarasa meke faruwa,   baisan waye wannan gayen ba, amma tabbas yaji tsanarsa fiye da misali, amma babban abun tambayar shine me yasamu Zahrah har aka kawota asibiti? sannan kuma meke tsakaninta da wannan mutumin? tambayar dayake buƙatar a amsa masa kenan, amma babu wanda zai amsa masa,   tambayar da ta kuma hanasa bacci kenan…

Ƙarfe bakwai na safe Zaid yasa aka turo masa nurses guda biyu, suka zo dankula da Zahrah, saboda yana buƙatar yaje gida yayi wanka…..

Tamkar amafarki haka fyaɗen da yayi mata yasake dawowa cikin idanu da ƙwaƙwalwarta, wani irin nishi tayi haɗe da sakin ƙara  mai sauti,  lokaci guda kuma ta ware idanunta da suka cika tab da ƙwalla, da sauri nurses ɗin nan sukayo kanta.

Kallon Nurses ɗin tashiga yi, haɗe da soma ƙaremawa ɗakin da take ciki kallo, tabbas idan ƙwaƙwalwarta bata juye ba, zata iya cewa nan ɗakin asibiti ne sannan kuma waƴan nan dake tsaye a gabanta nurses ne.

“Barkanki da tashi, me kike buƙata yanzu a kawomiki?” ɗaya daga cikin nurses ɗin nan ta tambayi Zahrah  cike da kulawa…

“Idanunta dasuke zubar da ruwan hawaye, ta ɗaga ta kalli nurse ɗin haɗe da girgiza kanta alamar batason komai.
Hanun nurse ɗin takamo duka biyu haɗe da fashewa da wani irin kuka me ciwo, da’alama wani abu takeson faɗawa nurse ɗin.. Dai dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Zaid ne yasha adonsa sai zuba ƙamshi yake.
Tsayawa yayi cak daga bakin ƙofar sakamakon ganin yanda Zahrah take kuka..

“Me kukayi mata?” yajefawa nurses ɗin tambaya cikin yanayi na rashin yarda dasu.

“Bamuyi mata komai ba,ranka ya daɗe tashinta kenan tasoma rusa kuka” su duka biyu suka haɗa baki wajen faɗan maganar…

Tamkar wanda aka zuba mata narkakken dalma haka taji sauƙan kalamansa acikin kunnuwanta, rumtse jajayen idanunta tayi, ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito.
A hankali Zaid yasoma takawa zuwa gare ta.

“Zahrah” yaƙira sunanta dai dai lokacin daya ƙarasa kusa da’ita.. Tunkafun yagama rufe bakinsa yaji sauƙan wani irin gigitaccen mari akan ƙuncinsa,  kafun ƙwaƙwalwarsa tagama tantance masa abun dake faruwa, yakumajin sauƙar wani marin aɗaya ɓangaren hagu na kumatunsa..

Kasa koda motsawa yayi saima hangame bakinsa da yayi  haɗe da zaro idanu yana kallonta,, Gaba ɗaya marukan nan Zahrah ce ta shararawa Zaid akan fuskarsa..

Yanayin yanda idanunta sukayi ja kace barkono ko attarugu aka watsa mata a ciki.
“Kazone ka sake cutar dani? to gani kacutar dani, gani nace ka cutar dani!!” tafaɗi haka da wani irin tsawa..
Cikin matsanancin kuka Zahrah tasanya hannayenta duka biyu tashiga dukan sa, tako ina Zahrah ke kai masa duka  tana kuka, ganin hanu bazai wadarta ba yasanya ta sanya bakinta, tashiga cizonsa a ƙirjinsa, hakama bai mata ba saida ta ɗauki wani ƙarfe dake  kusa da’ita tashiga kwaɗa masa a jikinsa tana kuka me tsuma zuciya… Haka Zaid ya tsaya tamkar gunki Zahrah na cizo da yaƙushinsa, gakuma dukan da take kai masa,   amma yakasa yi mata komai, yakuma kasa koda motsa hanunsa ne..   dai dai lokacin su Dr.Sadeeq suka shigo cikin ɗakin, turus suma sukayi sakamakon ganin abunda ke faruwa.

