NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

    *SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*

phatymasardauna
????Mrs Sardauna????

Dedicated To My Lovely Brother Khabeer

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
    *WATTPAD*

@fatymasardauna

Editing is not allowed ????

(kuyi haƙuri two days kunjini shiru, abubuwane sukai min yawa..)

Chapter 10 то 11

Zahrah ce kwance a ɗaki, bayan ta dawo daga aikan da Inna tayi mata,, zuciyarta cike take da saƙe saƙe kala kala, na farko tanason sanin wayeshi, maikuma yakawosa gidansu, haƙiƙa tasan cewa ya girmewa ajinta, amma sai gashi zuciyarta ta maƙale da tunaninsa, duk yanda taso manta shi a cikin zuciyarta hakan yagagara, amma cire tunaninsa acikin zuciyarta yazama dole, domin kuwa hanyar jirgi da ban, ta mota ma da ban,,,, a ranan nan da ƙyar bacci ɓarawo yayi awun gaba da Zahrah, dazaran ta kulle idanunta, kyakkyawan murmushin sa ne ke yi mata gizo….

Yau tana ƙirga wa kwanansa shida kenan dazuwa wajenta, amma har izuwa yau ɗin tunaninsa yakasa barinta tayi sukuni, bakomai yafi ɗaukar hankalinta a tattare da shiba kamar ƙawataccen murmushinsa mai burgewa, (Murmushin shu’umanci) uwa uba kwarjininsa yana ruɗata, wani irin son sake ganinsa takeyi…

A ɓangaren Zaid kuwa abubuwane sukai masa yawa, yayinda hankalinsa ya karkata zuwaga harkan kasuwancin sa, kwata kwata baya samun zama, amma komai yake Zahrah na maƙale a ransa, burinsa ɗaya shine Allah yakai damo ga harawa, ko baici ba yayi birgima, har ya hasasho, yanda zai keta mawa Zahrah rigar budurcinta, tun da yaganta yayi rantsuwa, cewa sai ya ɗanɗani zumanta, kuma bazai bar rantsuwarsa yatafi a banza ba…

Zahrah na zaune a tsakar gida, idanunta kekan handout ɗin dake riƙe a hanunta,, idan kayi mata kallon farko zakai zaton karatu takeyi, amma idan kakuma kallonta, to akasin haka zaka gani, domin gaba ɗaya hankali da tunanin ta ya tafi ga Zaid ya hanata sakat, karatun ma bako da yaushe yake shiga kanta ba,, wani yaro ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, Inna ce tayi saurin amsa masa, “Wai ana ƙiran Zahrah a waje ” yaron yafaɗa, baki Inna ta washe haɗe da cewa “ɗan albarkan nanne yazo na sani, je kace gatanan fitowa yanzu yanzun nan ” wani irin bugawa zuciyar Zahrah tayi, hakanan ta tsinci kanta da faɗuwar gaba, take kuma taji zuciyarta tayi sanyi,, lufayan da Inna ke miƙo mata ta amsa haɗe da zurawa ajikinta, kaitsaye tafice daga cikin gidan,,,
Tsaye yake a jikin motarsa yasha ado cikin wata blue shadda, sosai kayan yayi masa kyau, domin kuwa shiɗin ma ba baya bane wajen kyau,, turus haka Zahrah taja ta tsaya, ganin wata baƙuwar fuska ba wacce take tsammani ba,, murmushi yayi mata haɗe da yi mata nuni almar ta ƙaraso,, gaba ɗaya jitayi farincikinta ya gushe, sam bashi taso gani ba, taso ace Mai kyau (Zaid) ɗinta ta gani,, cikin sanyin jiki ta ƙaraso inda yake haɗe dayi masa sallama,, amsa sallamar nata yayi fuskarsa cike da fari’a,, sake gyara tsayuwa Jabeer yayi haɗe da cewa ” kiyi haƙuri a wancan lokacin na tsaidaki a’inda bai dace ba, amma yanzu gani nabiyoki har gida, ina fata zakiyi marhaba da zuwana “

Ɗan jim Zahrah tayi, domin ita bata da wani amsa da zata basa, ganin haka yasanya Jabeer ci gaba da cewa ” kamar yanda na faɗamiki a farko ni sunana Jabeer, ina zaune ne a unguwar asokoro nida mahaifana, ni ma aikacik banki ne,, tun daga randa na fara ganinki na ji na kamu da soyayyarki, idan har bazan takuraki ba inaso kibani dama don gwada sa’ata agareki… ” Jabeer yaƙare maganar yanamai kallon Zahrah, ɗan jim Zahrah tayi kamar wata mai nazari, ita dai batasan maizatace dashi ba, domin ita bata taɓa soyayya ba, kuma ita batama jisa acikin zuciyarta ba,,, ganin bazatace komai ba yasa Jabeer cigaba da yi mata bayanin kansa, haɗe da ƙoƙarin kafa gwamnatin sa wajen ta,, daga ƙarshe dai cewa tayi yabata dama tayi tunani,, yakoji daɗin hakan domin yanasa ran cewa zai samu karɓuwa a wajenta,,,, koda tazo tafiya maƙudan kuɗaɗe ya bata, amma sam Zahrah taƙi amsa, bayanda baiyi da’ita ba akan ta amsa amma taƙi, dole ya haƙura, saida yaga shigewarta gida kafun yayi mawa motarsa key yafice a unguwar tasu baki ɗaya……..

