NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wai ke da waye ne haka?  a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da’alama dai munsamu ƙaruwa” Zahrah tafaɗi maganar cikin sigar tsokana… Dariya Husnah tayi haɗe da ɗage giranta sama.    “Ƙwarai kuwa tawan, wallahi ɗazu na haɗu da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai”

Dariya Zahrah ta sanya haɗe da neman guri ta zauna akusa da Husnah haɗi da kwantar da kanta akan kafaɗan Husna’n….

“Husnah kinsan ya so yake?”  tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..

Mamaki tambayar da  Zahrah tayi mata  ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba…

“Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa  bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!” Husnah tafaɗi haka tana me wasa da wayar hanunta, da’alama sunan Yazeed kaɗai da ta ambata yasanyata cikin shauƙi..

Ajiyar zuciya me ƙarfi Zahrah ta sauƙe haɗe da ɗago kanta daga kan kafaɗar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da  Husnah “Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so?  sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take ƙoƙarin sake son wanda yacutar da’ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta”

Kallon mamaki haɗe da ɗaurewar kai Husnah tashiga yi mawa Zahrah, ƙwarai itakam maganganun Zahrah sun sanyata a duhu me Zahrah take nufi?

“Banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zanfi fahimta idan har kika warware maganar tazama abu guda, amma kuma ni a ganina  babu amfanin  zuciyar da zata so wanda baida amfani a wajenta, sai dai kuma amma kinsan shi so wani zubin yakan makantar da komai naka ne tahanyar da baka isa kayi yaƙi dashi ba, amma kuma shi so kala kala ne, kowani so da’irin ƙarfinsa haka kuma da irin rauninsa, wani son yana fita, wani kuma sai ahankali zai fita, wani kuwa baya taɓa fita har gaban abada, amma shi wanda baya fita har abada shi ake ƙira da ƙauna, ita ƙauna kuma idan zafinta yatashi ƙona ka, to  ƙunan yakan kasance me tsananin zafi da raɗaɗi bakamar na so ba,   ina fata dai Ƙaunar Doctor ce tasanya kikamin wannan tambayar?” Husnah tafaɗi haka tana murmushi.. Wasu siraran  hawayene suka silalo daga cikin idanun Zahrah zuwa kan ƙuncinta.

“Zahrah kuka kuma?” Husnah tatambaya cike da mamaki domin ita sam bataga abun kuka  acikin maganar da sukeyi ba, hasalima ita Zahrah’n ce tafara ɗago maganar ba wai ita ba.

Hanu tasanya ta share hawayenta haɗe da sakin murmushi,  “Bakomai Husnah kawai dai idanuna ne tunɗazu sukeyimin zafi, kinsan ban saba da irin wannan kwalliyar da akamin ba, bacci ma nakeji bana ɗan kwanta, idan kingama ki rufe mana ƙofa” Zahrah tafaɗi haka fuskarta ɗauke da murmushin dole..

Har Zahrah  ta kwanta Husnah bata ɗauke idanunta daga kanta ba,  sosai ganin hawayen Zahrah’n yabata mamaki duk da kuwa cewa tana lure da’ita a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya acikin damuwa take wuni, amma gudun kada ta dameta da tambaya yasanyata sharewa bata tambayeta ba, amma tasan damuwa kam akwai shi jingim acikin zuciyar Zahrah…

Kusan mintuna talatin hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma kuma ko kyakkyawan motsi taƙi tayi gudun kada Husnah ta fuskanci cewa batayi bacci ba,, bazata taɓa bari kowa yasan damuwarta ba, ta yarda ta amince zata haɗiye duk wani damuwarta acikin rai da zuciyarta ita kaɗai, koda kuwa damuwartata zata kasheta,  tabbas wannan abun da takeji ba abu bane wanda zai ɓoyu ba, amma kuma zatayi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta maidashi ɓoyayyen sirrinta a haka har baccin gajiya ya ɗauketa, tana bacci babu jimawa kuwa ƙiran Dr.Sadeeq yashigo cikin wayarta, ganin ya nace da ƙiran ne yasanya Husnah ɗaga wayar ta shaida masa cewa Zahrah tayi bacci, to kawai yace haɗe da ajiye wayar..   
Wani irin tausayinta ne yaji ya dirar masa acikin zuciyarsa, hakanan yaji yau soyayyarta yasake shiga zuciyarsa fiye da ko yaushe  yayinda tausayinta yakuma ɗarsuwa acikin zuciyarsa, yaso jin muryarta acikin wannan daren amma kuma hakan baisamu ba, haka yashare yashiga cikin abokansa suka cigaba da  sabgoginsu…… 

