SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Zahrah!” taji anƙira sunanta da murya wacce bazata taɓa mantawa da’ita ba a iya tsawon rayuwarta…
Ja tayi ta tsaya haɗe da maida kallonta inda taji sautin muryar tafito,, tabbas kuwa ba gizo kunenta keyi mata ba shiɗinne dai, kallonta yashigayi da idanunsa wanda suka zama jajaye, itama tsayawa tayi tana kallonsa, a wannan karon kam babu alamar wasa kokuma tsoronsa akan fuskarta,, kallonsa takeyi ido cikin ido…
“Dan Allah Zahrah ki saurareni, wallahi inasonki inamiki so me tsanani, inamiki soyayyar da babu wani wanda zaiyi miki shi a duniyar nan, meyasa bazakisoni ba Zahrah? Inasonki, Inasonki, Inasonki da duka zuciyata, dan Allah kiyarda muyi aure Zahrah!” cikin rauni yaƙare maganartasa saikace ba jarumin namiji ba…
Kallonsa Zahrah tashigayi tundaga ƙasan sa harzuwa samansa, wani irin murmushi tayi masa wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa,,, “Bantaɓa tunanin zaka iyayin wannan jarumtar ba, ƙwarai kayi ƙoƙari dahar ka iya tunkarana da wannan maganar, sai de kuma tun awancan lokacin na faɗamaka kafita a rayuwata, idan duka mazan duniya zasu ƙare na gwammace na mutu babu aure dana aureka, ka kalleni da kyau bancancanci zama matar mazinaci kuma ɗangiya ba, niba irin matan nan bane da yacancan ci fasiƙai irinka su samuba, natsaneka Zaid tsana me tsanani, wlhy danaga ranar da zan zamo matarka gwamma acemin naga ranar mutuwa ta, katafi kawai Zaid kaje nabarka da Allah, kuma inaso kasani cewa yau ɗin nan za’a tsaidamin ranar aurena da wanda zuciyata ta aminta dashi, wanda yake kamili me tsoron Allah, shi ba kamar kai bane ɗan giya!” tanakaiwa nan azancenta tajuya daniyar shigewa cikin gida…
Dasauri Zaid ya kamo hanunta haɗe da jawota da ƙarfi tafaɗa cikin jikinsa, dai dau lokacin ne kuma motar Dr.Sadeeq taƙaraso wajen….
Happy New Year ????
2/january/2020
Follow me on Whatsapp and Wattpad
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 76 to 77
Saurin turesa tayi haɗe da hankaɗasa gefe da iya ƙarfinta ta ƙwace jikinta daga nasa, wani irin mugun kallo tashiga yimasa haɗe da tofar da yawu aƙasa, da ace wulaƙanta ɗan adam abune me kyau to tabbas da akan fuskarsa zata tofa wan nan yawun ko hakan zai sanya ya gamsu da irin tsantsar tsanar da takeyi masa.
“Banafatan na sake haɗa jikina da wan nan ƙazamemmen jikin naka mai ɗauke da tarin najasa!” cike da tsananin ƙyamata Zahrah ta faɗi haka ga Zaid haɗe da juyawa tanufi hanyar shiga gida..
“Koda kuwa na daina aikata zina nakuma daina shan giya?” Zaid yafaɗi haka cikin dakakkiyar muryarsa…
Cak ta tsayawa daga tafiyan dakeyi, sosai maganar tasa ta daki zuciyarta..
A hankali yashiga takowa zuwa inda take saida yazo gaf da’ita kafun ya tsaya……. ” I promise to leave all my bad habit if you wish to marry me, I love you Zahrah, trust me for the sake of God, i will not hurt you!” gaba ɗaya muryarsa tayi rauni dagajin muryartasa kasan cewa yana cikin matsanancin damuwa…
Idanunta da suka kawo ruwa ta ɗago ta watsa masa su,,,,, Shi ɗin ma kallon ta yakeyi da idanunsa wanda suka zama tamkar an watsa musu garin barkono,, sun ɗauki tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafun da ga bisani Zahrah tajuya ta shige cikin gida, ko sake waiwayosa batayi ba yayinda yashiga ƙiran sunanta amma bata amsa masa ba harta shige cikin gida, because tagaji da wannan ɗan iskan yaudaran nasa, yanzukam bazata iya ɗauka ba….
