SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr.Sadeeq
Duk yanda Dr.Sadeeq yaso samawa kansa nutsuwa hakan yagagara domin kuwa sam zuciyarsa bata amince da zuwa wajen Zahrah da Zaid keyi ba, duk da yau yafara ganinsa aƙofar gidan su Zahrah’n amma jikinsa ya basa cewa ba yaune zuwansa na farko ba, amma bakomai zaiyi maganin abunne zai nisanta Zahrah da Zaid nisantawa me tsanani kuwa, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa…
Washe Gari.
Dasassafe Zahrah ta shirya tayi tafiyarta makaranta sai dai a ranta tana mamakin rashin ƙiranta da Dr.Sadeeq yayi, rabonta dashi tunjiya da yamma sunkuma rabu dashi akan cewa zai ƙirata sai gashi kuma har zuwa yanzu bai ƙirata ba, uzuri tayi masa akan cewa ko aikine yayi masa yawa domin tasan hakanan Dr.Sadeeq bazaiƙi ƙiranta ba…
Tana tafiya ba jimawa motar Dr.Sadeeq ta tsaya a ƙofar gidan nasu, fitowa yayi daga cikin motar yasha adonsa cikin blue ɗin shadda sosai kuma yayi kyau,, yaro ya aika cikin gidan yace yace ana sallama,, bajimawa yaron daya aika yadawo ya shaida masa ance me gidan yana fitowa…. Washe da baki Baffa yaƙaraso wajen Dr.Sadeeq dake tsaye ” Maraba da Likita, dama kaine ai da kashigo ciki amma ka tsaya a waje sai kace wani baƙo”
Murmushi Dr.Sadeeq yayi cike da girmamawa ya sunne kansa ƙasa haɗe da durƙusawa ya gaishe da Baffa,, fuska cike da fari’a Baffa ya amsa gaisuwan,,,
“Aikuwa kayi rashin sa’a domin kuwa mutumiyar taka bata jima da fita a gidan ba, tatafi makaranta ko karyawa bata tsaya tayi ba, amma ina ga zaifi kyau mushiga daga ciki ko”
“A’a Baffa nan ɗin ma yayi, dama wajenka nazo ae”
“To to masha Allah, saimu zauna ae ko abisa dakalin nan” Baffa yaƙare maganar yana meyi mawa Dr.Sadeeq nuni da dakalin ƙofar gidan.
Duk yanda Baffa yaso Dr.Sadeeq ya hau kan dakalin su zauna ƙiyawa yayi, domin kuwa Baffa surikinsa ne baidace ace sun zauna gaf da juna ba kodan saboda kara da matuntawa,,
“Shikenan to tunda dae kaƙi zama, inajinka Allah yasa dai lafiya?”
Kansa yaɗan sosa haɗe da sakin murmushi “Lafiya ƙalau Baffa dama akan maganan aure nane da Zahrah…” sai kuma yayi shiru ya kasa ƙarasa maganar dake cikin bakinsa, gani yake tamkar idan yafaɗi maganar kai tsaye Baffa zaice masa yayi gaggawa ko kuma yace yayi rashin kunya…
“Ka kwantar da hankalinka Likita kafaɗi duk wani abu dake ranka” Baffa yafaɗi haka ga doctor ɗin..
“Am dama…dama inaso ne kabani izini nasake turo magabatana dan sukawo sadaki san nan kuma a tsaida ranar aure”
“Alhmdlh to ai wannan abun farinciki ne Likita, wannan ae bawani abun damuwa bane, nabaka dama ka turosu aduk sanda kakeso, sai de kuma zakaɗanyi haƙuri, saboda zansa lokacin da ɗan tsayi saboda kasan ba a yin aure kai tsaye haka dole sai anɗanyi mawa yarinya sayayya, ina fata hakan bazai sosa ranka ba?”
Murmushin jin daɗi Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa “Naji daɗi sosai Baffa, amma kuma maganar sayayya basai kun wahalar da kanku ba, domin zuwa yanzu gidan da zamu zauna baya buƙatan komai, saboda haka don Allah kada kusa kanku a wahala”
Murmushi Baffa yayi haɗe da cewa “Ƙwarai mungode da wannan ƙoƙarin naka, amma sai de nace kayi haƙuri, duk da cewa mahaifin Zahrah baya raye ni ƙaninsa ina raye kuma niɗin ma ubane a wajenta, zan yi amfani da ɗan abun da nake dasu wajen ganin namata kayan ɗaki iya dede ƙarfina, kamarde yanda kowani uba keyiwa ƴarsa, wannan shine kaɗai gatan da zamu iyayi mata a yanzu” Baffa yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..
