SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tamkar wanda Dad ɗin ya watsa masa ruwan zafi haka yaji sauƙar maganganun mahaifinsa acikin kunnuwansa, da sauri yaɗago jajayen idanunsa ya watsawa mahaifin nasa su,, bakinsa na rawa yace “Ankarɓi sadakinta kuma Dad?”
“ƙwarai kuwa Zaid abunda Baffan nata yafaɗamin kenan, shiyasa nace ka cireta a ranka”
Kai Zaid yashiga girgizawa,,,,, “Bazai taɓa yiwuwaba Dad, wlhy wani bazai taɓa auran Zahrah ba matuƙar ina numfashi acikin duniyar nan, inasonta fa Dad meyasa bazaku gane hakan ba? bazan iya cigaba da rayuwaba idan har babu Zahrah a gareni, nasan laifinane Dad, amma duk da haka bai dace a hanani Zahrah ba, saboda inasonta inamata wani irin so me tsanani please Dad niko yanzu dan Allah a ɗaura mana aure idan yaso daga baya ni na amince zan shawo kanta, nasanma tana sona har yanzu, kuma nasan daga baya zata yafemin abunda nayi mata!”
Cike da tsananin mamaki Dad ke kallon Zaid wanda gaba ɗaya ya ruɗe alokaci ɗaya, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikinsa ba ? Dad yatambayi kansa cike da tsananin mamaki, domin kuwa sam Zaid ba haka yake ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu amma kuma wani babban abun mamaki shine yauga Zaid nan yana faɗin wai bazai iya rayuwa ba idan babu wata,,
“Zaid!” Dad yakuma ƙiran sunansa cike da tausayawa domin shikam baitaɓa ganin soyayya irin wannan ba…
Zaid bai iya amsawa mahaifinnasa ba, saide idanunsa daya ɗago ya kalli Dad ɗinnasa dasu.
“Zaid ka kwantar da hankalinka, ba ita kaɗai bace mace a duniyar nan akwai mata da yawa, kana da ƴancin da zaka zaɓi duk irin macen da kake so” Dad yafaɗi haka ga Zaid cikin lallami…
“Idan ni inada ƴanci ita kuma dana cuta fa? nacutar da ita Dad cuta mafi muni, na zalunceta, banda wata hanya dazanbi na goge laifina a wajenta, sai ta hanayar aurenta, dan Allah Dad kayi wani abu, bazan iya jure rashin Zahrah ba!” yanzu kam har ƙwalla suncika idanun Zaid batare daya sani ba. (hmm so mugun wasa)
Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sa kai yafice daga cikin falon Dad ɗin nasa, da kallo kawai Dad yabisa dashi harya fice, baisan me yake shirin faruwa da ɗan nasa ba amma ae so ba hauka bane…..
Zaid yana fita daga ɓangaren Mahaifinsa direct part ɗinsa yanufa, idanunsa gaba ɗaya sun rufe yayinda kansa ke matuƙar sara masa, sam bazai iyaba, bazaitaɓa iya jure rashin Zahrah ba, lallai yazama dole yakuma yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa,, tabbas yazama dole ya kusanto Zahrah zuwa garesa koda kuwa hakan zai jawo faruwar abubuwa masu tarin yawa…key ɗin motarsa ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe babu wani abun dayayi saura aciki banda tsananin soyayyar Zahrah…..
Da wani irin mahaukacin gudu Zaid yafigi motarsa yafice daga cikin gidan saura kaɗan yabitakan me gadi daya wangale masa gate, Allah ne ya ta ƙaita Me gadin yayi saurin matsawa gefe, domin kuwa ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba Zaid yayi yo kansa….
Tuƙi yakeyi amma kuma kwalbar giya ne riƙe a ɗayan hanunsa yana sha, jinkansa yake gaba ɗaya yana juyawa, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi, idanuwansa Zahrah kawai suke hango masa, batare da Zaid yakulaba motarsa tayi karo da wata babbar mota, take motar tasa ta ɗagu sama haɗe da faɗowa ƙasa sannan kuma tashiga gungurawa kan titi, batare da Zaid dake cikin motar ya tsira ba…..
