SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

A dai dai ƙofar gidan su Husnah ya tsaida motar tasa, haɗe da dawo da kallonsa ga Zahrah wacce ke ƙoƙarin buɗe murfin motar tayi ficewarta…
“Da yaushe zaki koma gida?”
Ɗan jim tayi kana tace “Ko zuwa bayan la’asar ma, irin ƙarfe biyar ɗin nan haka” yanayin yanda taƙai ƙarshen zancen nata tana me juya kyawawan idanunta, shi ya shagaltar dashi har ya tsaida idanunsa akan ta, sosai takeyi masa kyau idan tana juya idanunta, ya kuma lura cewa hakan al’adarta ne, idan hartana magana, to takan juya idanunta masu kyawun gani, musamman idan maganar tazo ƙarshe..
“Ya de?” Zahrah ta tambayeshi sakamakon ganin da tayi yakafeta da idanunsa..
“Babu, kikulamin da kanki kinji, zan zo na ɗaukeki idan 5 ɗin tayi, inafata babu wata matsala?” yatambayeta cike da nuna kulawa.
Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da cewa
“Babu wata matsala”
Yana kallonta tabuɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin gidan su Husnah tashige… Yana tabbatar da shigewarta yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yaɗauki hanyar asibitinsu, saboda dama aiki yabaro yazo gareta, to yazaiyi tunda tazama wani ɓangare na jikinsa…
Da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah tana mejin daɗin ziyarar bazata da Zahrah’n takawo mata, saboda bata faɗa mata zata zoba. Bayan Zahrah ta gaisa da Momyn Husnah ne, suka rankaya zuwa ɗakin Husna’n,,, ba ɓata lokaci Husnah ta cikawa Zahrah gabanta da kayan ciye ciye dasu drinks.
“Naji daɗin zuwanki sosai ƙawata, kamar kuwa kinsan ina kewarki, jiyafa har mafarkin ki nayi, da safe naƙira wayarki kuma najita switch off, ina fata dai kina lafiya?”
Hijabin dake jikinta ta cire haɗe da cewa “Lafiya amma ba sosai ba”
Da sauri Husnah ta dawo da kallonta ga Zahrah
“Meyafaru dear?” Husnah tatambaya cike da kulawa.
Kallon Husnah Zahrah tayi na tsawon minti guda….
“Babuƙatar tuna abun da yafaru Husnah, saboda kinsan inada raunin zuciya, tuna abun zai iya sake jefani cikin wani hali”
Damuwane ya bayyana ƙarara akan fuskar Husnah haƙiƙa tamkar ƴar uwa ta jini take kallon Zahrah saboda haka duk wata damuwa ta Zahrah damuwar tace itama.
“Zaki iya ɓoyewa kowa damuwarki amma bandani Zahrah, sai de kuma babu amfanin takuraki akan cewa lallai sai kin sanar dani, saboda bansan wani hali zaki samu kanki aciki ba bayan kin faɗamin”
Dafa kaɗan Husnah Zahrah tayi haɗi da daure zuciyarta…
“Nasake haɗuwa da…. da….wanda ya yimin fya…….” kasa ƙarasawa tayi saikawai tafashe da kuka.
Ko bata ƙarasaba Husnah tafahimci me Zahrah take nufi.
Cike da tashin hankali Husnah tasoma salati…
Sake jawo Zahrah jikinta tayi haɗi da rungumeta….”Ki daina kuka, yanzu ba lokacin kuka bane Zahrah, kinmaci abinci kuwa ?” Husnah ta tambayi Zahrah cikin kulawa…
“Banajin yunwa Husnah!” Zahrah tafaɗi haka cikin shaƙewar murya, wani yunwa zataji ita da take cikin bala’in sake ganin Zaid…
“Kinsan de ba kyau zama da yunwa ko, kinga yau ni namayi abincin dakaina, bana zuba mana muci tare, kuma dan Allah kada kicemin a’a”
Babu yanda Zahrah ta’iya dole tabiyewa Husnah taci abinci, gaba ɗaya Husnah se zuba take tamkar kurna, takasa yin shiru koda na minti biyu ne, tayi hakanne kuma saboda ta gusarwa da Zahrah da muwarta, daga ƙarshe de har game, Husnah ta jona musu a tv suka buga, sosai kuma hakan ya ɗebewa Zahrah kewa….
Tare sukayi sallan la’asar daga nan kuma Husnah ta ɗebi Zahrah, suka tafi shoprite, dangin su ice cream da chocolate suka jida, daga nan sukayo gida.
Kamar yanda yafaɗa ƙarfe biyar da minti ɗaya dai dai ya ƙaraso ƙofar gidansu Husnah.. Ƙiran Zahrah yayi a waya ya tabbatar mata cewa yana ƙofar gidan su Husnah….
