SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau tunsafe Zahrah tashiga busy hidama kawai sukeyi ita da Husnah domin kuwa yaune ranar da Dr.Sadeeq yace mata za’a kawo lefenta,, yanzuma daga shopping suke sunje sun sayo kayan drinks da kuma su snacks wanda za’abawa baƙi. Zama sukayi akan tabarma suna me da numfashi saboda sungaji sosai,,, kallon Zahrah Husnah tayi haɗe da sakin murmushi.
“Ƙawata nifa yau daɗi nakeji jinake tamkar ma nice za’a kawowa lefen” dariya Zahrah tayi haɗe dacewa “To aike kince bayanzu zakiyi aure ba saikin gama school gashi Nuruddeen yana tsananin son kuyi aure amma ke kinƙi”
“Hmm ai zan masa maganane yaturo kawai domin ni mafa yanzu dagaske auren nakeso nagaji da rungumar pillow idan nazo bacci” Dariya suka sanya su dukansu hadda tafawa, “Allah yashiryeki Husnah” Zahrah tafaɗa tana dariya.. Haka de sukaci gaba da ƴan hirarrakinsu irin na ƙawaye……….
Ƙarfe biyar dai dai wasu rantsa rantsan motoci suka soma tsayuwa a ƙofar gidan su Zahrah duk macen da tafito acikin motar sai kaga tana yatsuna fuska haɗe da soma ƙarewa wajen gidansu Zahrah kallo, motocine kusan guda goma sha biyu suka kawo kayan lefen ahankali aka shiga fito da akwatuna ana shiga dashi cikin gidan su Zahrah.. Fuska babu yabo ba fallasa haka matan nan suka soma shiga cikin gidansu Zahrah,,,,, da fari’a Inna da tawagarta suka tarɓi mutanen haɗe da basu wajen zama, haka suka zauna wasu daga cikinsu suna yatsuna fuska kamar wanda akace su zauna akan kashi…
“Sannunku da zuwa lale marhaba” Wata mata maƙociyar su Zahrah tafaɗa ga matan da suka kawo lefen. Amma kuma daƙyar aka samu biyu daga cikinsu suka amsa mata..
Akwatuna ne harguda shabiyu aka jibge akan wata tabarma dake shimfuɗe,, su Inna ne suka fara ɗagawa matan da suka kawo lefen gaisuwa ciki ciki suka amsa musu cike da isa,,,,, Aunty Raliya ce ma tayi ƙarfin halin cewa “Ga kayanan munkawo Allah yasa ayi bikin a sa’a, Allah kuma yasa asamu kyakkyawar zuri’a” dagajin yanda tayi maganar kaɗai ya isa ya tabbatarmaka cewa kalaman ba anyi su bane cikin daɗin rai,,, da Ameen kawai su Inna suka amsa musu,,, kuɗi Aunty Raliya taciro acikin jakarta bandir ɗin ƴan dubu dubu har na dubu ɗari ta ɗaura akan wani akwati haɗe da kallon ƴan uwanta tace “Muje ko” dukansu miƙewa sukayi suka nufi hanyar waje,,, yayinda Inna tasa yaran maƙotansu suka kwashi kayan tarban baƙin da suka musu aka kai musu cikin mota, maman Badi’a ɗaya daga cikin maƙotan su Zahrah ita tazari dubu hamsin daga cikin kuɗin da suka aje tabawa ƴarta Badi’a tace takaiwa matan dasuka kawo lefen,,, dawowa da kuɗin Badi’a tayi tace ae sun riga da sun tafi koda tafita ƙurar motarsu kawai tagani,,, “To suko wasu irin mutanene haka ae ba haka akeyi ba, ko fa kayan basu tsaya sun nuna mana ba saikace wanda suke akan ƙaya” Maman Badi’a tafaɗi haka cike da mamakin hali irin na matan da suka kawo lefen,,, washe da baki wata mata daga cikin gayyar Inna tace “Kai amma kuwa Zahrah tayi goshi kuga kayafa kamar wanda za a buɗe kanti” ae kuwa basusan cewa Zahrah tayi goshi ba saida suka soma buɗe akwatunan,, kowanni akwati shaƙe yake da kaya nagani na faɗa,, take Inna tasoma rangaɗa guɗa hadda rawan murna…….
