NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Zahrah!”  yaƙira sunanta cikin wata irin murya da bata fita sosai…

Manyan manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye ta ɗago haɗe da  waresu akansa,  batare da tace dashi komai ba,, wani irin kallo yakeyi mata wanda yake ɗauke da tarin ma’anoni masu yawan gaske..  Hanunta dake cikin nasa hanun  ya shiga murzawa  haɗe da langwaɓar da  kansa gefe yana me cigaba da kallon fuskarta.   Hawayene yaziraro daga cikin idanun ta zuwa kan ƙuncinta,  sam bata taɓayin zato ko tsammani ba, saijin sauƙar bakinsa tayi akan ƙuncinta, yayinda yasanya harshensa yana me lashe ruwan hawayen  dake gudu akan ƙuncin nata.  wani irin bugawa zuciyar Zahrah tashigayi da sauri, yayinda numfashinta keshirin ƙwace mata batare da tashiryawa hakan ba,,  cikin ɗan kuzarin daya rage mata tayi saurin tureshi gefe  haɗi  da miƙewa tsaye, ƙoƙarin kama hanunta  yakuma yi amma saidai baisamu daman hakan ba domin kuwa tuni harta fara tafiya.     “Zahrah”   yakuma ƙiran sunanta amma sai dai ko waiwayosa batayiba balle yasaran zata amsa masa..    Jefa ƙafarta kawai take batare dako da ganin gabanta tanayiba, gaba ɗaya ƙwalla suncika mata idanu,  yayinda ƙirjinta ke mata luguden duka kanta kuwa tamkar anɗaura mata gungumen ice haka takeji yamata nauyi…

Cikin Hanzari Zaid yarufa mata baya, yana me ƙiran sunanta amma kuma bata amsa masaba, haka kuma bata tsayaba, dai  dai lokacin wani me taxi yazo wucewa da sauri Zahrah taɗaga masa hanu, aikuwa take yatsaya,, ganin haka yasanya Zaid yaƙara sauri don yaga alamar tafiya zatayi batare da ta tsaya ta sauraresa ba,, amma ina yamakaro domin mai taxi ɗin yana tsayawa Zahrah    ta buɗe murfin motar tashige haɗe da cewa mai taxi ɗin yatada motar sutafi..    Zaid na ƙarasowa wajen, me taxi ɗin kuma na figar motar ya cillata kan titi.. Wani irin iska me zafi Zaid ya fesar daga cikin bakinsa, sam baiso haka ba, yaso ace yaji koda kalma ɗayane daga bakinta, amma kuma duk da haka yamatuƙar jin daɗin ganinta, gashi kuma har kusa da’ita yasamu yazo, babban abun farincikin kuma shine har numfashinta ya shaƙa. Take yaji zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi, yayinda daɗi da kuma nutsuwa suka cika masa ruhinsa.. Cike da farinciki haka yakoma  inda yabar motarsa…..

Zahrah kuwa ko acikin taxi hawayenta kasa tsagaitawa sukayi, saima kara tuttulowa da suke tamkar ana hankaɗosu…   Ahaka har mai taxi ɗin yakawota ƙofar gidansu. Kuɗinsa tabasa ko canji bata tsaya karɓa ba ta wuce cikin gida.. A zauren gidan nasu ta tsaya haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, sam bataso kowa yasan halin da take ciki, ta barwa Allah dakuma zuciyarta…

Tana shiga cikin gida Inna tayo wajenta da sauri 

“A’ina kika tsayane Zahrah? gaba ɗaya duk kinsa hankalinmu yatashi, munsan bakya kaiwa iwar haka baki dawo ba”  Inna tafaɗi haka tana me ƙaremawa yanayin Zahrah’n kallo.

“Bansamu abun hawa bane Inna, yau Samad yana da wani uzuri shi yasa baisamu daman ɗaukoni ba” Zahrah tafaɗi haka tana me ƙwaƙulo murmushi ta aza akan fuskarta..