Kafe cak idanunsa  suke akan haɗaɗɗen zanen POP’n dake mamaye saman ɗakin wanda aka ƙawatasa da ado me matuƙar burgewa, a hankali yake fitar da numfashi me zafi daga cikin hancinsa,, ahalin yanzu ba ciwon da yakeji bane damuwarsa, yafi damuwa da ganin  Zahrah’nsa fiye da komai,  yanzu kenan saura kwana uku a ɗaura mawa Zahrah’nsa aure da wani bashi ba,   rumtse idanunsa yayi da sauri haɗe da haɗiye wani irin yawu me ɗaci daya tsaya masa a maƙoshi, abu kamar wasa saiga ƙwalla suna gangarowa daga cikin idanun Zaid,  hanu yasanya yashafa gefen fuskarsa inda yaji sauƙar ɗumin wani abu kamar ruwa,,  ruwan hawayen daya fito daga cikin idanunsa ya lakato ahanunsa koda yaga cewa hawayene ke fita daga cikin idanunsa sai yasaki wani irin murmushi me matuƙar ciwo,  rayuwa kenan babu yanda bata juyawa bawa, watarana kaga me kyau watarana kuwa kaga mummuna, ƙaddara kenan babu tayanda bata zuwarwa bawa, haƙiƙa SO babban cutane ga bawa musamman idan baka samu abun da kakeso ɗin ba, tabbas ya jarabtu domin ko a iya haka Allah yabarsa ya horasa horo mafi tsanani ma kuwa,   tabbas Zahrah itace rauninsa, rasata kuma shine abu wanda zaifiye masa komai ciwo acikin rayuwarsa, baisan wani irin zazzafar soyayya yakeyiwa Zahrah ba, ashe tun dama yaudaran kansa yayi  ba sha’awarta yake ba sonta yake, amma kuma saboda wani banzan tunani da kuma banzar hujjan sa yasanya ya kasa yarda da hakan,  idan yace zai  misalta irin tarin yawan nadaman da yayi kawo daga randa ya yiwa Zahrah fyaɗe  zuwa yau to tabbas yayi ƙarya, ya cutar da’ita, ya zalunceta, tabbas yasan bai kyauta mata ba, sannan kuma baiga laifinta da ta ƙishi ba tabbas shida kansa ya san cewa bai cancanci ta sake yarda dashi ba,  saurin rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hannayensa da ƙarfi, bakomai ne yasanyasa yin hakan ba  face tunowa da yayi  lokacin da idanunsa suka rufe ya shigeta da ƙarfin gaske yanajin wani irin ihun da tayi amma saboda bushewar zuciya irin tasa haka bai saurara mata ba,,  kansa yashiga duka da hannayensa biyu kamar mahaukaci, ihun da Zahrah keyi masa alokacin da zai keta mata haddine yashiga dawowa cikin kunnuwansa ji yake tamkar alokacin ne abubuwan suke faruwa,,,  ihu yashiga yi batare daya sani ba, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu,   Mum da shigowarta falon nasa kenan taji ihun Zaid na tashi daga cikin bedroom ɗinsa, cikin sauri hartana haɗawa da tuntuɓe tanufi ɗakin nasa,, kwance tagansa akan gado yaɗaura duka hannayensa akansa yana wani irin ƙara tamkar wani wanda aljanunsa suka tashi..

“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, Zaid! Zaid!!” Mom taƙira sunansa cikin matuƙar ruɗewa,,   girgiza sa Mum tashiga yi  cike da ruɗewa sunansa kawai take ƙira, a tunaninta Zaid ɗin nata ya haukace ne, yanajin muryar Mom ɗinsa acikin kunnensa yatashi a zabure haɗe da faɗawa cikin jikin mahaifiyartasa,  abun mamaki saiga Zaid nan na kuka tamkar wani ƙaramin yaro, ita kanta Mum kasa motsi tayi haka ta tsaya kamar statue, wai da gaske Zaid ɗin tane wannan, kuka fa yake, anya kuwa ba aljanune suka shiga mata jikin ɗa ba?.
“Zaid” Mum takuma ƙiran sunansa cikin murya me sanyi domin kuwa itama tuni ƙwalla harsun cika mata ido…   “Please help me Mum, i don’t want to lost her!”  abun da Zaid ke faɗa kenan yana kuka,,  mamaki marar misaltuwa ne yakuma kama Mum  wannan wace irin masifa ne ya ruski Zaid wace irin tsinanniyar soyayyace wannan datake shirin haukata mata yaro? lallai yazama dole tayi wani abu, bazata taɓa bari tanaji tana gani ɗanta ya rasa ransa akan wata ba, wai dama ashe haka so yake? idan kuwa haka so yake to sai dai muyi fatan Allah yarabamu dayin so me tsanani….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button