NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sallama ɗauke a bakinta takutsa kanta cikin ɗakin Baffan nata,,    zama tayi akan tabarman dake shimfuɗe a tsakiyan ɗaki, haɗe dayi mawa Baffa barka da gida,,  fuska ɗauke da fari’a Baffa ya amsa mata..

Gyara zama Baffa yayi haɗe da  cewa      “Bakomai yasa nayi ƙirankiba sai dan na sanar dake abun dayake faruwa sannan kuma na danƙamiki haƙƙin ki a hanunki,   yau da safe yaron nan likita yazo yasameni akan cewa zaituro magabatansa don sukawo sadakin ki,  nakuma bashi dama, to yanzu dai sun riga da sun danƙamin sadakin ki a hanuna saboda haka ga abunki naira dubu ɗari ne cus nakine halak malak” Baffa yaƙare maganar yana me miƙa ma Zahrah maƙudan kuɗin dake hanunsa….   

Gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi laƙwas gaba ɗaya duk wani kuzarinta ya gudu, hakanan taji wani iri a cikin zuciyarta.

“Ki karɓa mana Zahrah” Baffa yafaɗi haka ganin da yayi ko ɗago kanta takasa yi.

Girgiza kanta ta shigayi a hankali cikin muryarta me sanyi  tace “Duk abun da ka yanke a gareni Baffa dai dai ne, amma maganar sadaki ka riƙe a wajenka, saboda ko kabani  babu abun da zanyi dasu!” taƙare maganar cikin ladabi.

“A’a Zahrah ki karɓi abunki haƙƙin kine, saboda haka nima babu abunda zanyi dashi ki karɓi abunki saiki adana a wajenki, idan kuma wani abu zaki saya saiki saya, amma kada kiyi almubazzaranci dasu, zaifi kyau kisaya abu me mahimmanci wanda zai amfaneki yanzu ko gaba” maganar da tafito daga bakin Baffa kenan.

Shiru Zahrah tayi ita tama rasa yanda zatayi gaba ɗaya yanayinta yasauya, cikin sanyin jiki Zahrah tasanya hanu ta karɓi sadakin nata a hanun Baffa bawai dan ranta yasoba sai dan Baffa ya matsa akan cewa saita karɓa..

“Yauwa kinga idan kika riƙe abunki a hanunki ae yafi ko, sai kuma maganar sa rana, nasa nanda wata ɗaya, ai inaganin hakan yayi domin kafun lokacin insha Allah mungama iya ƙoƙarin da zamuyi wajen sayan ƴan kayayyakin ɗaki”

Wannan magana ta sa rana yafi komai rugaza mata zuciya, fiye da maganan sadaki,  haka nan taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta,, amma haka tayi mawa Baffa sallama cikin sanyin jiki tanufi ɗakinta…

Zama tayi akan katifarta haɗe da rumtse idanunta, take hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta suna gudu akan fuskarta,,   shikenan yanzu saura mata wata ɗaya tazamo matar aure? tambayar da tayiwa kanta kenan, bazata iya faɗan  wani irin yanayi ta tsinci kanta aciki ba, fargaba ne ko kuma tsoro ne shine abun da bata sani ba,,  idanunta ta buɗe haɗe da maida kallonta ga kuɗaɗen dake riƙe a hanunta,, tsurawa kuɗin idanu tayi tamkar mai son gano wani abu ajikin kuɗin,,   hawayene suka kuma ɓalle mata, batasan dawani idanu zata kalli Dr.Sadeeq ba, shi wani irin mutum ne? yasani ƙwarai cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace da ita da bazawara duk ɗaya suke, amma kuma shine ya cire maƙudan kuɗaɗensa yabada amatsayin sadakinta alhali kuma farashinta baikai haka ba, ita ba irin matan nan bane dasuka  dace a sayesu da tsada har haka ba, domin kuwa acikin abubuwa goma da zasu ƙara farashinta babu kaso tara,  saboda haka bata cancanci wannan sadaki ba,,    hanu tasanya ta share hawayenta,  haƙiƙa bazatace batason Dr.Sadeeq ba amma kuma batajin son nasa acikin jini da jikinta,  amma hakan bawai wani abu ne da zaisanya taƙi aurensa ba, domin shi ne ma mutum na farko aduniya daya cancanci ta aura, kodan halaccin daya gwada mata a rayuwa…. Cikin wata jakarta tasanya kuɗin sadakin nata, haɗe da dawowa ta kwanta akan katifarta,  bazama ta iya ƙarisa assigment ɗin nata ba domin kuwa gaba ɗaya yanayinta yasauya damuwa ta bayyana a tattare da’ita,, da ƙyar ta iya jawo wayarta taƙira Husnah ta sanar mata da duk wani abun daya faru,, daɗine ya kama  Husnah sosai take ta hau farinciki haɗe da cewa gobe zatazo yakamata su fara shirye shiryen biki tunda wuri, domin wata ɗaya bawani lokaci ne me tsawo ba idan har darai da kuma lafiya…


“Kiyi kuka da kyau Saleema amma kuma kozaki mutu bazaki auri Sadeeq ba matuƙar bai fasa auren da zaiyi da waccar ƴar ƙasƙantattun mutanen ba, ni bazan iya haɗa iri da jinsin matsiyata ba!” Abunda Hajiya Habiba take faɗa kenan cikin ɓacin rai.