Ajiyar Zuciya Dr.Sadeeq ya sauƙe, haƙiƙa shi Zahrah kawai yakeso bawai wani abu na daban ba, kuma shi baiso akawota da komai, domin musamman ya ware mata ɓangarenta, kuma tuni yabawa wani abokinsa me saida furnitures a Dubai order akan akawomasa setin kujeru dakuma gado harma da duk wani abu wanda yasan zai ƙawata ɗaki,, amma tunda yaga Baffa yadage akan cewa shima zaiyi iya nasa ƙoƙarin shikenan zai ware wani ɗaki na da ban idan yaso sai a sanya kayan da Baffan yayi mata acan,,, cike da mutuntawa Baffa da Dr.Sadeeq sukayi sallama….
Baffa na shiga gida ya kalli Inna dake zaune,, “Salame inajin fa tafiyana yola yagabato idan banje jibi ba to zanje gata insha Allah”
Fuska ɗauke da mamaki Inna ke kallonsa, “Yola kuma Malam?”
“Ƙwarai kuwa, kinga fitana ɗin nan to yaron nan ne Sadeeq yazo min da maganar cewa inbasa dama yaturo magabatansa don sukawo sadaki akuma sa rana, to ni dai nace yaturosu duk sanda yakeso, yanzu dole zanje yola insanya fili dakuma gonan nan namu na gado a kasuwa idan aka siya intarkata kuɗin nan nasamu nasaiwa yarinyarnan kayan ɗaki dakuma kayan aikace aikace kamar de yanda kowani iyaye kemawa ƴarsu dan baiyiwuwa ace mu miƙata haka”
Ajiyar zuciya Inna tasauƙe haɗe da gyara zama ” Duk naji batunka Malam, amma kuma mezai hana kabar shi mijin nata yayi mata komai, ae naga yana da halin da zai iyayi mata fiye da wannan ma”
Murmushi kawai Baffa yayi shi kam tun ba yau ba yasan cewa bakoda yaushe ne Inna take gane karatun da’ake biya mata ba, don haka baiƙara cewa da’ita komai ba yawuce ɗakinsa, domin yasan kozai shekara a wajen yanason ganar da’ita tofa bazata fahimcesa ba,,, Inna kuwa baƙin ciki ne yakamata ina ma laifin yace zaiƙara jari da kuɗin, sai yace wani wai zai siyawa Zahrah kayan ɗaki,, haka taita ƙananun maganganunta babu maijinta ma balle yatanka mata……
Da yamma Dr.Sadeeq yaƙira Baffa yasanar masa cewa Baffansa zaizo da dare donsu tsaida magana, duk da cewa Baffa yayi mamakin sauri irin na Dr.Sadeeq ɗin amma saiya share yace Allah yakawosu lafiya,,
Hargida Baffa yaje yasanarwa Alhaji Umar abun da Dr.Sadeeq yace, kuma dama Alhaji Umar ɗin tuni yasan da maganar saboda duk abun da yafaru Baffa yanazuwa ya sanarmasa har kawo lefen da akayi ma Baffa yasanar masa,, sosai Alhaji Umar yayi murna yakumace zaizo gidan Baffa’n da dare a ƙarɓi baƙin dashi……
Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakane yakasance domin ana idar da sallan Isha Baffa Amadu da wani shaƙiƙin amininsa suka zo gidansu Zahrah,, sosai Baffa da Alhaji Umar suka musu tarba na mutunci,, zama sukayi haɗe dayin magana ta fahimtar juna, nan Baffa Amadu ya miƙa sadakin Zahrah ga Baffa naira dubu ɗari (100,000) bawani ɓata lokaci Baffa yasanya lokacin aure wata ɗaya, aikuwa take kowannensu yacika da farinciki haka sukayi sallama cike da girmama juna…….
(Team Dr. Saiku fitarmana da ankon biki, nasan duk Baba Zaid ze saya mana auren Zahrah’nsa ne ae ????????????)
4/Junuary/2020
Follow me on Whatsapp and Wattpad
~Fatymasardauna~
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 78 to 79
Zahrah na zaune a ɗakinta Inna takutso kanta cikin ɗakin.
“Idan kin gama rubuce rubucen banzan naki kije Baffan ki nanemanki!” Inna tafaɗi haka aƙufule, ko jiran amsan da Zahrah zata bata batayi ba tayi ficewarta acikin ɗakin,,, da kallon mamaki Zahrah tabi bayan Inna wai meke faruwane tun dawowarta amakaranta tafuskanci cewa ran Inna a matuƙar ɓace yake da’ita, domin kuwa ko abincin rana Inna batayi mata tayi ba, kamar yanda ta sabayi mata kullum, to koma dai menene Allah yasa bawani abu bane me zafi… Tattara books ɗin dake gabanta tayi haɗe da miƙewa ta sanya hijab a jikinta kana tafice daga cikin ɗakin…..