NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr.Sadeeq yana shiga ɗakin yace inna tabasa ruwa, aikuwa mintuna kaɗan Inna takawomasa ruwa, cewa yayi Inna taɗan basu wuri bamusu Inna tafita a ɗakin…

ɗago Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da kai kofin ruwan bakinta,  sosai tasha ruwan, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya,  amma still hawaye na gangara akan fuskarta..

Idanunta dasukayi luhu luhu saboda kuka ta ɗago dasu  takalli Dr.Sadeeq, saikuma tasake fashewa da kuka, haɗi da faɗawa cikin jikinsa tarungumesa ƙam,  hanunsa duka biyu yasanya shima ya rungumeta,  a hankali ya shiga hura mata kunnen ta, saboda hakan zai sa taɗan samu relief, koba komai kukan nata zai tsagaita.  Har tsakiyar kansa yakejin kukanta.
Tsawon mintuna 15 yakai yana hura mata kunne, a hankali tasoma rage sautin kukan nata,  bayan kamar mintuna 5 yajita shiru, sai sauƙar numfashinta da yake ji akan ƙirjinsa  akai akai..
Yana duba fuskarta yaga tayi bacci, hawayene yaji suncika masa idanu, tabbas Zahrah taga ƙaddara a rayuwarta, wani irin tausayinta yakeji me tsanani, tabbas idan ya aureta zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya mantar da ita duk wani damuwa da tshin hankalin da ta tsinci kanta ciki, zai kuma yi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin yabata farinciki me ɗorewa.
A hankali ya kwantar da’ita, haɗe da sanya hanu ya gyara mata dogon gashinta da ya rufe mata fuska.   Yajima yana kallonta kafun  daga bisani ya tashi yafita daga cikin ɗakin…

Zaune yasamu Baffa da Inna a tsakar gidan sunyi jigum.  Yana fita suka tsaresa da ido da’alama bakinsu ɗauke yake da tarin tambayoyi..

Ajiyar zuciya ya yi haɗe da cewa “Tasamu bacci, kada ayi wani abu da zai tasheta, ni zan wuce office anjima zandawo” 
Har bakin motarsa Baffa yarakasa bayan sun tattauna wata magana me mahimmanci….

Zaid ne zaune a cikin falon sa dake guest hause ɗinsa,  kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa yana cikin tashin hankali, kwalaben giyane zube a gabansa, guda uku daga cikin kwalaben duk ya shanye giyan dake a
cikinsu,   ba abun dake gigita masa tunani da ƙwaƙwalwa kamar yanda Zahrah ta nunamasa tsana a fili ƙarara,  kallonsa yakai ga hanunsa na dama wanda yake fidda jini, bakomai yajawo hakan ba face ƙarfen da Zahrah ta kwaɗa masa akan hanun,,  runtse idanunsa dasuka kaɗa sukai jajur yayi, haɗe da cije laɓɓansa,  wani irin  zafi yakeji acikin zuciyarsa a duk sanda idanunsa suka hasko masa  lokacin da Zahrah taje ta faɗa ƙirjin Dr.Sadeeq,  jiyake kamar ya kurma ihu, ko zai samu salama acikin zuciyarsa…. Ahankali yamiƙe tsaye haɗe da nufar ɗakinsa,  Da ƙyar yake iya tafiya, saboda abuge yake mankas, kai tsaye   ɗan ƙaramin drowern dake kusa da gadonsa yanufa,  wani tablet yaɗauko haɗe da ɓarewa kusan guda takwas ya watsa a bakinsa, haɗi da korawa da ruwan swan…  Faɗawa kan gado yayi yana me rumtse idanunsa,  “Natsaneka” shine kalmar da tafi ɗaga masa hankali aduk cikin kalaman da Zahrah ta faɗa masa.  itace kuma kalmar da takeyi masa yawo acikin kansa, cikin wani irin yanayi Zaid yatashi tsaye haɗe da nufar wajen da yake aje kayan shafansa,  watsi yashigayi da duk wani abu dake kan dressing mirror ɗin nasa,  lokaci ɗaya yayi buji buji da ɗakinsa, yayinda ya fasa gaba ɗaya kwalaben turarensa, har sai da wasu kwalaben suka yankesa a hanu da ƙafarsa, amma don tsabar baƙin kishi ko zafi baiji ba, idanunsa Zahrah kawai suke hangomasa kwance a ƙirjin Dr.Sadeeq.  Lokaci ɗaya yaji wani irin juwa ta ɗebesa, harsai da yariƙe bango, a daddafe yaƙa risa kan gadonsa ya kwanta,  ji yayi kansa yasoma juyawa, yayinda idanunsa suka soma rufewa, yasoma ganin komai bibbiyu,  cikin mintuna ƙalilan  idanunsa suka rufe ruf…..

Follow me on Whatsapp and Wattpad

25/December/2019

Wattpad user name fatymasardauna
????????????????????????????????????????

                SHU’UMIN NAMIJI !!

      Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

         
         WATTPAD
   @fatymasardauna

Editing is not allowed????

     
      CHAPTER 68 to 69

 
Ba’itace ta farka ba sai wajen ƙarfe ɗaya na rana..

A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaɗa suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buɗe idanun nata ba sai yanzu.  Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiɗin yacika ɗan iska kuma shu’umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji ɗar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiɗin acikin ƴan iska ma daban yake,, haka nan taji gaba ɗaya zuciyarta ta ƙeƙashe takuma bushe,  lallai tunda ya nuna mata shiɗin babban ɗan iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako ƙafa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali… Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maƙurar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taɓa mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baƙin duhu,  ya katse mata jin daɗi da kuma walwalanta,  ya lalata mata rayuwa a rana ɗaya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata ƙarfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar ƴa mace?  tasan ƙiyayya amma kuma zafin ƙiyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne,  tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haƙiƙa ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ba’irin ƙuncin nan bane da yake fita,  lallai ƙuncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roƙi Allah daya sassauta mata…..

Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haɗe da miƙewa zaune, babu amfanin ɓata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba.     Kayan jikinta tashiga cirewa, haɗe da ɗaura zani akan ƙirjinta kana ta sanya lufaya….

Tana fitowa daga cikin ɗakin nata, Inna ta kalleta haɗe da cewa.

“Yauwa Zahrah kintashi ko? ya ƙarfin jikin naki de?” alokaci ɗaya Inna tajero mata duka waƴan nan  tambayoyin..

“Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba ɗaya banajin daɗin jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah” tafaɗi maganar tana me ɗan rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana ƙoƙarin ɗibanta..

“Kinkuwa ci sa’a  yanzu na ɗaura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki ɗiba, amma idan kin ɗiba ki ƙaramin ruwa acikin tukunyar” Inna tafaɗi haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin  dake ɗaure kan murhu…

Sosai taji daɗin jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi,  bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haɗe da ɗaukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin  idanunta, ko powder bata shafa ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button