SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zahrah kuwa yau da wani irin irin matsanancin ciwon kai ta tashi, gaba ɗaya idanunta sunyi luhu luhu dasu, da gani kai kasan cewa kuka tasha ta ƙoshi.
Yau ya kasance aurenta da Dr.Sadeeq saura kwanaki shida kenan tana ƙirgawa kuma acikin kwanakin nan ne zasu fara gudanar da shirye shiryen da suka tsara,, gaba ɗaya ji takeyi bata marmarin auren, sannan kuma ji takeyi komai yafice mata arai, bawai kuma don batason Dr.Sadeeq ɗin ba, tun shekaran jiya Dr.Sadeeq yakawo mata ɗinkunanta da kuma kayan da zata sanya a kamu da wajen diner, amma kuma ko duba kayan batayi ba balle taga ma ko sunyi mata ko basuyi mata ba, batasan meyake damunta ba, amma tabbas tasan akwai wani baƙon al’amari dayake ta kusanto rayuwarta aduk kwanan duniya. Yau hakanan tatashi taji ko gyaran jikin ma batason zuwa, amma kuma dazaran tace bazata jeba tasan Inna zata sanyata agaba da yawan tambayoyi, don haka ma gwamma kawai ta je ɗin zaifiye mata… Sauri sauri haka ta shirya tafito, saboda tasan cewa yanzu haka Samad na ƙofar gida yana jiranta… ai kuwa tana fitowa taga motar Dr.Sadeeq fake a ƙofar gidan nasu, murmushi kawai tayi haɗe da ƙarasawa wajen motar… “Allah sarki Samad yana da haƙurin jira, da Dr.Sadeeq ne da yanzun ya ƙirata a waya” tafaɗi haka a zuciyarta dai dai sanda taƙaraso gaf da motar, buɗe murfin motar tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, “Kayi haƙuri Samad nabarka kana ta jira” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin rufe murfin motar, batare da takalli Inda Samad ɗin ke zaune ba.
Tana rufe murfin motar tadawo da kallonta wajen zaman driver fuskarta ɗauke da murmushi,, a maimakon taga Samad saitaga Dr.Sadeeq, mamakine ya bayyana akan fuskarta alokaci guda, sake ware idanu tayi tana kallonsa, da’alama dai ganinsa yabata mamaki sosai…
Murmushinsa me kyau yayi mata haɗe da kafeta da idanunsa wanda suke sauƙar mata da wani irin yanayi na kasala ajikinta.. Itama murmushin tayi masa haɗe da shagwaɓe fuska….
“Ni dai nayi fushi!” tafaɗi haka a shagwaɓe…
“Tuba nake”
Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me kama kunnuwansa da duka hannayensa.. alaman ban haƙuri.
“Ni dai naƙi wayon” tafaɗi haka tana me kaɗa idanunta.. Murmushi yayimata haɗe da kamo duka hannayenta yasanya acikin nasa hanun, lumshe idanunsa yayi alokaci guda haɗe da buɗewa
“Nayi kewarki sosai Zahrah na!” yafaɗi haka cikin wata murya me sanyi.
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da soma ƙoƙarin janye hanunta daga cikin nasa hanun, amma kuma bata samu daman hakan ba. “Meyasa jiya kika ƙi ɗaga wayana?” yatambayeta cike da kulawa bayan yagama karantar yanayin da take ciki. Sai alokacin ne ma Zahrah ta tuno da cewa jiya taga missed calls ɗinsa, sanann kuma bata bi bayaba,, ƙaƙalo murmushi tayi haɗe da cewa ” Kayi haƙuri nayi bacci ne alokacin”
Kansa ya jinjina badon wai ya gamsu da abun da ta faɗa ba,, ta da motar yayi suka hau kan titi. Saida sukayi nisa a tafiyar kafun yadawo da kallonsa gareta, sosai tayimasa kyau komai nata ya canja, sai dai kuma kallo ɗaya yayimawa fuskarta yafuskanci cewa tayi kuka, dafari yaso tambayarta meke damunta, amma kuma sai kawai ya share,,, sama sama yake janta da hira harsuka iso gidan Hajiya Shuwa… Yana ganin shigewarta cikin gidan ya sauƙe ajiyar zuciya ƴaɗe da kifa kansa akan steering motar, “meke damun Zahrah ne?” ya yiwa kansa tambayar a bayyane, amma sai dai kuma bayida amsar da zai bawa kansa…. A jiyar zuciya yakuma sauƙewa akaro na barkatai, zuciyarsa cike da tunani kala kala yaja motarsa yabar ƙofar gidan……. Ɓangaren Zahrah kuwa kwana biyun nan wasu irin magunguna masu ƙarfin gaske Hajiya Shuwa take bata tanasha, hakan kuwa shike taimakawa wajen hautsina mata tunaninta, wani irin abu takeji acikin jikinta wanda kai tsaye za’a iya ƙiransa da suna sha’awa, ko da yaushe yanzu Zahrah cikin jin feelings take, hattakai ta kawo yanzu alwala ma baya daɗewa ajikinta yake karyewa saboda sosai sperm ke fita ajikinta, duk kuma ɗaya daga cikin aikin magungunan ƙarin ni’iman da Hajiya Shuwa ke bata ne, lallai ita kanta tasan cewa Hajiya Shuwa tayi mata babban haɗi me matuƙar kyau…… (su Doctor za’asha nice????????)