Iskan dake cikin bakinsa ya fesar haɗe da meda duka hannayensa cikin aljihun wandonsa, cikin sanyin jiki haka yakoma cikin motarsa driver yayimawa motar key suka ɗauki hanyar fita unguwar batare da sun kula da Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa ba…
Haƙoransa ya sanya ya danne laɓɓansa na ƙasa komai daya faru akan idanunsa ya wakana sai de baijiyo magan ganun da suka shiga tsakaninsu ba,, wani irin ɗaci yaji maƙoshinsa nayi, iya matuƙa ɓacin rai yashigesa, bakomaine yafi komai ƙona masa ransa ba kamar yanda yaga Zaid yajawo Zahrah jikinsa, hakanan yaji wani irin mugun kishi ya turnuƙe masa zuciya,, babban abun dayafi ɗaga masa hankali shine yanayin daya hango fuskar Zahrah, tabbas yafuskanci wani ɓoyayyen abu daga gareta,,, key yayi mawa motarsa cikin ƙunan rai yayi reverse haɗe da barin ƙofar gidan nasu batare da ya aika ayi masa ƙiranta ba..
Zahrah na shiga cikin ɗakinta ta durƙusa a ƙasa haɗe da fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya kaicon zuciyarta da ta so mata namiji irin Zaid, ashe da gaske shiɗin mazinaci ne tunda gashi da bakinsa yafaɗa, kuka tashiga yi tamkar wacce aka sanarmawa da ranar mutuwarta, yayinda wani abu yataso ya tokare mata ƙirji wanda batasan komenene shi ba kamar yanda batasan kukan me takeyi ba…
Driver yana parking motar Zaid yace yafita ya bashi waje, aikuwa babu musu driver’n yafita daga cikin motar….. Kansa ya kafa ajikin kujera haɗe da fidda wani irin zazzafan numfashi ta bakinsa, zuwa yanzu kam bazai iya jurewa ba, sam bazai iya jure raɗaɗi dakuma azaban soyayyar Zahrah dake damunsa ba, tabbas da ace zai iya to da yayi iya ka ƙoƙarinsa wajen ganin ya yakice soyayyarta acikin zuciyarsa amma hakan bazai yiwuba domin kuwa duk kowani kwanan duniya soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarsa, zuwa yanzu soyayyar Zahrah babu inda bata ratsa acikin jikinsa ba,,,, a ƙalla yakai kusan 30 minute acikin motar yana saƙawa da kuncewa, da ƙyar ya’iya fitowa daga cikin motar kai tsaye yanufi babban parlour’nsa dake cikin guest house ɗin nasa, domin kuwa daga gidan su Zahrah guest house ɗinsa suka yiyo….
Yana shiga cikin falon ya faɗa kan doguwar kujera haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, kansa ne ke saramasa yayinda juwa ke ɗibansa, lallai yazame masa dole yasamawa kansa mafita, yazama dole yafarka daga wannan mafarkin daya keyi tabbas al’amuransa a yanzu suna masa kama da al’amara,, tabbas yana buƙatar samun relief daga damuwar dayake ciki, amma sai dai babu amfanin shangiya a yanzu domin kuwa koda yashama bata basa wani relief ɗin da ya kamata, miƙewa yayi yashiga cikin ɗakinsa, kai tsaye wani ɗan drower yanufa haɗe da buɗewa, hanu yasanya ya ɗauko wata wayarsa ƙirar techno phantom 9 wanda dama yana ajewane saboda rana irin haka, kasancewar baifito da wayoyinsa ba duk yabarsu a gida,, yana kunna wayar ya laluɓo wata lamba haɗe da turawa lambar text message, yana ganin alamar saƙon ya isa inda yakeson yaje yayi switch off ɗin wayar haɗe da maidata inda ya ɗaukota kwanciya yayi akan makeken gadonsa wanda yasha shumfuɗa ta alfarma, cusa kansa yayi cikin pillow haɗe da soma fitar da numfarfashi akai akai….
A hankali taturo ƙofar ɗakin wanda kafun ma tashigo tuni ƙamshinta yarigata shigowa, sanye take da jan wando pencil wanda yayi matuƙar bayyana kyakkyawar surar jikinta yayinda rigarta yakasance baƙa me kyau, rigan irin masu faɗin wuyan nan ne hakan ne yasanya manya manyan breast ɗinta bayyana kansu tasaman rigar,, takalmine me uban tsini a ƙafarta yayinda ta tufke dogon gashin kanta da jan ribbon kalan wandonta,, kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa wayayyar macece ƴar duma, shigarta kaɗai ya isa yabayyana maka ainihin ko wacece ita, saboda bashigane da mata masu mutumci sukeyi su fita ba kamar yanda ita tayi, domin kuwa ko ɗan kwali babu akanta, wani irin murmushine kwance akan fuskarta dake nuna alamar cewa tana cikin farinciki,, lumshe idanunta tayi haɗe da buɗesu alokaci guda, kallon surarsa kaɗai ya isa sanya mata nutsuwa, tajima tana tsumayi da kuma fatan Allah ya sake ɗaurata akansa, harta cire rai saikuma gashi yau shi da kansa ya gayyatota, lallai zata iya cewa a rana irin ta yau tafi kowa sa’a..