SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai Zaid yashaƙa da irin yanda Abid yasanyasa agaba yaketa yi masa dariya,, tsuka Zaid yaja me tsayi haɗe da kawar da kansa gefe jiyake tamkar ya tashi ya rufe Abid da duka, idan banda iskanci taya zai sanyasa gaba yayi ta masa dariya bayan yagama jin matsalarsa…
Wani mugun kallo Zaid yajefawa Abid me ɗauke da tarin ma’anoni da yawa, ganin haka yasanya Abid saurin gimtse dariyarsa haɗe da kama hanun Zaid ɗin…
“Yi haƙuri Abokina, maganar ce tabani dariya”
Tsuka Zaid yakuma ja batare da yace komai ba…..
“Nafuskanci inda matsalanka ta dosa Zaid amma kuma nasan abune me wahala ka yarda da abun dazan faɗa ma”
“Bazaka gane yanda nakeji agame da’ita ba ne Abid, dakasan yanda nakeji a zuciyata da ka tausaya kasanar dani maganin matsala ta, kodai shine so ɗin da kake cewa?” Zaid yatambayi Abid cike da damuwa…
“Ƙwarai kuwa Zaid wan nan shine SO, sai de naka SO’n ya banbanta da sauran soyayya’n, kai naka soyayya’r me tsanani kakeyi, wanda tariga da tajima acikin jikin ka batare da ka sani ba, ina da yaƙinin cewa tun farko Son Zahrah kake bawai sha’awarta ba kamar yanda ka ɗauka!” Abid yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa…
Nannauyar ajiyar zuciya Zaid ya sauƙe haɗe da sanya duka hannayensa ya dafe kansa wanda yake ɗan sara masa a hankali.. Tabbas yanzu kam ko yaso ko yaƙi dolensa ya yarda da maganan da Abid yafaɗa masa, domin kuwa idan har ba soyayya ba menene ke damunsa dayake sawa yakejin zafi a zuciyarsa? idan ba soyayya ba menene yake sanya tunaninsa hargitsewa da zaran yatuno Zahrah? idan ba soyayya ba menene yake sanya sa rasa sukuni da nutsuwarsa aduk sanda yatunanota kokuma yaganta? lallai kuwa soyayya baimasa adalci ba da bai sanar dashi kansa ba tun sanda yafarasa batare da yasani ba..
Idanunsa da sukayi jajur dasu ya ɗaga haɗe da maida kallonsa ga Abid “Inasonta Abid inasonta sosai!”
Waro idanu Abid yayi yana me kallon Zaid idan da ba Zaid ɗin ne da gaske a gabansa ba, to tabbas da sai yace badaga bakin Zaid wa ƴan nan kalaman suka fitoba, yau Zaid da kansa yake cewa yakamu da son wata? lallai kuwa rayuwa tana shirin juyawa abokin nasa baya.
Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan ɗan ƙaramin table ɗin dake aje gabansu.
Kallonsa Abid yayi cike da mamakin ganin yanda lokaci ɗaya yanayin Zaid ɗin ya sauya.
“Inakuma zaka?” Abid yatambaya..
“Zanje gidansu Zahrah Abid, idanuna sun matsamin zuciyata har bugawa take Abid, ita kawai nakeson gani, idan har zata amince inaso ayau base gobeba koda ƙarfe ɗaya ne na dare a ɗaura mana aure da’ita” yanakai wa nan a zancensa yayi tafiyarsa.. Hangame baki Abid yayi yana kallonsa harya ɓacewa ganin idanunsa. Anyakuwa Zaid yana cikin hankalinsa? Kodai asiri yarinyar talakawan nan tayi masa ne? Abid yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin, bayan yasan baida amsa bai kuma da me basa amasar…
Zahrah dake zaune tana gudanar da assigment ɗinta, wani yaro yashigo cikin gidan nasu haɗe da kwaɗa sallama.. Amsa masa Zahrah tayi batare da taɗago kanta takalli yaron ba..
“Wai ana ƙiran Zahrah a waje” yaron yafaɗa yana me kallon Zahrah domin kuwa yasan cewa itace wacce aka aikosa yayi ƙiranta..
Sai alokacin Zahrah taɗago kanta ta kalli yaron, haka nan taji gabanta yafaɗi, to waye kenan yake sallama da’ita? ta tambayi kanta, wayarta dake kusa da’ita ta ɗauka haɗe da dubawa, 1 missed call tagani na Dr.Sadeeq, dayake wayartata a silent tasanyata shi yasa bataji ƙiran nasa ba, kenan shine yazo yaƙira wayarta bata ɗauka ba shiasa yaturo yaro. “Jekace inazuwa” ta bawa yaron amsa a taƙaice..