Zahrah na ajiye wayarta Husnah ta kalleta haɗe da kashe mata ido ɗaya.
“Ƙawata tazama ƴar soyayya, sosai yanayin soyayyarku da Man ɗin nan yake kasheni, kinfasan gayen naki ya haɗu over, da badan ke bace danayi snatching ɗin sa!” cike da zolaya Husnah ta faɗi maganar…
Dariya suka sanya su dukansu, haɗe da rungume juna.
Har bakin motar Dr.Sadeeq Husnah ta raka Zahrah, bayan Momyn Husnah ta cikawa Zahrah leda da dangin su turare dakuma kayan shafa hadda kyautar wani haɗaɗɗen leshi, sosai Zahrah tayi godia, hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan daya sanya bata son zuwa gidansu Husnah, saboda idan dai tazo tofa sai mahaifiyar Husnah tayi ɗawainiya da’ita wajen bata kyautan kayayyaki masu kyau da tsada…
Harsaida Husnah taga tashin motar su Zahrah kafun takoma cikin gida…
“Kinsamo abun daɗi shine kokimin tayi ko?” Dr.Sadeeq yafaɗi haka ga Zahrah wacce ta ɗaura ledan sayayyar da sukayi a shoprite ita da Husnah akan cinyarta…
“Murmushi me sauti tayi haɗe da cewa “Ba’abun daɗi bane, kayan shafa ne”
“Um um ni banyarda ba, kitaimaka kiban ko chocolate ɗaya ne, naci yunwa nakeji, yau duk banci abinci ba” yaƙare maganar yana me shagwaɓe fuska, sai kace wani ƙaramin yaro…
Dariya Zahrah tayi haɗe da satar kallonsa “wai ma ya’akayi yasan cewa acikin ledar hanunta akwai chocolate?” ta tambayi kanta.
“Kina mamakin ya’akayi nasan cewa a ledarki akwai chocolate ko?, ai ba abun mamaki bane, tunda nasan shiɗin favorite ɗin ki ne” yafaɗi haka cikin yanayin shauƙi, amma still idanunsa naga titi..
Buɗe ledar tayi taciro wani chocolate mai kyau da daɗi kusan yafi kowanne ma daɗi acikin sauran chocolate ɗin da ta saya, ta miƙa masa haɗi da cewa “Ga wan nan amma bazan iya baka kyautarsa duka ba, saboda haka kaci rabi kabarmin rabi”
Saurin kallonta yayi fuskar sa ɗauke da murmushi… ” Naƙi wayon, idan har kinaso na karɓa saide kibani kyautansa duka”
Turo ɗan ƙaramin bakinta tayi gaba, haɗe da noƙe kai alamar hakan bazai yiwuba, kallon bakin nata yayi, harsai da yaji tsikar jikinsa ƴa zuba, hmmm lallai idan ya auri Zahrah, zai tsotse wan nan ɗan ƙaramin bakin nata ne yanda ya kamata????…
“Kici chocolate ɗinki ke kaɗai nikam na gode” yafaɗi haka a taƙaice domin dama wasa yake mata baci zaiyi ba, shi da yake fama da ciwon ciki idan yaci chocolate kuma yake nan?
Lokacin da suka iso gida biyar da rabi har ta gota… kallon Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da ɗan nisawa.
“Nagama haɗa miki kayan lefe da kuma sauran abun da suka dace, wace rana kikeso a kawo?”
Saurin ɗaga idanu tayi ta kallesa jin abun da yace.
Idanunsa ɗaya ya kashe mata, wanda yasanya taji gabanta yafaɗi, saboda a wajen mutum ɗaya ta saba ganin irin wan nan kashe idon, kuma shi hakan yazame masa al’adarsa ne, bakowa bane kuma face ZAID.
“Zamuyi waya” Zahrah tafaɗi haka don son kawar da tambayar tasa, saboda a yanzu bata da amsar da zata basa..
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da dafa steering motar da duka hannayensa biyu. “Shikenan idan kin nutsu zan ƙiraki” yafaɗi haka cikin sanyin murya..
Murmushi tayi masa irin me tsayawa a rai ɗin nan, kana tabuɗe murfin motar tayi ficewarta, sai de batare da yasani ba, ta aje masa wan nan chocolate ɗin…
Bayan kamar 2 minute da shiganta cikin gida yaja motarsa shima yayi tafiyarsa…
ZAID
Tunda yasha wan nan ƙwayoyin baisan inda kansa yake ba harsai ƙarfe uku na yammaci,, ko da ya buɗe idanunsa ji yayi duniyar na juya masa, amma haka adaddafe ya shiga bathroom yayi wanka haɗe da ɗauro alwala, sai yanzu zaiyi sallan Azahar don tsabar asara, gashi har la’asar ma takawo kai….