NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Gidansu Doctor…

“Gaskiya da sake Hajiya, yakamata a dakatar da wan nan batun auren na Sadeeq da yarinyar nan,  kinkuwa ga gidansu Hajiya? wlhy ko suminti babu a tsakar gidansu zallan turbuɗin yashine, kallo ɗaya zakai musu kafuskanci cewa suɗin faƙara’une basu da komai, kwata kwata ma Sadeeq baisan inda zaije ya nemo aure ba domin a wan nan gidan bana tunanin akwai wata halitta da zata burge wani ɗa namiji acikinsa, kawai dai ni inaga ma asiri sukayi masa wlhy, amma bacin haka banjin dakansa zaije neman aure wan nan gidan!” Auntie Raliya ce ke faɗan haka cikin ɓacin rai…..

Ajiyar zuciya Hajiya tayi cikin ɗacin rai tace  “Hmmm Raliya kenan aeni ban isa hana wan nan auren ba ko kinmanta cewa har ƙarana wajen Baffan ku Sadeeq yakai akan naƙi amincewa da aurensa,  ni yanzu baruwana acikin lamarin aurensa ko mai ya jajiɓowa kansa shiya sani”

Ƙwafa Auntie Raliya tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin Hajiyar, harga Allah ita sam batason wan nan auren da Sadeeq zaiyi, yarasa ma wacce zai kwaso musu sai wacce wani ya haiƙewa a waje san nan kuma ƴar talakawa futuk…

Auntie Raliya tana fita falo ƙawayenta da ta gaiyato suka kai lefe  tare, sukayi caaa akanta kowacce tana ingizata akan cewa tasa afasa auren domin kuwa sam ajin  Sadeeq  yagirmewa neman aure a wan nan gidan matsiyatan,,, take kuwa Auntie Raliya tahau kan zancen tazauna dabas, takuma ƙuduri aniyar lalata zancen auren abune me sauƙi kuma dakanta zataje ta kwaso kayan lefen ƙanin nata……..

Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da tunzuro ɗan ƙaramin bakinta gaba  cike da shagwaɓa tace “Dagaske nake faɗa maka kayan lefen nan sunyi yawa, ko ɗazu dawowan Baffa daya gani shima haka yace, kuma kafasan ba kyau yin wasa da dukiya” taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujeran motar dayake zaune akai kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, sautin muryarta nayi masa daɗi sosai…

Shirune yashiga tsakaninsu har na tsawon minti ɗaya.

“Duk abun da mayi miki kin can can ci haka daga gareni ne Zahrah, dan Allah kibar maganar yawan lefen nan, ni banga wani yawa da sukayi ba, naso ma nayi miki wanda yafi wan nan to abubuwane sukai min yawa, amma kin wuce haka a wajena, kuma kinsan ku biyu ne” yafaɗi haka yana me kafeta da idanunsa..

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sam bataso idan yana kallonta itama ta kalleshi saboda takanjin nauyinsa awasu lokutan,, amma kuma hakanan taji kalmar dayace su biyu ne yaɗan sosa mata rai,  wato idan ma ta manta to yatuna mata…

Wani murmushin Dr.Sadeeq yakumayi sakamakon ganin yanda fuskarta ya ɗan sauya lokaci ɗaya yakuma san maganarsa ce batai mata daɗi ba, dama kuma yafaɗi hakanne don yagane cewa tana kishinsa ne ko a’a….

“Bansan wani irin daɗi da kuma farinciki zan tsinci kaina ciki ba aduk sanda wannan ranar  taruskeni, amma kuma da zanfi kowa jin daɗi idan har Allah ya gwadamin wannan rana!” yafaɗi haka cikin shauƙi, dason kawar da wancen zancen nasu..

Cike da mamaki Zahrah taɗan saci kallonsa haɗi da cewa “Wace rana ce wan nan?”

“Ranar da zaki zamo mallakina, ranarda za’akawomin ke ɗakina amatsayin matata ta sunna, ranar da zan kwana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki babuko ƙyafta ido”

Kunyane yakama Zahrah wanda haryakaita ga cusa kanta  tsakankanun cinyoyinta, sautari Dr.Sadeeq yakan faɗi abubuwan da suke sanyawa takejin kunyarsa sosai…

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake kwantar da jikinsa akan kujeran motar,,,, yana matuƙar son komai na Zahrah ciki kuwa hadda wan nan kunyar nata, tun asalinsa yanason mace me kunya, sai gashi kuma yanzu Allah yabasa, sai de kuma yasan nan gaba kaɗan zaisha fama da’ita saboda idan sunyi aure yasan wan nan halin nata na kunya zatai ta gwadamasa.

