NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Doguwar rigar atamfa irin me sauƙin kuɗin nan tasanya ajikinta, haɗih da ɗaura hijab akan kayan nata mai kalar blue,  yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuɗi).   Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba….

Kallon Inna dake ƙoƙarin sauƙe tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace.    

“Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah”

“Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace ɗazu ɗazun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauƙin da zaki soma fita yawo?”

(Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol)

“Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!” Zahrah ta faɗi haka cikin yanayi na nuna zaƙuwa.

“Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi”

“A’a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci” takai ƙarshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan…

Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na  mamaki…

Giransa ɗaya ya ɗage haɗe dayin murmushi….   “Ashe ma kinyi sauƙi, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me takowa zuwa  wajen da take tsaye.

Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru ɗazu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taɓa mutumin da ba muharrami’n su ba,  duk da cewa ba’acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba…

“Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita ɗakin mijinta” Dr.Sadeeq  ƴafaɗi haka cike da zolaya.

Sai alokacin ta’iya ɗago kanta ta   aika masa da
hararan wasa,,,,,   ” Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?”

“Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keɗin sauri kike zaki unguwa ko?”
Yaƙare maganar yana me leƙa fuskarta wanda ta sunkuyar da ita ƙasa.

Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da sanya haƙorinta na sama taɗan datse leɓenta  na ƙasa..

“Yajikin naki?” yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya.

“Dasauƙi, dama ni lafiyata ƙalau”  tabasa amsa a ta ƙaice..

“Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti”

Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace,  “Lafiyan?” ta tambaya cike da mamaki.

“Eh itafa lafiyan, to baga example  akan ki ba”  yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya’isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa..

“Hmm” kawai Zahrah tace haɗi da ɗan satan kallonsa, aikuwa karab suka haɗa idanu, saurin ɗauke nata idon tayi.

Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiɗin ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda  da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya ɓanɓareta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya’iya saboda alokacin tana cikin halin buƙatar taimako, kum san nan  shi be rungumeta don yaji daɗi ba.

“Inazakije ne haka, da rana tsaka?”  yajefo mata tambaya…..

“Gidan su Husnah zani”  ta basa amsa a taƙaice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba…

“Shikenan muje saina kaiki, domin kinsan samun abun hawa zaimiki wahala, saboda rana tayi sosai” 

Kallonsa tayi naɗan sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace “Dama kabarni, koda ƙafana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma nasan zan samu”

“Da gaske zaki iya takawa da ƙafa daga nan har gidansu Husnah?  to shikenan tunda zaki iya, zaimafi kyau ki taka da ƙafan, saboda kisamu ki ɗan rage wan nan ƙiban dakika haɗa, gaba ɗaya duk yasa kin yi muni, kin zama wata super mama dake”  yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo.

Waro idanu Zahrah tayi haɗi da soma kallon kanta, wai tayi ƙiba, takuma zama super mama.

Take idanunta suka yi raurau dasu, yayinda ruwan hawaye ya soma cika cikin su, “ashe da gaske tayi ƙiba bata sani ba? gashi harya fara goranta mata, to me yasa ita bataganin ƙibanta?” tatambayi kanta…

Dariya Dr.Sadeeq yasanya domin kuwa yalura tayarda da maganarsa, shikuwa wasa yake mata, bawai dagaske tayi ƙiban bane, gashi har tana ƙoƙarin yin kuka, shikam ya lura gaba ɗaya kuka baya bata wahalar yi, hawayenta a maƙale suke, mintuna kaɗan saikaga sun tsiyayo”

“Kintsorata ne dan nace kinyi ƙiba? hmmm nan gaba kaɗan zakiyi bindiga ki fashe saboda tsabar ƙiba”

Sake waro manya manyan idanunta tayi zuwa yanzu kam har ƙwallan cikin idanunta sun gangaro akan fuskarta….

“Au kinfiso ki kumbura ki fashe ɗin kenan?” yatambayeta yana me danne dariyar da ta taso masa…

Kai ta girgiza masa alaman “A’a”

“To kinaso na faɗamiki me zakiyi wanda zaisa bazaki fashe ba?”

Dasauri ta ƙaɗa kai alamar tanaso yafaɗa mata…

“Yauwa ƴar gari ashe de kema bakyaso ki fashe, to abu ɗaya zakiyi wanda shizai hanaki fashewa, kinga de ni likita ne ko? nakumayi zurfi cikin karatun likitanci, saboda tsabar zurfin da nayi ina karatune ma yasanya nagano cewa idan mutum yacika matsantawa kansa da damuwa da kuma yawan koke koke to yakan iya kumbura kamar de yanda kikayi yanzu, daga nan kuma bayan kamar 1 week shikenan sai dai yayi bindiga yafashe fush, shikenan kuma sai de wani bashi ba, kinaso haka ta faru dake?” yafaɗi haka yana me zura mata manya manyan idanunsa.

“A’a” tabashi amsa cikin murya me sanyi, domin kuwa a haƙiƙanin gaskiya ta yarda da kalamansa, ko kaɗan bata gano cewa shiya shirya abunsa ba. take fargaba ya ɗarsu a zuciyarta….

Wata irin dariyane takama Dr.Sadeeq amma kuma ba halin yasaki dariyar tasa, dolensa ya danne ta matuƙar yanaso Zahrah ta gamsu da bayanan sa hundred percent,,, lallai yau yaƙara tabbatarwa kansa cewa Zahrah yarinyace kuma yarinta na damunta, amma inbanda haka ta’ina ta taɓa jin ance mutum ya yayi bindiga yakuma fashe da ransa.

Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da cewa “To yanzu de zaɓi ya rage gareki Yarinya, ko ki daina kuka ko kuma ki fashe, saboda haka zaki biyoni muje ne ko kuwa a’a nayi tafiyata?”

“Zanbika” tafaɗa cikin muryar tsoro saboda gaba ɗaya kalaman likita sun rikitata…

Murmushin gefen baki Dr.Sadeeq yayi haɗe da juyawa yanufi wajen motarsa, yana me danne dariyarsa…
Zahrah kuwa tamkar wacce ƙwai yafashewa haka ta bi bayansa.

Saida suka hau titi kafun yajuyo da kallonsa gareta, gani yayi tayi jigum da’ita, da’alama tunani takeyi….

“Amma nace miki yawan sakai a damuwa shike sa mutum ya fashe ko? hala don ba ɓangaren likitanci kike karanta ba shiyasa bakisan da hakan ba”

Kallonsa tayi haɗe da ƙwaɓe fuska,  cikin murya me sanyi tace “Ni ae yanzu bawai a damuwa nake ba, kawai de ina kallon hanya ne” ….

Kansa ya jinjina haɗe da cewa tayi masa kwatancen gidansu Husnah’n domin shi basani yayi ba….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button