Miƙewa tayi haɗe da tattara takardunta tayi ɗaki. Mayafi taɗauka ta yafa akan kayan dake jikinta…
Tsaye yake ajikin motarsa yayinda yakifa kansa asaman motar yana me kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa..
Kanta a ƙasa tafito daga cikin gidan tana me duba wayar dake hanunta. Tsayawa tayi cak bayan ta haɗe wani miyau dayazo me ɗaci ya maƙale mata a maƙoshinta.
Murmushi yasakarmata haɗe da soma takowa zuwa gareta..
Lokaci ɗaya idanun Zahrah suka sauya kala daga fari zuwa ja, juyawa tayi a fusace tanufi hanyar shiga gida, da sauri Zaid yasha gabanta haɗe da marairaice fuska cike da tashin hankali yasoma cewa….
“Dan Allah Zahrah kitsaya ki saurareni, dan Allah kada kimin haka Zahrah, inaso ki saurare…..” kasa ƙare maganar nasa yayi sakamakon kyakkyawan marin da Zahrah ta shimfiɗa masa akan kyakkyawar fuskarsa…
Cikin ƙuna da kuma zafin zuciya haɗi da raɗaɗi Zahrah ta haɗa yatsanta na tsakiya dakuma babbar yatsarta, ta kaɗa ade de fuskar Zaid duk da kuwa cewa yakerema tsayinta..
“Natsaneka tsana mafi muni, natsani jin kowani irin kalma ce da zata fito daga bakinka, wlh wlh nayi rantsuwa sau biyu, idan har ka sake naƙara ganin fuskar ka to zanyi maka abun da baka taɓa tunani ba!” cikin matsanancin ɓacin rai taƙare maganar tana me raɓan gefensa zata wuce, Zaid da zuciyarsa tariga da ta karye baiyi ƙasa a guiwa ba yasake shan gabanta.
“Kimin duk abun da kikeso Zahrah, zanfi jin daɗima idan akace kece zakiyi silan mutuwa ta, dan Allah ki saurareni mana Zahrah!!” yaƙare maganar cikin rawan murya…
Kuka ne ya ƙwacewa Zahrah me tsanani cikin muryan kukan tasoma cewa…..
“Miye laifina Zaid? Menene aibuna? shin wani abu na aikata maka da ka zaɓi cutar da rayuwata? ashe de ganganci ne don na ɗau soyayyata na baka? me yasa ka yaudareni Zaid? meyasa dole saini kazaɓi ka tozarta? Kacutar da rayuwata ka dasamin ƙunci a cikin zuciyata, wlh natsaneka Zaid, Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mezaka amfana dashi acikin rayuwarka? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci? Natsaneka Zaid! Natsaneka!! Bana fata Allah yaƙara haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada! Dan Allah kafita a rayuwata Zaid!!!” cikin matsanancin kuka taƙare maganar tana me durƙushewa ƙasa domin kuwa zuwa yanzu tsayuwa ya gagarewa ƙafafunta…
Idanun Zaid ne suka kaɗa suka zama jajur dasu tamkar wanda aka zuba musu jan barkono. gaba ɗaya jikinsane yasoma ɓari, shi ɗin ma durƙusawa yayi agabanta cikin murya me tsananin rauni yaƙira sunanta,, saurin ɗaga masa hanu Zahrah tayi alaman batason jin komai daga garesa..
“Banason nasake koda jin muryarkane Zaid, kafita a rayuwata, wai mekake nema dani ne? ko kana tunanin zan sake aminta da kai ne? hmmm kayi babban kuskure Zaid idan kuwa har haka kake tunani, zaifi maka kyau, kamanta dani kakuma manta da wacece ni, ni na barwa Allah cutarwan da kayi agareni, kuma insha Allah nasan zai ɗaukarmin fansa,, sai de inaso kasani cewa har abada bazan taɓa yafe maka ba, inaso kuma kada kamanta da cewar natsaneka !” a fusace ta faɗa cikin gida haɗe da banko ƙofar gidan nasu.
Tashi yayi daga durƙuson da yake haɗe da bin bayanta da kallo, gaba ɗaya zuciyarsa tagama karaya, wani irin abu yakeji ajikinsa yayinda kansa yayi masa wani irin masifaffen nauyi, zafi yakeji azuciyarsa irin sosai ɗin nan.
Zahrah kuwa zamewa tayi jikin ƙofar gidan nasu tasaki wani irin kuka me tsuma zuciya. Se yaushene zata warke daga raɗaɗi dakuma ciwon abun da Zaid yayi mata? ganinsa yasake tasomata da mikin daya ƙi warkewa tsawon lokaci acikin zuciyarta, maiyasa Zaid yazame mata bala’i acikin rayuwarta? kuka tashiga yi sosai da sosai…