NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Direct Emergency  aka kai Zaid cikin gaggawa likitoti suka shiga basa temakon gaggawa…

Jigum jigum haka Abba da Mom sukayi a wani ɗan corridor dake kusa da ɗakin da aka kai Zaid, iya ƙololuwar tashin hankali sun shigesa, kuka kawai Mom da Labisat keyi, kasa koda rarrashinsu Alhaji Ma’aruf yayi domin shima da akwai hali da kukan ze sanya ko da zaiji sassauci a cikin zuciyarsa…

Likitotin nan sunci baƙar wahala kafun da taimakon Allah suka samu suka daidai ta numfashin Zaid. Haka suka fito suna sharce gumi….   Kallon Alhaji Ma’aruf ɗaya daga cikin Doctors ɗin yayi haɗe da cewa “Ranka ya daɗe muje office”    ƙoƙarin binsu Mom tasomayi Alhaji Ma’aruf yaɗaga mata hanu alamar tajirasu….

Handkerchief likitan nan yaɗauka ya ƙare share gumin dake tsatstsafawo akan goshin sa..
Ganin haka yasa Abba cike da tashin hankali yace “Yade Dr.Bilal meke faruwa ne, dan Allah kada kafaɗamin wani mummunan labari!”

Jinjina kai Dr.Bilal yayi haɗe da kallon Dad.  “Kwakwantar da hankalinka Alhaji zuwa yanzu komai ya daidaita munshawo kan matsalan”

Nannauyar ajiyar zuciya Dad yasauƙe haɗe dayin hamdala acikin ransa…

Sake gyara zama Dr.Bilal yayi haɗi da cewa “Sai de kuma agaskia bazan ɓoye maka ba Alhaji ɗan ka yana cikin matsala wanda yake gab da rasa rayuwarsa matuƙar baikiyayewa kansa shan ƙwayoyi masu mugun haɗari ba, baya ga haka kuma idan har ya cigaba dashan giya  nan da ƴan kwanaki tofa sai de kuma abun da Allah yayi!”

Yanzukam Dad ne yashare gumi ba Dr.Bilal ba, domin kuwa a iya tsawon rayuwarsa baitaɓa sanin Zaid nashan wasu ƙwayoyi masu bugarwa ba,  yade san da ya nashan giya amma kuma atunaninsa yajima da dena shan giyan.

“Bangama fahimtarka ba likita, naji kace ƙwayoyi na bugarwa, kana nufin shiɗin ne yakeshan ƙwayoyin bugarwa?” Dad yatambayi Dr.Bilal cike da son sanin ƙarin haske akan batun..

“Wato a iya bincikenmu mungano cewa akwai wata ƙwaya me haɗarin gaske da yakesha lokaci zuwa lokaci, wanda kuma haɗarin ƙwayar yana da matuƙar yawa,  bazanyi mamakin a ina yasamu ƙwayan ba, saboda nasan shiɗin isashshene, saboda ƙwayar ba ako ina ake samunta ba, a ƙa’ida ma anhana shigo da ƙwayar nan gida Nigeria, kawai de rayuwar yanzune  da ta zama sai a hankali, zai iya yuwuwa kuma ba anan yake sayan ƙwayan ba daga can waje yake shigowa da abarsa, sai de kuma wan nan duk bashine damuwar ba, idan har ya cigaba da shan wan nan ƙwaya to ina me tabbatar maka da cewa zai iya rasa ransa ako da yaushe, duk da kuwa dama munsan mutuwa tana kan kowa yanzu ko anjima, amma tabbas kiyayewan shine yafi, san nan kuma giya tayi masa mummunan illa saboda tasamu mafaka acikin cikinsa, wataƙila yamai da ita ruwan shansa ne, amma kuma duk hakan ba wani babban matsala bane idan har ze kiyaye to da taimakon Allah komai zezo masa cikin sauƙi!”

Salati Alhaji Ma’aruf yayi a bayyane haɗe da sanya hanu yazame hular dake kansa,  ashe bayan giya hadda wata tsinanniyar ƙwaya me haɗari Zaid yake sha? anya kuwa Zaid yanada cikakken hankali? shin wani irin haline haka da Zaid? amma babban abun tambayar shine laifin waye acikinsu, laifinsune su iyayensa kokuwa laifinsa ne shi kansa Zaid ɗin?