Tunda bacci ya ɗaukeshi da asuba bashi yafarka ba sai ƙarfe 9:30 am, da wani irin zazzafan zazzaɓi yatashi, wanda ya zamana ko ɗaga kansa ba ya’iyawa hatta numfashima da ƙyar yake iya fitarwa. Yana a wannan halin ne yaji anturo ƙofar ɗakin nasa, bai iya ɗago kansa ya dubi ko waye ba amma kuma duk da haka ya gane waye ne yashigo cikin ɗakin… Dasauri Alhj Ma’aruf yaƙaraso garesa…
“Lafiya Zaid meke damunka?” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka yana me kai hanunsa jikin Zaid, da sauri yajanye hanunsa daga jikin Zaid ɗin domin kuwa jiyayi jikin Zaid ɗin yaɗau zafi rau kamar wuta. “Subahanallah, bana ƙira Doctor yanzu” Dad yafaɗi haka yana me ƙoƙarin ciro wayarsa daga cikin aljihu,, bugu biyu Dr.Bilal yaɗauki wayar, cike da damuwa Dad yace yanason ganinsa jikin Zaid ne yatashi. take Dr.Bilal yace gashinan zuwa..
Zama Dad yayi jigum agefen gadon Zaid ɗin, gaba ɗaya yarasa mekeyi masa daɗi, sosai matuƙa cutar Zaid ke damunsa, yana matuƙar ƙaunar Zaid sam bayaso wani abu ya samesa, musamman ma yanzu da Dr.Bilal yashaida masa cewa Zaid ɗin yana ɗauke da ciwon zuciya me tsanani… Mintuna kaɗan Dr.Bilal yaƙaraso gidan, babu wani ɓata lokaci kuwa yashiga yiwa Zaid wasu ƴan gwaje gwaje, drip yaɗaura masa bayan yayi masa wasu allurai guda biyu wanda zasu taimaka wajen kawar da zazzaɓi da kuma ciwon da kansa keyi masa uwa uba kuma su sanyasa bacci, saboda idan yana a cikin hayyacinsa bazai taɓa barin zuciyarsa ta huta ba, yin hakan kuma shike ƙara sawa ciwon yayi tsanani… Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Dr.Bilal yagyara tsayuwarsa haɗe da duban Alhaji ma’aruf,, bayani yashiga yimawa Alhaji Ma’aruf ɗin sosai agame da ciwon Zaid ɗin. Bayan sun kammala maganan ne Alhj Ma’aruf yakoma wajen Zaid da tuni wani baccin wahala yasake ɗaukansa……
Rana bata ƙarya, ranar yau takasance laraba kuma yautake kamun Amarya, tun da safe gidan su Zahrah yake acike ƴan uwan Inna sun tattaro ƙwansu da ƙwarƙwatansu sun garzayo, don haka tuni gida yaɗauki hargowa da hayaniyan mutane yayinda amarya kuwa tunsafe take ƙunshe a ɗaki acewarta cikinta ne keyi mata ciwo,, Husnah da Suhaima ne suka taimaka wajen ɗebe mata kewa ta hanyar zama da’ita…..
Ƙarfe uku na yammaci kenan amma tuni gidansu Zahrah ya ɗinke da mutane, ciki kuwa hadda ƴan matan school ɗinsu wanda Husnah ce ta gayyacesu, domin ita dai Zahrah bata da wasu ƙawaye Husnah ce kaɗai ƙawarta… Kowacce ka kalla acikin ƴan matan nan tasha kyau cikin kayan anko ɗinta. Husnah ce tsaye akan Zahrah tana ta faman ɓaɓatu akan cewa Zahrah’n ta tashi su tafi shagon meckup domin tuni Dr.Sadeeq yaturo freinds ɗinsa waƴanda zasu kaisu shagon yin meckup ɗin suna ma jiransu aƙofar gida,, ita dai Zahrah yau jitayi gaba ɗaya bakinta ya mutu sambatajin wani kuzari ajikinta. Kayan da zata sanya da duk wani abun da zatayi amfani dashi, Husnah ta ɗaukar mata haɗe da kama hanunta suka fice daga cikin gidan. Wasu haɗaɗɗun motoci suka shiga kai tsaye aka wuce dasu wani shahararren shagon meckup….