SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana idar da sallan azahar ya miƙe daga kan sallaya haɗe da zura slipper ɗinsa yafice daga ɗakin… Kai tsaye masallacin jikin gidansu yanufa don gudanar da sallan la’asar wanda ake ƙira yanzu.. Ko a cikin masallacin mutane sai mamakin ganinsa suke saboda abune mawuyaci ka gansa a masallacin da wan nan time ɗin, yafi yawan zuwa sallan isha ko asuba, amma banda azahar da la’asar saboda a wan nan lokacin ma kwata kwata baya gida, sai de yayi sallah a wani wajen. Baidamu da kallon da mutane suke masa ba, yana idar da sallan sa yatashi yayi shigewarsa cikin gida…
Tsab yagama shirya kansa cikin ƙananan kaya, riga da wando na blue jeans wanda suka matuƙar amsar jikinsa. Ba abun da yake sai tashin ƙamshi.
Zama yayi abakin gadonsa haɗe da sanya hanunsa duka biyu ya dafe kansa dake yi masa ciwo kaɗan kaɗan,, wani irin sabon al’amari yakeji a cikin zuciyarsa, baisan da wani suna ze ƙira abun ba, amma tabbas jiyake zuciyarsa na azalzalarsa akan Zahrah, san nan yanajin cewa itace muradinsa, saurin buɗe idanunsa da ke lumshe yayi sakamakon hasko masa marukan da Zahrah ta sharara masa akan fuskarsa da sukayi, hanunsa yakai kan ƙuncinsa ya shafa haɗe da sakin murmushi, tunda yake a a rayuwarsa wata mace banda mahaifiyarsa bata taɓa kai hanunta jikinsa da sunan duka ba ballan tana har akai ga mari, sai gashi yau, Zahrah ta shararamasa lafiyayyun maruka harguda biyu akan fuskarsa, takuma haɗa masa hadda duka, amma ko kaɗan baiji zafin abun ba, anya kuwa shine? kodai an musanyashine bai sani ba? meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarsa ne? shine Zaid kuwa? Yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin….
(Team Zaid saiku basa amsa, shi ɗin ne koba shiɗin bane?)
27/December/2019
Follow me on Whatsapp and Wattpad
Wattpad user name fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
???? Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 70 to 71
Yajima zaune a kan gadon nasa, gaba ɗaya kansa ya kulle yarasa meke damunsa, wai shin da gaske SO yake ko kuwa? anya kuwa yanaga zaman sa haka zai yi wu? zaifi masa kyau yanemi Abid domin shi ne kaɗai zai iya fayyace masa halin da yake ciki, tabbas shi koda son Zahrah Abid ɗin yace masa yanayi yanzu bazai musa masaba, idan kuwa har haka so yake to yana mawa Zahrah so me tsanani, saurin laluɓar wayarsa ƙirar Samsung dake kusa dashi yayi. Numbern Abid ya dannawa ƙira, bugu biyu Abid ya ɗaga ƙiran cikin muryan kasala yace “Mutumin ya akayi ne, ka katseni ina cikin holewata”
“mcheeww aikin ka kenan cin ƴaƴan mutane, kana ina yanzu inaso muyi serious magana da kai” Zaid yafaɗi haka cike da zaƙuwa.
Miƙa Abid dake kwance shame shame a gado yayi haɗe da sakin daria, wai yau shi Zaid ke cewa baida wani aiki se cin ƴaƴan mutane, hmm ai duk iskancinsa shikansa yasan a ƙarƙashin Zaid yake, domin kuwa Iskancin Zaid me lasisi ne.
Cike da ƙuluwa Zaid yace ” Nifa bana ƙira ka kamin iskanci bane, da zaka tsaya kanamin dariya”
“Yi haƙuri mana nawan, maganartaka ce tabani dariya, zuwa anjima mu haɗu a Millinion Park ina fata de bawata matsala bace ta afku?”
Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe da duban agogon Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. “Shikenan to muhaɗu ƙarfe 5 na yamma banakumason kamin african time, 5 nacika idan bakazoba, bazan tsaya ɓata time ɗina wajen jiranka ba” yayi maganar cikin yanayi da yake nuna cewa ba wasa yake ba..
