NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da ɗaukan sauran kayan tawuce ɗakinta yayinda tabar Inna tayi pieces  tana cin kaza hadda rausayar da kai gefe alamar daɗinta takeji….

Jigum tayi haɗe da sake takurewa  waje ɗaya akan ƴar katifartata,,,  tabbas Dr.Sadeeq yacancanci ta sadaukar masa da duka soyayyarta ko dan saboda halaccin da yayi mata a rayuwa, bazatace batasan menene so ba, itacema zata ba da labari akan so, domin ta ɗanɗana zafinsa me matuƙar ɗaci da dafi,,   idan tace Dr.Sadeeq baya burgeta tayi ƙarya, haka kuma idan tace Dr.Sadeeq baida abubuwan burgewa ajikinsa da zasu sa mace tasosa nan ma tayi ƙarya? tabbas Dr.Sadeeq baida wani makusa daga halayya ɗabi’a harma da surarsa yacika cikakken namiji, amma babban abun dake damunta shine batajin tsananin soyayyarsa acikin zuciyarta, bawai tana ƙinsa bane, kawai de zafin soyayyar tasa ne bataji a jiki da zuciyarta, ba kamar yanda taji na Zaid ba,, ada batajin soyayyar Dr.Sadeeq acikin zuciyarta amma ayanzu tayi ƙoƙari wajen ganin takoyawa zuciyarta sonsa,  takuma yarda cewa zata iya zaman aure dashi domin baida wani makusa  atattare dashi wanda zaisa a ƙisa, murmushine yasuɓuce mata sakamakon tunowa da tayi da irin kallon dayakeyi mata ɗazu, tabbas ya iya nuna soyayyarsa a fili, abu ɗaya ne ajikinsa wanda yake ɗaukar hankalinta,  shine ƙwayar idanunsa, duk da cewa shi ɗin namiji ne amma yanada idanu masu kyau wanda zasu sanya maka nutsuwa aduk sanda ka kallesu, hakan yasa ako da yaushe takeson kallon cikin idanunsa amma bata iyawa saboda kunya….. Tunanin Zaid ne yakutso kansa cikin zuciyarta harsai da taji faɗuwar gaba,,    “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” shine abun da tashiga nanatawa acikin zuciyarta,, wannan wani irin bala’i ne? tunda Zaid yashigo cikin rayuwarta shikenan kuma komai nata ya ruguje, lallai itakam taɗaukeshi amatsayin annoba wanda gani da jinsa babu alkhairi …..

Yau Kwanansa ɗaya da wuni ɗaya cur baisanya ko wani irin abinci abakinsa ba, sai ruwan giya dayake ta kwankwaɗa ba dare ba rana,, damuwa ce tayi masa mugun yawa abubuwa gaba ɗaya sun caɓemasa,    kallo ɗaya zakai masa kafuskanci cewa yanacikin halin damuwa, domin kuwa lokaci ɗaya ya zabge rama ta bayyana kanta ajikinsa, yayinda manya manyan idanunsa suka sake fitowa waje,,    wani irin zafi zuciyarsa keyi masa, baisan da yaushene kuma ta yaya yakamu da soyayyar Zahrah me tsanani haka ba,     tunjiya yarasa nutsuwarsa a sakamon labari dayaji daga bakin wanda yasanya  yana kulamasa da shiga da ficen   Zahrah,  inda yasanar masa cewa ankawowa Zahrah kayan lefe, iya ƙololuwar tashin hankali Zaid yashiga dajin wannan magana, sam be shirya wa rasa Zahrah ba saboda rasata dai dai yake da rasa rayuwarsa gaba ɗaya, akuma yanda yakejin matsanancin sonta a cikin zuciyarsa zai iya sadaukar da komai nasa gareta, ko da kuwa ransa ne…

Yanzuma zaune yake yatusa wani ƙaton hoton zanen fuskarta daya zana a daren jiya a gaba yana kallo, saboda tsabar kyawun da zanen yayi idan kagani bazamakace zane bane…

