SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwalliya sosai shahararriyar meyin meckup ɗinnan ta tsantsarawa Zahrah akan fuskarta lokaci ɗaya saiga Zahrah ta sauya kamanni asalin kyawunta yasake bayyana tamkar wata balarabiya ita kanta Zahrah saida tayi mamakin ganin kanta, tabbas dabadan tasan ita ɗin ceba, to da sai tace sanja mata fuska akayi, kowa yaga kwalliyanta saiyayi santi saboda tasha kyau iya kyau.. Wani doguwar rigan leshi me kyau da tsada ta sanya ajikinta, take kyakkyawar surar jikinta ya bayyana kansa acikin kayan, sosai ɗinkin yayi kyau yakuma amshi jikinta, zama tayi aka tsantsara mata haɗaɗɗen ɗaurin ɗankwali akanta, yayinda aka nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyar kanta, ita dai tsayawa tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata, daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma ɗan karamin fos ɗin dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones ɗin kayanta suka kasance farare, lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haɗe da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga ɗaukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka ƙaraso don ɗaukar ƙawayen amarya,, duka ƴan matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaɗai saboda Ango yace shi dakansa zaizo yaɗauki amaryarsa… Ƙawaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma ƙara,, murmushi tayi haɗe da kallon Zahrah adai dai lokacin da taɗaga wayar takara akan kunenta, “To ranka shi daɗe gamunan fitowa” abun da Husnah tafaɗa kenan haɗe da miƙewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haɗe da miƙar da’ita tsaye..
“Angonki yaƙaraso yace nafito masa dake” murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta ƙasa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan ƙasa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaɗan ƙamshin turare,, gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau ɗin..
Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuƙar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili….. Har Husnah ta buɗe murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai ɗauke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta, kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe ƙawatuwa.. A hankali ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunsa,,, Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana me wasa da yatsun hanunta,, Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin…
“Zahrah!” Dr.Sadeeq yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauƙar da nutsuwa. Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluɓeta.
“Kinyi matuƙar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa’a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!”
Sai alokacin Zahrah ta ɗago kanta, haɗe da sakar masa ƙawataccen murmushi, jiyayi gaba ɗaya ta kashesa da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da’ita haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya riƙesu gam acikin nasa, wani irin soyayyartane yaji yana ƙara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa ya rungumeta kozai sake samun nutsuwa acikin zuciyarsa…. Harsuka iso katafaren hall ɗin daya cika maƙil da jama’a zuwan amarya da ango kawai ake jira, amma Dr.Sadeeq bai ɗauke idanunsa akan abar ƙaunarsa ba, wani abun daya ƙara rikitar da Zahrah takasa cewa dashi komai shine yanayin yanda yake mata magana da wata irin murya me sanyi… Motarsu na’isowa wajen taron, mc yasoma shela cewa ga ango da amarya sun ƙaraso, take guri yasake ɗaukan shewa yayinda kowa yazura idanun ganin ango da amarya, waƴanda suka zo wajen dan gulma suka sake miƙa wuya musamman ma familyn Dr.Sadeeq wanda anriga da angama gayamusu cewa amaryan ƴar matsiyata ne saboda haka suka baza idanuwan ganin ta don kashewa idanuwansu ƙwarƙwata…. Habeeb ne ya buɗewa Dr.Sadeeq ƙofar motar yafito, yayinda shikuma Dr.Sadeeq da kansa yazagayo ya buɗe mawa Zahrah nata ƙofar,,, cikin nutsuwa ta zuro ƙafafunta waje, kafun daga bisani tafito daga cikin motar, hanunta ɗaya Dr.Sadeeq yakama suka soma taku cike da nutsuwa,, wajene yaɗauki shewa masu murna nayi masu baƙinciki ma sunayi, haka masu ɗaukar amarya da ango hoto da vedio’s ma duk sunayi,, gaba ɗaya family’n Dr.Sadeeq ƙamewa sukayi ƙam ganin kyawun amarya ya tsoratasu sosai, saboda basu taɓa tunanin haka zasuga amaryan ba, sunyi tunanin zasu ganta wata almajira da’ita amma kuma sai suka ga saɓanin tunaninsu, lallai ba’abanza ba Dr.Sadeeq ya liƙe akan cewa shi dole sai’ita, takai takuma cancanci ayi mata fiye da haka ma… Har amarya da ango suka ƙarasa mazauninsu mutane basu daina yimusu vedio’s ba, haka kuma idanu bai ɗauke daga kan suba………
(Bazan’iya cigaba da typing ɗinnan ba, saboda banaso ayi bandani domin nima yau zantaka rawa sosai???????????????? idan kamu ya kammala zan cigaba da typing???????? Team Zaidu muna tare iya wuya????, Team Dr.Sadeeq kuna cikin ƙalbina asahun farko ma kuwa????)
12/January/2020
Follow me on Whatsapp and Wattpad
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 86 to 87
Sunkuyar dakai ƙasa Zahrah tayi gaba ɗaya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taɓa shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron, ba abun dake damunta kamar yanda idan taɗaga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waƴanda suka santa haddama waƴanda basu santa ba,, matso da kansa yayi kusa da’ita haɗe da kawo bakinsa wajen kunnenta “Anan ma kunya zaki nuna?” ƙasa ƙasa yayi maganar. satan kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi amma kuma batace dashi komai ba, haka dai masu yin vedio suka ci gaba da ɗauka yayinda….. Hmmmm kamu dai yayi kamu yakuma ƙawatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a ɗari ɗari takeyinsa, abu biyune suka haɗe mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taɓa zuwa irin waƴannan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai, su Husnah sunyi rawa sosai sun raƙashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata’iya ba gaba ɗaya nauyi da kunya sun hanata sakat…. sai gab da magrib aka tashi daga kamu kowa yasamu abun arziƙi ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka… Yanzu kam mota ɗaya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban… Jingina bayanta tayi da kujera haɗe da kwantar da kanta akan kafaɗan Husnah, duk hiran da Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC’n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaɓi, haka dama ita take matuƙar ta shiga hayaniya to kanta sai ya ɗanyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita ɗanyi zazzaɓi.. Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi… Fitowarta a wanka kenan, sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..