Ɗago kai Saleema tayi takalli mahaifiyarta ta fuska caɓa caɓa da hawaye, cikin muryar kuka Saleema tasoma cewa  ” Wlhy inasonsa Mom kuma bazan taɓa iya auren wani bayan shiba, nidai na amince zan aureshi a haka, idan yaso bayan auren sai nasan yanda zanyi naƙori ita yarinyar”

Kallon ke shashasha ce Hajiya Habiba tashiga yi mawa Saleema, cike da baƙin ciki taja tsuka haɗe da watsawa Saleema’n harara “Nibansan yaushe zuciyarki ta mutuba wlhy Saleema, ashe ke baki da hankali? to nifa kisani nagama maganata aure da Sadeeq ne anfasa, kuma suzo su kwashe lefensu bama buƙata, domin kuwa kamarni Hajiya Habiba bazan lamunci cinfuskaba, saboda abunda suke shirin yi yanzu cin fuskane a gareni” fuuuu haka tayi wucewarta sama, tabar Saleema tana ta ruskar kuka, saikace wanda akace ubanta ya mutu….


Baffa na zaune a wajen sana’arsa wasu maka makan motoci guda biyu suka faka adaf dashi..  Sosai yayi mamakin ganin Alhaji Ma’aruf yakuma dawowa garesa a karo na biyu, wanda ko kusa baiyi tunanin haka ba..  

Bayan sun gaisane Alhaji Ma’aruf ya nisa haɗe da cewa “Nasan zakayi mamakin dawowata gareka Malam Hayatu, sai de kuma me nema baikamata ya gajiya ba”

Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe haɗe da tattaro duka nutsuwarsa yadubi Alhaji Ma’aruf…
“Bazan taɓa ɓoyemaka ba Alhaji, kamardai yanda nafaɗa maka afarko yanzu ma hakane, domin maganan da nakeyi maka yanzu ma jiya aka kawo sadakin yarinyar, saboda haka sedai nace kawai kuyi haƙuri”

Kai Alhaji Ma’aruf yashiga jinjinawa, zuwa yanzu dolensa zaibawa Zaid haƙuri akan cewa yayi haƙuri yacire yarinyar aransa, domin kuwa idan ba wani ikon Allah ba to babu alamun cewa Zaid zaisamu auren yarinyarnan Zahrah..

Haka Baffa da Alhaji Ma’aruf suka rabu, bayan Alhajin yayi mawa Baffa alkhairi maiyawa, amma sam wannan karon Baffa yaƙi karɓa yace bai buƙata, duk yanda Alhaji Ma’aruf yaso Baffa ya amshi kuɗin hakan bai samu ba,, haka Alhaji Ma’aruf yayimawa Baffa sallama shida tawagar body guard ɗinsa suka bar wajen, sam Alhaji Ma’aruf baiji daɗin hakan ba, yaso ace ɗansa yasamu abunda yakeso…..

Cike da tsananin damuwa Alhaji Ma’aruf ke kallon Zaid dake zaune a ƙasa yayi shiru, gaba ɗaya ya sanja, komai nasa yazama sanyi sanyi, ga alamomin damuwa da suka bayyana kansu a jikinsa, baisan wani irin masifaffen soyayya ɗannasa ya kamu dashi ba, baimasan taya ya Zaid zai ɗauki maganar da zai faɗa masa ba, amma dai yazama dole yafaɗa masa gaskiya amatsayinsa na mahaifinsa.

“Zaid!”
Alhaji Ma’aruf yaƙira sunan Zaid murya a tausashe.

“Na’am Dad” Zaid ya amsa murya  ƙasa ƙasa.

“Inaso kabani hankali da nutsuwarka, dan Allah Zaid ka kwantar da hankalinka, nasani kuma kaima kasani nema cikin nema haramunne, kacire wannan yarinya acikin zuciyarka domin kuwa yau naje nasamu shi Baffan nata, yakuma shaidamin cewa a halin yanzu har ya karɓi sadakinta, saboda haka zaifi kyau kacireta a zuciyarka, kanemi wata nasan babu wata mace da zata ƙika”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button