SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaid kuwa daƙyar ya iya jan ƙafafunsa yanufi motarsa, kasa tuƙa motar tasa yayi, gaba ɗaya idanunsa duhu suke gane masa, tabbas bazai taɓa iya tuƙa mota yana a irin wan nan halin ba,, da ƙyar ya’iya laluɓa wayarsa yaƙira driver’nsa… Mintuna kaɗan drivern Zaid yazo ya wuce dashi….
Saida tayi kukanta son ranta har sai da taji kanta yasoma ciwo kafun ta tsagaita, haɗe da miƙewa daga jikin ƙofar tashige cikin gida, direct ɗakinta ta wuce ta kwanta numfarfashi kawai take sauƙewa, lokaci ɗaya zazzaɓi yarufeta, harsaida tajawo mayafi ta lulluɓi jikinta….
Sanda yashiga falonsa ko gani bayayi sosai, wani irin ciwo kansa ke masa me tsanani wanda yasanya idanunsa sukayi nauyi, da ƙyar ya’iya jan ƙafansa yashiga ɗaki, kalaman Zahrah ne sukeyi masa yawo acikin kansa,, yatsani jin kalmar tatsaneshi da take yawan faɗa ɗin nan, wlhy a gurinshi da ta faɗi wan nan kalman gwamma ta sharara masa maruka koda kuwa guda biyarne akan ƙuncinsa.. Ya yanke shawara da de yakasance a irin wan nan yanayin ya gwammace yafita daga cikin hayyacinsa idan yaso bayan wasu tsawon lokaci yadawo cikin hayyacin nasa,, wasu ƙwayoyin magani yaɗauko harkala biyu, wanda suke gusarwa mutum da hankalinsa, maganin suna da hatsari sosai hakan nema yasanya ba’a sai dasu a bayyane sai de a ɓoye, kuma suna mugun sa bacci sosai… Saida ya ɓalli guda uku uku daga jikin kowani sachet, kafun ya watsa maganin cikin bakinsa, wan nan karon ko ruwa baisha ba haka ya haɗiye magungunan, yanda kalaman Zahrah ke dawowa cikin kunnensa yafi komai ɗaga masa hankali, kwanciya yayi lamo akan gado yayinda yake ƙwato numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwace masa da ƙyar. wani irin fusga numfashinsa yayi lokaci ɗaya kuma komai najikinsa ya sake…
Zahrah kuwa zazzaɓine ya dirarmata me zafin gaske, wanda yasanya lokaci ɗaya jikinta yasoma ɓari ta fara rawan ɗari, har zuwa yanzu hawayenta bai tsaya ba. Zaid ya cuceta itakam duk irin ƙuncin daya jefata a baya bai ishe saba saida yakuma da wowa gareta, sai yaushene hawayenta zasu tsaya? sai yaushene zata samu farinciki ingantacce wanda babu algus acikinsa? tunda ta haɗu da Zaid ƙuncin rayuwarta yasoma, wani irin annoba Zaid yazame mata ne?…..
(Kuyi haƙuri kuyi manage da wan nan, headache ke damuna, nida Zaid duk cutarmu ɗaya???? banyi posting da wuri ba wlh network ɗin sim ɗi nane gaba ɗaya ya ɗauke????)
29/December/2019
Follow me on Whatsapp and Wattpad
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
(????Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareku my wattpadi’ans inagodiya sosai a gareku????)
Editing is not allowed????
CHAPTER 72 to 73
Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haɗe da ɓata fuskarta duk wai akan don Mom ɗinsu tace taƙira mata Zaid a ɓangarensa ne yasa take wan nan abun…
“Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki ƙiramin yayanki ba!” Mom tafaɗi haka cike da faɗa, ganin Labisat ɗin bata da niyar zuwa aiken datayi mata.
“Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!” Labisat tafaɗi haka cikin shagwaɓa.
Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon…
Aranta kuwa roƙon Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faɗa baya masa kaɗan ko kaɗan, jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haɗata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya????)
Kusan sau huɗu Labisat tana knocking ƙofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura ƙofar tashiga,, bakowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshinsa dake tashi.. Direct ƙofar bedroom ɗinsa tanufa haɗe da soma knocking ƙofar,, jin shiru ne yasanya tashiga ƙiran sunan sa…
“Brother! Brother!” ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin ɗakin ko baya ciki ba..
Gajiya tayi da knocking ƙofar ta juya tayi tafiyarta…
“Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door ɗinsa amma bai amsa ba”
“Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita ba, miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin ƙyaliya ba” Mom tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take..
Itama ɗin de knocking tayi masa haɗe da ƙiran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta kutsa kanta ciki bakinta ɗauke da sallama..
Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..
“Zaid!” taƙira sunansa cikin kakkausar murya… Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..
Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma’abocin yawan bacci ba’a bisa ƙa’ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa ɗayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan ƙwayoyi, “Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?” tajeromawa kanta waƴan nan tambayoyin, “Haƙiƙa Zaid ɗanta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa ƙa burgesa ba yanada wani shegen shu’umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi”…
A hankali tashiga takawa zuwa gaban gadon nasa..
Idanu Mom tasake warowa waje, tabbas idan de idanunta de de suka gane mata to kuwa Zaid baya numfashi, domin babu wata alamar da take nuna akwai nunfashi a tattare dashi saboda ko cikin sa baya motsawa, alama ta baya shaƙan numfashi kenan..
Hanunta takai setin hancinsa ko da zataji ɗumin numfashin sa.
Salati Mom tasa haɗe da dafe ƙirjinta, sakamakon wani irin bugawa da taji zuciyarta tayi.
“Zaid!Zaid!” Mom tashiga ƙiran sunansa cikin tashin hankali haɗe da soma jijjigasa.
Hawayene suka shiga bin ƙuncin Mom bashiri ta fita daga ɗakin, direct ɓangaren Alhaji Ma’aruf ta nufa saboda yana gida baikai ga fita office ba..
“Alhaji! Alhaji! katemaka wlhy Zaid baya numfashi zo muje ka gani, katemakeni kada na rasa ɗana mafi soyuwa a gareni!!” gaba ɗaya cikin tashin hankali Mom keyimawa Dad bayani..
Mamaki haɗi da al’ajabi ne yakama Alhaji Ma’aruf amma de yanzu balokacin tambaya bane gwamma yabita yaga meke faruwa da Zaid ɗin….
Shima sosai ya tsorita kuma hankalinsa yatashi daganin Zaid yashe a gado baya numfashi sai kace gawa…
Da ƙyar Abba ya’iya sungumarsa yasanyasa a mota, abunka da ƙaƙƙarfa kuma ma’abocin yin gym shiasa jikinsa yake ko ina a murɗe, san nan kuma me ƙaramin ƙarfi bazai iya ɗaga sa ba, Dad ɗin ma saida temakon Mom ya iya ɗagasa… Daga Mom har Labisat hankalinsu amatuƙar tashe yake haka suka shiga mota suka rankaya zuwa asibiti…