Da kallon tuhuma  Inna tabi ta harta shige cikin ɗakinta, tana shiga cikin ɗakin ta dannawa ƙofarta sakata, a hankali tazame  ƙasa  haɗe da jingina bayanta da ƙofar, kana ta cusa kanta cikin cinyoyinta, wani irin kuka tashiga rerawa me tsananin bantausayi,   Yazatayi da rayuwarta ne itakam, da badon kada tayi saɓo ba da sai tace  wannan ƙaddaran nata yayi mata girma dayawa, amma sai dai kuma ba’aja da ikon Allah, haƙiƙa tayi imani cewa komai zaizo yawuce, domin kuwa komai yayi farko yana da ƙarshe, amma kuma sai dai tana da yaƙinin cewa kafun  nan wataƙila zuciyarta tayi  bindiga ta tarwatse,,   “yazatayi da abun da takeji acikin zuciyarta?” tambayar da kullum saitayi mawa kanta kenan, amma kuma zancen ɗayane shine bata da amsar da zata bawa kanta..  Tana cikin kukan taji wayarta na ƙara, amma ko ɗago kanta batayiba haka wayar  taƙaraci tsuwanta har ƙiran ya katse, wani ƙiran ne yakuma shigowa  still har wayar ta katse batako  ɗaga ido ta duba taga waye yake ƙiranta ba..  Kuka tayi sosai kafun tatashi daga durƙushen da take takoma kan katifarta,,,, kwanciya tayi luf tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai, yayinda tsikar jikinta ke yawanta tashi, idan tatuno kusancin da suka samu ɗazu ita da Zaid,  bakomai ke dagula mata lissafi da kuma hautsina mata ƙwaƙwalwa ba kamar idan tatuna da yanda yasanya harshensa akan kumatunta yanashan hawayenta, yana me kuma yi mata wani irin kallo wanda yakasa ɓacewa daga cikin idanunta,,,  batasan me Zaid yakeso a tattare da’ita ba,  wataƙila rayuwarta yakeso, wataƙila kuma hauka yakeso yaga tayi, baisan yatakeji idan ta gansa ba, baisan metakeji agame dashi  aduk sanda taɗaura idanuwanta akansa ba, sake gyara kwanciyarta tayi, tabbas tana da buƙatar samun wani wanda zata faɗawa gaba ɗaya damuwarta, tana da buƙatar wanda zai kwantar mata da hankali yakuma samamata nutsuwa, tana kuma buƙatar wanda zai fayyace mata abun dake cikin zuciyarta, koda hakan zaisanya tasamu sauƙi da salama,, haka dai Zahrah tayi bacci zuciyarta cike da tarin tambayoyi…..

Zaid ne kwance akan  wata haɗɗɗiyar kujera mai kama da gado, wanda take aje cikin wani irin katafaren falo wanda aka ƙawatasa da kayan ƙyale ƙyale dakuma more rayuwa.    Murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda kyawawan idanunsa suke a lumshe, wani irin shauƙi me tsanani yakeji a tattare dashi,  a iya ganinta da yayi jiyake tamkar anyaye masa gaba ɗaya damuwarsa ne,   idanunsa yasake lumshewa haɗe da  sake shaƙan daddaɗan ƙamshin da yakeyi masa yawo acikin hanci,  ƙamshin da tun ɗazu yakasa barin  hancinsa, “wani irin daddaɗan ƙamshine haka Zahrah’nsa keyi?”  ya tambayi kansa,,  tabbas zai so ace  iyanzu Zahrah na kusa dashi,  dakuwa kwana zaiyi manne da’ita yana shaƙan wannan daddaɗan ƙamshin nata,  sannu ahankali wani irin muguwar kasala ke dirar masa, yayinda wani irin sha’awarta me tsanani ya kawo masa ziyara,,   a hankali yasanya harshensa ya lashi laɓɓansa haɗe da sanya hanu yashafi  ƙwantaccen beard ɗin sa wanda koda yaushe yake ƙara ƙawata masa fuskarsa,,    a hanakali ya ware manyan idanunsa wanda suka soma sauya launi daga farare zuwa kalan bacci, wanda idan ka kallesu dole zasu sauƙar maka da kasala…  Laptop ɗin dake kusa dashi ya ɗauka, haɗe da buɗewa, take hoton kyakkyawar fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin,, murmushi yayi haɗi da sanya hanu yashafi kan screen ɗin laptop ɗin..