“Haƙiƙa dukansu suna da laifi, amatsayinsu na iyaye basu wani tsaya sunbawa Zaid kyakkyawar kulawa ba, kuɗi kawai suka sake masa haɗe da turasa makaranta har wata uwa duniya, amma duk da haka bekamata ace yakasance haka ba, idan su basa lura da al’amuransa shi ɗin mahaukaci ne da be san dede ba?   tabbas yasan shiyake da alhakin kulawa da tarbiyan Zaid tunda shine yaɗaukosa daga wajen Mahaifiyarsa yadawo dashi  America kusa dashi,  tunda suke America bai taɓa tsayawa da kyau yakula da wani irin rayuwa Zaid ɗin keyi ba, shide kawai yabuɗe masa bakin aljihu yana ganin hakan shine gata,  ƙwarai mafiyawancin iyaye ayanzu sunfi bada kulawarsune ga Ƴaƴa mata, yayinda ƴaƴansu maza kuwa ko oho, duk wata kyakkyawar tarbiya Ƴaƴa mata ake ƙoƙarin koyawa, yayinda Ƴaƴa maza kuwa suka zama hoto, aganin iyaye komiye ɗa namiji yayi adone bakamar ƴa mace ba, tabbas hakane duk abun da ɗa namiji yayi adone bakamar mace ba, amma hakan bawai yananufin shi ɗa namiji abarsa sakaka haka bane batare da annuna masa kulawa ba,  shi namiji a koda yaushe ana ganin zai iya kula da kansa, amma yana da kyau ana nuna masa kulawa ana kuma jansa ajiki kodan yasamu inda zena faɗan damuwarsa, kowafa yanason yasamu tarbiya me kyau daga Namiji har mace, saboda haka yazama lalle iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ƴaƴansu maza saboda ba mata ne kaɗai suke buƙatan kulawa ba harsuma maza suna buƙata……

Dr.Bilal ne yakatse Dad daga tunanin da yafaɗa me zurfi tahanyar cewa da yayi dashi.    “Zaid yana buƙatar hutu saboda haka sai nan da 4 hours kafun su samu ganinsa”

Jiki ba ƙwari haka Dad yafito daga office ɗin  yanufo inda su Mom ke tsaye suna sharce hawaye..

“Yaya de Alhaji me likitan yacema?” Mom tatambaya cike da damuwar son sanin wani hali ɗanta yake ciki..

“Kada kidamu, ku kwantar da hankalinku jikinsa da sauƙi zuwa anjima kuma insha Allah zamu samu ganinsa yanzu likita yace yana buƙatar hutu ne, to dole zamu barsa yaɗan huta” Dad yaƙare maganar yana me kamo duka hannayen mom alamun rarrashi..
Hamdala Mom tayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya

Sake kallon Dad tayi cikin yanayi na tuhuma tace “Meyasanya naga fuskarka ɗauke da tashin hankali me tsanani Alhaji?”

Murmushin dole Dad yanemo ya ara akan fuskarsa bayason faɗa mata wan nan maganar yanzu yafiso saisun samu nutsuwa sunkoma gida tukunna, sai de kuma abun da shi besani ba shine tafikowa sanin cewa Zaid yanashan giya, saboda tasha kamasa acikin maye yayi mankas, san nan kuma tajima da sanin cewa yanashan ƙwayoyi, sede abun da bata sani ba shine haɗarin da ƙwayoyin suke ɗauke dashi….


Haka Zahrah tawayi gari yau da zazzaɓi sede duk da haka bata nunawa kowa cewa bata da lafiya ba, sede kuma idanunta sun kunbura sakamakon kukan da taci ta ƙoshi a daren jiya..
Haka de tashirya kanta tsab don zuwa makaranta amma kowa yaganta yasan bata da wani isashshen kuzari a tattare da’ita,, ko abun kari bata tsaya taci ba haka ta fice a gidan nasu….


“Kuka bazai taɓa yimiki maganin komai ba Zahrah, tabbas nasan kinajin raɗaɗi a cikin zuciyarki amma zuwa yanzu yakamata ace kimanta da baya kifuskanci gaba,   aure zakiyi  yanzu babu amfani kicigaba da sanya kanki cikin ƙunci!” Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cikin yanayi na tausasawa, kasancewar duk wunin yau ɗin da sukayi amakaranta bata gane kan ƙawarta ta ba…

Hannayen Husnah duka Zahrah takama haɗe da kallonta.  Cikin murya me rauni tasoma cewa…..

“Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuƙar Zaid yana raye a doron ƙasa,  koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa  akwai wani namiji da zaiyi ɗokina idan ya aureni?  Shifa budurci wani abune me matuƙar mahaimmanci a rayuwar ƴa mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta ɗakin mijinta,  mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani  kyautar budurcinta,   mata irina suna da yawa Husnah wa ƴanda aka mawa fyaɗe aka ƙwaci budurcinsu da ƙarfin tsiya, san nan kuma akwai waƴanda maza suke ruɗansu da kuɗi ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu,  san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin  ga wani daban,   rasa budurci abune me matuƙar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaɗe, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure  su samu matansu  da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta,  haƙiƙa akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuƙar takawomasa  budurcinta ɗakinsa, saɓanin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure’nta, koda ace ya yarda ƙaddarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saɓanin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haƙƙinsa na aure,,   wan nan ranan nake gujewa kaina  Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!” gaba ɗaya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar ƙaddara wand ba’a taɓa mantawa da’ita,,  rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin ƙawarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaɗa gaskiya ne kai budurci ɗakin miji yafi komai daɗi a rayuwa saboda ko ba komai zaiƙara muku danƙon soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba’asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faɗa hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa ƙaddararsa…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button