(Team Dr.Sadeeq da Zahrah saiku wanke ƙafa don zuwa gano kayan lefen Zahrah????)
31/December/2019
Follow me on Whatsapp and Wattpad
Wattpad user name fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
(Kutayani jaje wlh sau biyu kenan typing ɗina yana gogewa???????? yanzu saida nayi 2000 words wlh ya kuma gogewa maganan danake wlh yanzu haka ina rubutun nan ina kuka???????? wlh abun da ciwo sosai????????)
CHAPTER 74 to 75
Hayaniya haɗi da guɗan da su Inna keyi shiyayi sanadiyar janyo hankalin Zahrah dakuma Husnah da suke zaune a ɗakin Zahrah sunyi muƙus,,,,
“Ke nifa tashi zanyi naje nabawa idanuna abinci, dan wlh bazan iya zama aɗaki kamar wata sabuwar amarya ba, ke dai da zaman yazamemiki dole saiki ta fama” Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take,,, murmushi kawai Zahrah tayi mata haɗe da binta da kallo hartafice daga cikin ɗakin…
Hamdala Husnah tayi haɗe da nunatsantsar farincikinta alokacin da idanunta sukai mata tozali da kayan lefen ƙawartata,,,, lallai Dr.Sadeeq yayi ƙoƙari domin kuwa naira tayi kuka, koda kyawun akwatunan aka barka sun isa sanyaya maka rai, balle kuma aje ga kayan ciki masu kyau da tsadar gaske, wan nan shiyasake tabbatar mata da cewa Zahrah bazatayi kuka ba idan ta auri Dr.Sadeeq, saboda me sonkane kaɗai zai iyayin komai dayasan zai faranta maka rai….
Duk yawan atamfofin dake cikin akwatunan nan saida su Inna suka irgesu kaf, turame hamsin banda su laces haɗi da shaddodi dakuma dangin su materials,, ɓangaren dogin riguna ma akwati guda aka cika dasu, sosai kuma yasaki bakin aljihunsa wajen zaɓo masu kyau da tsada,, haka ɓangaren sarƙokima komai yaji domin kuwa kaf cikin sarƙoƙi da ɗan kunnayenta babu wani mai sauƙin kuɗi acikinsu gwala gwalanta har guda uku,, san nan kuma ɓanagaren jaka da takalma ma yayi ƙoƙari sosai, domin kuwa kusan kowani kaya yanada jaka da takalmi hadda mayafinsa,, wajen kayan shafa ma yayi ƙoƙari sosai wajen fidda naira yasai kayan shafa ƴan yayi masu kyau duk da kuwa yasan cewa ita ba gwanar kwalliyan fuska bace…
“Gaskiya kaya yayi kyau yarinya tayi goshi, ai wan nan kayan ko ɗiyar babban attijiri sai haka” Maman Badi’a tafaɗi haka bayan taƙarewa wani haɗaɗɗen leshi dake riƙe a hanunta kallo wanda a ƙalla kuɗinsa zai kai 50k,,,
“Ƙwarai kuwa yarinya tayi goshi Maman Badi’a ai dama tuntuni nasan fiye da haka ma sai yafaru, ga kaya kan nan harda nasadakarwa!” Inna tafaɗi haka cikin murna…
Wata dake zaune kusa da Inna tace “wan nan haka yake muma dai Allah yabawa namu ƴaƴan mazajen aure masu ƙashin arziki”
Duka matan suka haɗa baki wajen cewa Ameen domin kuwa babu wacce zataƙi ace ƴarta ce tasamu wan nan kayan more rayuwan….
Sai kusan magriba matan dasuka karɓi lefen Zahrah suka soma tafiya, bayan Inna ta yaga musu wani abu daga cikin dubu hamsin ɗin daya rage,, haka suka tafi suna mata godiya suna kuma zuba santin kayan domin kuwa koda maƙiyin Zahrah ne yaga wan nan uban kaya da Dr.Sadeeq yayi mata tabbas dole sai ya jinjina abun…..
Lokacin da Zahrah taga irin yawan kayan lefen da Dr yayi mata kasacewa komai tayi, sosai abun yabata mamaki domin kuwa bata taɓa zaton zai ɓarnata dukiya mai yawa harhaka wajen yi mata lefe ba, bayan kuma yasan cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace,,, sai de taƙudura aranta cewa zata faɗa masa kayan sunyi yawa……