Kallon agogon dake ɗaure a hanunsa na dama yayi.

“8:30pm” yafaɗa a bayyane  kana yadawo da kallonsa ga Zahrah wacce har yanzu bata ɗago kanta ba.

“Shikenan to tunda dai kunyana kikeji ni zantafi naga dare yasoma yi” yafaɗi haka adai dai lokacin da yake ƙoƙarin  ɗaura sit belt ajikinsa..

Sai alokacin taɗago kanta amma bata yadda ta kallesa ba,, “Sai da safe” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin fita daga cikin motar domin dama taƙosa yace mata zaitafi saboda tagaji da zaman motan gashi tana da assigment kuma gobe zasuyi submit ɗinshi, san nan kuma tana buƙatar kasancewa ita kaɗai domin tattaunawa da zuciyarta a game da sabon al’amarin dayake shirin kunnu mata kai….

Kansa yajinjina haɗe da cewa “Dama so kike natafi ko?”

Murmushi tayi masa kana taɗan  girgiza kan ta alamar a’a, cikin murya me sanyi tace “Bahaka bane kawai de nafara jin bacci ne”

Kansa yakuma jinjinawa cike da gamsuwa  haɗe da juyawa baya yaɗauƙo wata farar leda dake aje kan kujeran gidan baya na motar.

“Idan Allah yakaimu da safe zanƙiraki ina fata zakiyi bacci me daɗi” yafaɗi maganar yana me miƙomata ledan dake riƙe a hanunsa…

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da marairaice manya manyan idanunta da suke sauƙar masa da kasala aduk sanda ya kallesu,,   “Gaskiya ni dai a’a nagaji da wayon da kakemin, kuma tun ba yauba na faɗa ma hidiman dakakemin yana yawa!”

Lumshe idanunsa yayi  haɗi da buɗesu alokaci guda, idan yanaganin irin wan nan shagwaɓan nata to tabbas zata iya zautar dashi lokaci ɗaya, yafice a hayyacinsa, domin shi shagwaɓan mace nasanyawa yaji feeling ajikinsa sosai,, cikin murya me sanyi yace “Kiyi haƙuri  ki ƙarɓa kinji princess ɗina, kinga ba kyu maida hanun kyauta baya!”

Sake turo baki tayi haɗe da kwaɓe fuska,    abun mamaki sai taga shima ya marairaice mata fuska kamar wani ƙaramin yaro,,  “Please!” yafaɗa cikin muryarsa da tayi ƙasa sosai..

Dole babu yanda ta’iya haka tasanya hanu takarɓi ledan haɗe dayi masa saida safe tafice daga cikin motar,,,  yanaganin shigewarta cikin gida yasaki murmushi haɗe da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan ƙuncinsa,  key yayi mawa motar haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu.    Yana tuƙi amma shikaɗai yaketa zuba murmushi, aduk sanda yake tare da Zahrah yakansamun kansa cikin farinciki da nishaɗi, tabbas yanayimawa Zahrah so me tsanani…..

Zahrah kuwa tana shiga cikin gida direct wajen da Inna ke zaune tanufa,  ƙoƙarin zama tasomayi haɗi dayimawa Inna sannu da gida.

Washe da baki Inna ta amsa mata bayan ta kafe Zahrah da’ido, Allah Allah take taga menene acikin ledan da  Zahrah ta shigo dashi..

Dariyane ya ƙwace mawa Zahrah sakamakon ganin yanda Inna ta tsareta da’idanu tamkar wata mayya.

“Dariyan uban me kike? banson shashanci wallahi” Inna tafaɗi haka ga Zahrah a hasale, ganin bata da shirin buɗe ledan…

Hannayenta tasanya ta toshe bakinta haɗe dasoma ƙoƙarin shanye dariyar ta.

Ledan da tashigo dashi ta buɗe tasoma dubawa gasassun kajine manya guda biyu sai kuma sauran kayan ciye ciye kamar su snacks dakuma chocolate,,
Ledan da kajin ke ciki ta ciro ta miƙamawa Inna ae kuwa hanun Inna har rawa yake lokacin da tazo karɓan ledan tsabar kwaɗayi.

Fari’ar Inna ne yasake yawaita sakamakon ganin kaji da tayi, babu wani ɓata lokaci ta yago cinyar kaza ɗaya takai bakinta,, tsabar daɗin kazar saiga Inna tana lumshe idanu haɗi da jijjiga kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button