“Kasheni zaifi maka sauƙi aduniyar nan, akan ace kabarni da raina, natsaneka, dan Allah ka kasheni!!” Abun da Zahrah ke faɗa kenan tana kuka.  Kowa a wajen tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, bakomai ke tashi a ɗakin ba face kukan Zahrah,  tun tana dukansa da’iya ƙarfinta har ƙarfin nata yasoma ƙarewa a hankali ta sulale  zuwa  ƙasa, saboda kuka har shiɗewa take…

“Zahrah” Dr.Sadeeq yaƙira sunanta, cikin wata irin murya.. Jin muryan Dr akunnenta yasa taɗago kanta, tana ganinsa tsaye tatashi a guje haɗe da nufar inda yake da sauri tafaɗa cikin jikinsa haɗi da rungumesa ƙa ƙam,wani sabon kukan kuma ta sanya, haɗe da soma buga kanta akan ƙirjinsa..

Duka hannayensa shima yasanya ya rungumeta..

“Wayeshi?” Dr. Sadeeq yayi mata tambayar acikin kunnen ta..

“Shine wanda yaruguzamin rayuwata, shine yarabani da budurcina, shine yayi sanadiyar lalacewar farinciki na!!”  Zahrah ta bashi amsa cikin matsanancin  kuka, muryarta ko fita batayi da kyau tsabar kuka…

Iya kaɗuwa Dr.Sadeeq ya kaɗu dajin cewa wai wanda yayiwa Zahrah fyaɗe ne tsaye a gabansa, kallon tsana Dr.Sadeeq yashiga yi mawa Zaid..
Zaid kuwa tuni idanunsa sun rune sun zama jajur dasu, jikinsa har rawa yake, koda sau ɗayane baiji zafin duka dakuma marin da Zahrah tayi masa ba, babban abun da yayi masa zafi, shine yanda Zahrah taje jikin wani ta lafe.  Tun da yake a rayuwarsa baitaɓa jin abun da yaji a yau ba… Takowa yashiga yi harzuwa inda suke tsaye ita da Dr.Sadeeq, hanunsa yaɗaga domin ya ciro Zahrah daga jikin Dr.Sadeeq. Da sauri Dr.Sadeeq ya tura Zahrah bayansa, haɗe da damƙe hanun Zaid wanda yakawo daniyar taɓa Zahrah..

“Babban kuskuren da zakayi a rayuwarka shine kayarda hanunka yasake taɓa jikinta, kayi na farko yakuma isheka, saboda haka ka kiyaye! ”  Dr.Sadeeq yafaɗi haka cikin matsanancin ɓacin rai…

Hanun Zahrah yakama haɗe da janta suka fice daga cikin ɗakin, da sauri su Inna ma suka rufa musu baya,  saurin  dafe saitin  zuciyarsa Zaid yayi, wanda yakeji tamkar zatayi tsalle ta fito waje.. Jingina bayansa yayi da bango haɗe da lumshe idanunsa.. Zafi yakeji a ƙirji dakuma zuciyarsa, take wani irin ciwon kai da zazzaɓi me zafi suka sauƙar masa alokaci guda..

Dr.Sadeeq dakansa yasanya Zahrah a mota, wacce har yanzu kuka take, ataƙaice dai tsabar kuka numfashinta har ɗaukewa yake….  Saboda tsabar gudun da Dr.Sadeeq keyi cikin mintuna ƙalilan suka isa gida, kowa acikinsu yana cikin tashin hankali.  Inna ce takama Zahrah takaita ɗakinta.   Bayan minti kaɗan Inna tafito  daga ɗakin Zahrah da sauri.  “Likita temaka numfashinta yana shirin ɗaukewa, taƙi daina kukan” Inna tafaɗa a ruɗe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button