Zahrah nashiga gida Inna tayo kanta tana mai cewa ” Mai arzikin nan ne ko ? bansan a’ina kika samosa ba,amma gaskia banaso ya kuɓuce mana, saboda haka kiriƙesa da kyau “

cikin sanyin Murya Zahrah tace “Bashi bane Inna, wani ne daban” wata uwar harara Inna ta doka mawa Zahrah haɗe da cewa “to idan bashi bane wani ɗan iskan ne ? nifa kinganni nan banson harka da talakawa, domin a gaskia bazan ƙare rayuwata cikin talauci ba ehe, in ma baƙin ciki ne yasa kika kori mai arzikinnan to yazama dole ki bashi haƙuri ya dawo, kam bala’i ga samu gakuma rashi, ina bazai yi wuba, shi wannan ɗin a mai yazo ba dai a ƙafa ba ?”

“a mota” Zahrah tayi maganar kai tsaye, sam batajin daɗin abun da Inna keyi, shigewa ɗakinta tayi, yayinda tabar Inna tsaye tana faman ɓaɓatu ita kaɗai a tsakar gida….

Jigum tayi, zuciyarta cike da tarin tunani kala kala, “Bazai zo ba, dama nasan ya girmewa ajini, mai yasa nadamu dashi ? maiyasa nake yawan tunasa akowani lokaci ? maiyasa zuciyata keson jefa kanta inda bata dace da zuwa ba ? yazama dole na daina tunasa kwata kwata a rayuwata, to amma yazanyi da wannan daya kawomin tallen soyayarsa gareni ? ” Zahrah tayi maganar a fili,, haka dai Zahrah tayi ta saƙe saƙe acikin zuciyarta…

Bayan Kwana biyu da zuwan Jabeer….