“Inasonki Zahrah!” 

ya faɗi haka cikin wata irin murya me ɗauke da matsanancin shauƙi.  Take yaji yana matuƙar sha’awan kallon vedion dayayi mata ɗazu batare da tasani ba, lokacin fitowarta daga gidan Hajiya Shuwa.   Wayarsa da vedion ke ciki ya ɗauka haɗe da kunnawa,  kallon vedion yakeyi yana murmushi, amma  kuma kwata kwata saƙonnin da suke shigowa ta Email ɗinsa sun hanasa sakat..   Kai tsaye fita daga ɓangaren vedion yayi ya kutsa cikin Email ɗin nasa,  saƙonnin abokanan business ɗinsa ne, sama sama yakaranta saƙonnin, haryana shirin fita daga cikin Email ɗin sai kuma idanunsa suka sauƙa akan    saƙon  Jasheer wanda yaturo masa,, hakanan yaji gabansa yaɗan faɗi saboda  yasan duk saƙon da zaizo daga Jasheer to akan Zahrah ne,,   buɗe saƙon yayi haɗe da ƙurawa hoton da Jasheer yaturo masa idanu..  Wani irin abu ne yaji ya taso yatokare masa maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sukai jajur dasu, take gashin jikinsa suka mimmiƙe,   wani irin juyawa yaji kansa nayi masa,, shin dagaske katin ɗaurin auren Zahrah idanuwansa suke gane masa ko kuwa? sake waro manya manyan idanuwan nasa yayi aikuwa ba ƙarya idanun nasa keyi masa ba, sunan Zahrah ne rantaɓe ajikin katin dakuma sunan Dr.Sadeeq,, wani irin ƙara Zaid yayi haɗe da yin cilli da  wayartasa, take ta bugi bango  takuma faɗowa ƙasa lokaci ɗaya ta tarwatse.. Cikin matsanancin ɓacin rai jikin Zaid yasoma rawa take yaji wani irin matsancin  zafi a dai dai saitin zuciyarsa, lokaci ɗaya wani irin tari  ya tasomai,  take yasoma tari babu ƙaƙƙautawa, sai ga jini na fita ta bakinsa abun mamaki, abun da bai taɓa gani ba arayuwarsa,,  da ƙyar yasamu tarin ya tsagaita, amma kuma duk da haka ƙirjinsa bai daina yi masa ƙuna ba, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi har cikin cikinsa kuwa yakejin zafin,, a hankali ya jingina bayansa da jikin bango, haɗe da rumtse jajayen idanunsa,    numfashi yashiga fitarwa a hankali, daga ni kai kasan yana matuƙar jin ciwo,, cikin yanayi na wahaltuwa  haka ya daddafa zuwa cikin ɗakinsa,  ƙaramin drower’n dake gefen gadonsa ya jawo haɗe da ciro magungunansa,  tsabar ɗacin da yakeji a maƙoshin sa da ƙyar ma ya iya haɗiye magungunan… Kwanciya yayi  akan gado haɗi da rumtse idanunsa, baisan ina zai tsoma rayuwarsa ba,  baisan tayaya zai fara jure rashin Zahrah akusa dashi ba… Kamar dai yanda Zaid yaga rana haka yaga dare, koda kuwa na minti guda ne baiji wani salama ko sanyi acikin zuciyarsa ba, haka ya share awanni masu yawa cikin ciwo,, sai da yayi sallan Asuba ƙafun wani irin bacci me nauyi ya sace sa batare daya shiryawa hakan ba……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button