“Okay” kawai Abid yace haɗe da aje wayartasa yajawo babe ɗin dake kusa dashi, suka ci gaba da watsewarsu ko kunyar Allah dayake ganinsu basayi, Allah karabamu da ƙeƙashewar zuciya Ameen.
Zaid yana aje wayartasa yasanya hanu yashafi cikinsa, sai alokacin yake tuna rabonsa da yasanya abinci acikin cikinsa tun jiya da yammaci, amma saboda tsabar yashiga tension ko yunwarma bayaji, murmushi yayi tunowa da yayi da yanda yaji muryan Abid, dagajin yanda yaji yanayin muryartasa yatabbatar masa cewa holewa da mace Abid ɗin keyi, “hmmm Abid ba dama wajen iya latsa mace” yafaɗi haka a fili, shikamma rabonsa daya kusanci wata mace harya manta, shi yanzu ko mace ma yagani bata wani burgesa, yanzu idan zaiyi sex to badakowacce mace yakeso yayi ba, face Zahrah ita kaɗai yakejin cewa zai iya sauƙewa damuwarsa yanzu, itakuma kaɗaice zata iya basa gamsuwa ɗari bisa ɗari. Miƙewa yayi yanufi wajen fridge ɗin dake ɗakin nasa, fresh milk ya ɗauka haɗe da tsiyayawa a cikin glass cup, zama yayi yasoma sipping fresh milk ɗin a hankali, gaba ɗaya hankali da tunaninsa sunaga Zahrah, ko yanzu wani hali take ciki? Allah masani…
Sake narke masa murya tayi cikin shagwaɓa tace “Nide bance bana sonka ba, aikaima kasan inasonka, kawai de nakasa sakewa da kai ne har yau!” taƙare maganar tana me rausayar dakanta gefe tamkar yana ganinta..
Dr.Sadeeq dake zaune cikin luntsumemiyar kujeransa na office ya lumshe idanunsa haɗe da gyara zaman wayar akan kunnensa, sosai shagwaɓan Zahrah ke sauƙar mai da kasala acikin jikinsa, yayinda idan yaji muryarta yake samun nutsuwa a cikin zuciya da ruhinsa…
“To meyasa bakya iya sakewa dani ne My Princess, kinkuwa san irin sonda nake miki? inasonki Zahrah fiye da tunaninki, amma bazaki gane hakan ba, sai idan nasameki a matsayin matata, na tabbata nan da 3 weeks kinzamo mallakina daganan kuma zaki gaskata soyayyata a gareki!” yafaɗi maganar tasa cikin yanayi na shauƙi..
Saurin kulle idanunta tayi haɗe da sanya hanu tarufe fuskarta, saikace wanda take aga banshi, sosai maganarsa yasa taji kunya,, ta lura haka Dr.Sadeeq ɗin yake watarana baruwansa kansa tsaye yake faɗar maganar da zaisanya taji kunya.
“My Princess kinyi shiru” Dr.Sadeeq yafaɗi haka a kasalance.
Numfashi Zahrah ta fesar haɗe da sake yin ƙasa da muryarta cikin shagwaɓan daya zamemata sabo tace “Munyi magana da Baffa, yace ku kawo kayan lefen duk sanda kuka shirya kawai”
Daɗi ne yakama Dr.Sadeeq harsaida yakasa ɓoye murnarsa idan kuwa hakane to tabbas acikin satin nan zai sanar da ƴan uwansa saisu shirya rananda zasu kawo kayan, shida zasuce yauma to tabbas da zaiso hakan.
“Naji daɗin maganarki My princess saboda haka kincancanci nabaki kyauta ta musamman, idan banzo da dare ba gobe zanzo insha Allah”
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗi da cewa “Nagode amma kariƙe kyautarka bayanzuba”
“Meyasa?” yatambayeta cikin yanayi na ɓata fuska.
“Saboda hidiman da kakeyi yayi yawa, dan Allah kabari haka kaji!” taƙare maganar cikin yanayin shagwaɓa.
“Inde akan kine Zahrah bazan taɓa gajiyawa ba, zanyi wani aiki yanzu zanƙiraki anjima kinji princess ɗina!” yafaɗi haka cike da lallashi…..
Haka sukayi sallama cike da kulawa ga junansu, yanzu kam tagama aminta da Dr.Sadeeq insha Allah kuma idan ta auresa zata basa farinciki me ɗorewa, iyaka iyawarta…..