Misalin ƙarfe 8:30 pm, Zahrah ce kwance akan ƴar yalolon katifarta, yayinda idanunta ke lumshe, da’alama bacci keson ɗaukarta…. Shigowar Inna da sauri cikin ɗakinnata shiya sanya tayi saurin buɗe idanuwanta, domin shigowar Inna ɗakinnata a dai dai wannan lokacin bainuna alamar lafiya…. ” Miye kika wani zura min idanu kamar mayya, tashi kije waje wannan mai arzikinne yakuma da wo wa ” Inna ta faɗa cike da zumuɗi,, dumm haka ƙirjin Zahrah ya buga,, ganin Zahrah tayi saƙare yasa Inna, cewa “zaki tashi kijene kokuwa saina mangareki ” sumi sumi Zahrah tamiƙe haɗe da ɗaukar hijabinta tana ƙoƙarin sanyawa a jikinta,, saurin fusge lufayar Inna tayi haɗe da wurgi dashi gefe, wani gyale dake hanunta, ta miƙomawa Zahrah’n haɗe da cewa ” ungo yafa wannan banson wannan shirmen koda yaushe kina nanuƙe da lufaya kamar wata mayya !” badon Zahrah taso ba haka ta yafa gyalen da Inna ke miƙomata, har zaure Inna ta raka Zahrah, saida taga ficewarta kafun ta koma gida,, kasancewar gari gaba ɗaya yayi duhu hakan yasa bata iya hango wanda ke cikin motar, kuma zuciyarta bata bata akan cewa shiɗinne ba, saboda ba motar da yazo da’ita ranan bane watace daban,, don haka tafara zaton ko bashi bane,, wani irin daddaɗan ƙamshine yashiga yawo acikin ƙofofin hancinta, kallonta ta maida izuwa inda ƙamshin ke fitowa, mutum ne tsaye a wajen amma bazata iya shaida ko waye bane, saboda duhu,, wani irin tsoro taji yakamata kaddai mai satan mutanene yabiyota har gida, da sauri tajuya don komawa gida, taku ɗaya yayi kacal, ya cafko hanunta, wanda hakan ya haifar masa da zubawar tsikar jiki,, jawota yayi gab dashi, cikin wata irin murya yace ” Shiiii idan kikayi magana saina yankaki !” jikin Zahrah ne yaɗauki rawa haɗe da ɓari, tsoro ne ya lulluɓeta a sakamakon jin abun daya ke faɗi, shikenan itakam Inna tajawo mata, tana zaman zamanta ta tilasta mata fitowa gashi wani zai yi garkuwa da’ita,, babban abun daya da gulamata lissafi, bai wuce yanda jikinsa da nata ke manne awaje guda ba, ga ƙamshin sa gaba ɗaya yagama rikitata,, a hankali ya ɗaura kansa a gefen wuyanta, wanda hakan yasanya tattausan sajensa gogar fatar wuyanta, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu a lokaci guda, ” Kinshirya mutuwa yanzu kokuwa ?” yaje fo mata tambayar data kusa tsinka ƴaƴan hanjinta,, cikin rawan murya tace “dan Allah kayi haƙuri kada ka cutar dani wallahi ni marainiya ce, da Allah kaɗai na dogara ” tuni hawaye sun wanke kan fuskarta, wata irin dariya Zaid yayi mai cike da mugunta, hannayensa yasanya duka biyu ya juyo da’ita gabansa, yazamana suna faced ɗin juna, wayarsa ya dannan take hasken tocila (torch light) yabayyana, rufe idanunsa yayi haɗe da kai hasken tocilan kan fuskarsa, cikin mayaudariyar murya yace ” fatan baki manta da wannan fuskar ba” sai a lokacin Zahrah taɗago idanunta ta sauƙesu akan kyakkyawar fuskar Zaid, wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da yin hamdala acikin zuciyarta,, wani irin ƙawataccen murmushi Zaid yayi mata, haɗe da kashe mata idonsa ɗaya, ” matsoraciya ” yafaɗa cikin murya mai sanyi,, hararan wasa Zahrah tayi masa haɗe da cewa “ko wama matsoraci ne idan har yaga mutuwa ” murmushi Zaid yayi haɗe dayi mata wani irin kallo, mai ɗauke da ma’anoni dayawa, wani irin yawu ya haɗiye alokacin da idanunsa suka sauƙa kan cikakkun breast ɗinta… “Muje mota” yayi maganar yana mai nufar inda motarsa ke fake,, bamusu itama ta biyo bayansa,, kan kujeran mai zaman banza ta zauna, haɗe da takure jikinta waje ɗaya, sam itakam sa gyale bawai yawani damunta bane, tafiso koda yaushe tazamana cikin hijabi, domin yana kare mata tsiraicinta, gashi yanzu duk ta takura kowani motsi tayi sai surarta ya bayyana,, “Yauma bazaki gaisheni bako ?” Zaid yafaɗa daidai sanda yajefa wani sweet cikin bakinsa,, sunkuyar da kanta ƙasa tayi cike da kunya, itakam balaifinta bane, i dan ta gansa ne komai ke kuncemata,, kallonta yayi ta gefen idanunsa haɗe da cewa ” kinsan maiya kawoni unguwarku yau ?” “A’a” tabasa amsa a taƙaice,, “SOYAYYA !!” yafaɗa cikin wata irin murya mai ɗauke da shauƙi,, “Soyayya kuma ?” Zahrah tatambaya domin sam bata fahimci inda kalamannasa suka dosa ba,, “INASONKI ZAHRAH !!” Zaid yafaɗi maganar yana mai kafeta da idanunsa, cikin tsananin mamaki Zahrah ke kallon Zaid, ko da wasa bata taɓa zaton zaiyi mata maganar soyayya anan kusaba, “Kinyi shiru sanar dani idan kinasona ” Zaid yafaɗa yana mai kama hannayenta yashiga murzawa a hankali,, wasu irin ƙwallane suka shiga gangarowa daga cikin idanunta zuwa kan fuskarta, ” kada ka yaudareni, ni macece mai rauni da kuma naƙasu, kaduba gidanmu, kaduba irin shigar dake jikina, ka dubi kanka kasan cewa nidakai ba ɗaya bane, akwai tazara mai tarin yawa a tsakaninmu, ban taɓa soyayya ba, bakuma naso nafara soyayya a’inda zuciyata zata wahalta, don Allah kajanye maganar soyayyata a gareka, domin nida kai bamu daceba ” tuni hawaye sungama wanke fuskarta,, murmushi Zaid yayi haɗe da cewa “Ba labari nake baki ba, saboda haka ki farka daga baccin dakike, nabaki nan da 3 days ki koyamawa zuciyarki soyayyata, zan aureki idan har kin amince da hakan, bana buƙatar da cewar mu ko rashin sa,, ungo wannan idan kin koma ki kunnata saboda zan iya nemanki koda yaushe ” yaƙare maganar yana miƙomata wata leda dake hanunsa,, kai tagirgiza alamar bazata karɓa ba, take yaɓata ransa, wanda hakan yasa taji ba daɗi, haka dolenta ta karɓa,, saida safe tayi masa, kana ta shige cikin gida,, tana shigewa shima ya ta da motarsa yayi gaba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button