(Dan Allah ku daina min kutse acikin labarin nan, kudaina saurin yanke hukunci, haryau ban ce ga wanda zai auri Zahrah a tsakanin Zaid ko Dr.Sadeeq ba, kubarni ni kaina nasan abunda ya dace, zaifi kyau ku sanyamin idanu kukuma ci gaba da bina harzuwa ƙarshen labarin nan, amma abun da wasunku sukemin banajin daɗinsa, suna nunawa kamar ina shirin yin abun da bai dace ba, suna nunawa kamar bansan me nakeyiba, dan Allah kuyi haƙuri zancigaba da rubuta labarin nanne kamar yanda yazomin acikin kai dakuma zuciyata, idan kukayi haƙuri komai zaizo cikin sauƙi kuma ina da tabbacin cewa ƙarshen labarin zai muku daɗi, nasan dama dole zan fuskanci ƙalubale a wajen wasunku, amma banyi tunanin abun zaiyi tsanani har haka ba,, amma bakomai namuku uzuri my lovely fans nasan ƙaunace tajawo hakan????… kuyi haƙuri nayau baida yawa wlhy gaba ɗaya banganewa kaina bane shiasa inafatan zakumin uzuri)
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
fatymasardauna
Editing is not allowed????
(Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareki Masoyiyar asali MY SHALELE (marubuciyar RAGGON MIJI) kiji daɗinki Shalelena iya wuya munatare inakuma yi miki son so)
CHAPTER 84 to 85
Kyakkyawan murmushinsa ne ɗauke akan fuskarsa still hannayensa a ware suke, alamar ta taho zuwa garesa.
Ahankali tashiga takawa tana nufar inda yake, ganin haka yasanya Zaid sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, haɗe da sake sakin murmushi alokaci na ba adadi,, koda tazo gareshi yana shirin yaji ta rungumesa amma kuma sai yaji saɓanin haka, domin kuwa tana zuwa kusa dashi, sai gani yayi ta raɓa ta gefensa ta wuce batare dako kallonsa tayi ba. Cikin hanzari yasha gabanta haɗe da kamo hanunta. Cak ta tsaya daga tafiyan da takeyi haɗi da rumtse idanunta,, a hankali ya zame guiwowinsa ƙasa, ya durƙusa mata, duka hannayenta ya kama ya riƙe acikin nasa hanun….
Cikin murya me ɗauke da matuƙar rauni yace da’ita…… “Koda kalamaina baza suyi tasiri acikin zuciyarki ba, dan Allah inaso ki tsaya ki saurareni, ki dubi halin danake ciki Zahrah, banda wani sauran farinciki a duniyar nan idan har babuke a tare dani, haƙiƙa nayi nadama nakumayi dana sanin abun dana aikata a gareki, amma dan Allah Zahrah kiyi haƙuri kiji tausayina ki yarda muyi aure, wallahi namiki alƙawari zandaina duk wani abu danakeyi, zan baki farinciki me ɗorewa, zan mantar dake duk wani damuwa, me yasa bazaki cigaba da sona ba Zahrah? meyasa bazakiji tausayina ki yarda da tuban danayi ba, inasonki Zahrah so irin wanda bantaɓa yiwa kowa irinsa ba acikin wannan duniyar, zan iya fansar da komai nawa idan har zaki amince ki aureni, zan iya rayuwa babu komai babu kuma kowa, amma bazan iya rayuwa babu keba, zan iya sadaukar da duka dukiyata, dakuma duk wani abu nawa dana mallaka, matuƙar zansameki amatsayin matata, dan Allah Zahrah ki yarda dani mana, ninefa Zaid, nine mutumin da kika fara so acikin rayuwarki, shin mai yasa bazaki tausayamin ba, kikalli cikin idanuwa na Zahrah hakan kaɗai ya’isa bayyana miki irin tsananin ƙaunar danakeyi miki, inasonki, wallahi inasonki Zahrah!!..” gaba ɗaya zuciyarsa ta karye, sosai rauninsa ya bayyana… A kan fuskar Zahrah kuwa hawayene ke zuba tamkar anbuɗe famfo sannan kuma haryanzu idanunta akulle suke, yayinda harkawo yanzu hannayenta ke cikin nasa hanun. Bazatace yaushene ko kuma tayayane itama ta tsinci kanta da zamewa ƙasa ba, ta dai tsinci kanta da kafa guiwowinta a ƙasa. kukane yaci ƙarfinta bazata kuma iya cewa ga abu ɗaya dake damunta ba… Hanunta tashiga ƙoƙarin cirewa daga cikin nasa hanun, amma kwata kwata Zaid yaƙi bata daman hakan saima ƙara matsowa kusa da’ita da yakeyi…