Idanunsa dake kan idanunta na cikin zanen ne suka kaɗa sukai jajur dasu.  Saiyanzu yakejin tsanar kansa dakuma tsanar wannan banzan halin nasa, sai yanzu yake tsananin danasanin abun daya aikatawa Zahrah, haƙiƙa yasan cewa ya zalunci Zahrah ya cutar da’ita ya lalata mata rayuwa, kuma hakan da yayi mata shiya nisan ta masa ita, wani irin tsana ne Zahrah tayi masa haka? shin tasan irin zafi dakuma raɗaɗin dayakeji akanta kuwa? yadaina cin abinci tasanadiyar ta, wannan yasa  ulcer tayi masa mummunan kamu, gakuma soyayyarta da ta sanya masa ciwo a zuciya,, ta wani ɓangare kuma yana fama da wani  matsanancin ciwon kai wanda dashi yake kwana yake kuma tashi, cikinsa kuwa tamkar anhura masa wuta haka yakeji aciki,, hanu yasanya yashafi zanen fuskartata, tabbas idan baisamu Zahrah ba bazai taɓa iya cigaba da rayuwa ba,,, abun da Zaid baisani ba shine tuni  ruwan hawaye sun cika idanunsa gangarowa kan fuskarsane kawai da basuyi ba,  zumbur haka yamiƙe tsaye haɗe da zura silifas ɗinsa ko wayoyinsa bai tsaya ɗauka ba, haka yafice daga cikin ɗakin nasa….

Yana fita compound ɗin gidan nasu driver’n sa yaƙaraso garesa da sauri,,,, “Oga fita zamuyi ne?” driver’n yatambaya cike da girmamawa,,  kai kawai Zaid ya ɗaga masa alamar “eh”    jikin driver’n na rawa yace “Oga da wacce motar zamu fita?”

Cike da ƙosawa Zaid yace “Kowacce”

Driver yayi mamaki sosai dajin maganar Zaid domin yasan idan dai har fita Zaid ɗin zaiyi to sai yazaɓi motar dayakeso amma kuma sai gashi yau yace kowacce..   Wata haɗaɗɗiyar baƙar benz driver’n yatuƙo daga cikin parking space zuwa inda Zaid ke tsaye ya harɗe hannayensa acikin  aljihun wandon track suit ɗin dake jikinsa..

Zaid nashiga cikin motar driver yabawa motar wuta yayinda me gadi ya wangale musu gate suka fice daga cikin gidan…..

Baffa ne zaune akan dakalin ƙofar gidan yana me latsa ƴar ƙaramar wayarsa, zaman da yayi Zahrah yake jira ta dawo daga aiken da yayi mata,, daf dashi motar tayi parking, hakan yasa Baffa  ya kafe motar da’ido don ganin wanene zai fito daga ciki…

A hankali Zaid yabuɗe murfin motar yafito, kallonsa Baffa yashigayi daga sama har ƙasa saboda sarai yagane shine  ɗan iskan me kuɗin da yamawa Zahrah fyaɗe,  saida Baffa yagama ƙaremasa kallo kafun yakawar da kansa gefe…

Da sallama Zaid yaƙarasa wajen Baffa,, ciki ciki Baffa ya amsa masa sallaman,    durƙusawa Zaid yayi haɗe dayin ƙasa da kansa cikin murya me sanyi yace “Kagafarceni Baffa, nasan ban kyautaba amma dan Allah kada ka hanani auren Zahrah, wallahi a yanda nakeji idan bansamu Zahrah ba mutuwa zanyi!”

Baki Baffa yasake yana kallon Zaid,  namiji har namiji amma wai yana cewa idan bai auri Zahrah ba mutuwa zaiyi kuji iskanci fa,,
Sake ɗago kansa Zaid yayi haɗe da watsawa Baffa jajayen idanunsa,   “Wlh Baffa yanzu da gaske nake aurenta zanyi, kada kace zaka hanani ita dan Allah, wallahi Zahrah tana da matuƙar mahimmanci acikin rayuwata!”

Yanzukam kallon tsab Baffa yashiga yi masa saida yaɗauki kusan minti biyu yana kallon Zaid ɗin kafun yaɗan nisa haɗe da cewa “Bantaɓa tunanin kana da idanun da zaka dawo ka kallemuba, amma sai gashi kadawo kana kallona har kuma kana roƙona dana baka auren Zahrah, idan da kanasonta tunfarko mai yasa baka aureta ba kalalata mata rayuwa? ni bazance maka komai ba saide ince munbarka da Allah saboda bamu da yanda zamuyi dakai, amma kuma kasani bazan baka auren Zahrah ba harsai da amincewarta, idan har tace ta amince zata aureka shikenan nime iya baka aurenta ne” Baffa yana kaiwa nan a zancensa yatashi yayi shigewarsa cikin gida.. Da ƙyar Zaid ya’iya tashi ya  zauna akan dakalin da Baffa yatashi hannayensa duka biyu yasanya ya dafe kansa dake yi masa nauyi kamar ze faɗo ƙasa…..

Da ɗan sauri take tafiya tana latsa wayanta burinta kawai shine taganta acikin gida, duk sanyin da akeyi yau yagama ratsata, saboda haka take Allah Allah ta’isa gida.. sam bata lura da akwai mutum a ƙofar gidan nasu ba dan hankalinta gaba ɗaya nakan wayartata…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button