SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kansa mum tashiga shafawa ahankali cike da tausayawa tace “Ka kwantar da hankalinka Zaid, kayi haƙuri kasamawa kanka nutsuwa, badai kana sonta ba?”
Kai Zaid ya kaɗa tamkar wani ƙaramin yaro.
“Insha Allahu zata zamo taka, zaku rayu da’ita rayuwa ta har abada, kadaina damun kanka kaji my son!”
Mum ta ƙare maganar cike da lallashi..
Kansa ya kwantar akan kafaɗan mahaifiyartasa lokaci ɗaya yashiga sauƙe ajiyar zuciya irin dai yaro ƙarami yayi kuka ya ƙoshin nan…. Bayansa Mum take shafawa a hankali sai gashi cikin mintunan da basufi 10 ba Zaid yasoma fidda numfashi a hankali cike da nutsuwa da’alama dai bacci ne ya ɗaukesa, Mum tana tabbatar da cewa Zaid ɗin yayi bacci ta tattaro duka ƙarfinta haɗe da zameshi akan kafaɗanta ta kwantar da kansa bisa kan pillow’n sa haɗe da ja masa bargo ta rufeshi, kallon fuskarsa Mum tashigayi cike da tsananin tausayinsa, tajima tana kallonsa kafun daga bisani tayi masa addu’a ta shafa masa akan fuskarsa, cikin sanyin jiki ta tashi tafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni……
Washe Gari
Tun safe kwararriyar me zanen lalle wanda Dr.Sadeeq ya ɗaukarwa su Zahrah bayan yabiyata maƙudan ƙuɗaɗe tazo gidan,, zanen jan lalle me matuƙar kyau aka tsantsarawa Zahrah akan hanu da ƙafarta, abunka da farar fata take zanen jan lallen yafito akan fatarta yayi kyau sosai,,, lokacin da ta wanke zanen lallen nata hakanan ta tsinci kanta da sakin murmushi ita kanta sosai zanen yayi mata kyau gashi ya ƙara ƙawata farar fatarta gwanin sha’awa. Wayarta dake ringing ta ɗauka haɗe da karawa akan kunnenta, cikin wata irin kasalalliyar murya taji yace “Amaryata” murmushi tasakar masa me sauti haɗe da cewa “Umm” Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa yagyara zama haɗe da cewa “Ki ɗan bani aron minti 10 daga cikin lokutanki na yanzu inason ganinki” ya ƙare maganar yana wani lullumshe ido kamar wanda yake a gabanta. Ajiyar zuciya Zahrah tayi haɗe da cewa “Gani nan zuwa” tana aje wayar ta ɗauki wani haɗaɗɗen mayafi wanda aka masa ado da fararen duwatsu ta yafa ajikinta yayinda haɗaɗɗen gashinta dayasha saloon ya bayyana kansa ta cikin mayafin..
Tana fitowa tsakar gida ta kalli Husnah wacce yanzu ake zana mata nata lallen, murmushi tayi mata haɗe da kashe mata ido ɗaya, dariya suka sanya su duka domin sukaɗai suka san ma’anar hakan…. Murmushi yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya alokacin dayaga fitowarta daga cikin gida,,, buɗe murfin motar tasa tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama,, cikin murya me ɗauke da kasala ya amsa mata sallaman haɗe da maida kallonsa gareta. Murmushinta dake ƙara mata kyau akoda yaushe tayi masa haɗe da ɗan tsaida idanunta akansa,,,, shiɗinma kallonta yake batare dayace komai ba, azuciyarsa kuwa mamakinta yake ta yanda ta’iya tsaida idanunta akan sa a yau ɗin, bayan kuma yasani sarai batayi masa dogon kallo.
“Namiki kyau ne ƴan mata?” yatambayeta yana me duban kansa,, dariya ne ya kwace mata amma kuma saitayi saurin sanya hanu ta toshe bakinta,
“Wow! gaskiya wannan zanen lallen yayi kyau sosai!” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin kamo hanunta, sam shi bai lura da zanen bama sai yanzu,, saurin maida hannayenta cikin mayafin dake jikinta tayi haɗi da cewa “Sai an biya kuɗi me yawa sannan ake kallon wannan zanen” murmushi yayi me sauti, ba ɓata lokaci ya sanya hanu acikin aljihunsa, kuɗi yaciro wanda baisan ko nawa bane, ya ɗaura mata akan cinyarta.
“Karki hanani gani please” yafaɗi maganar yana me marairaice fuska,
“Naƙi wayon kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan” tafaɗi haka cikin sigar wasa.
“Laluma aljihunsa yayi dama da hagu amma kuma yaji babu ko sisi, kawai saiya marairaice idanunsa yana kallonta, dariya yanzu kam tashigayi, sai da tayi dariyarta ta ƙoshi sannan tace “Kasan baka da kuɗi kuma kakeson ganin zanen lallena?”
Jin shiru bai bata amasa ba yasanyata saurin ɗago kanta ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata idanu kamar wani wanda bai taɓa ganinta ba, murmushi kawai tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sosai takejin wani iri ajikinta idan yana kallonta.
“Zahrah na!” yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi. Zahrah bata iya amsa masa ba, sai dai ta dawo da kallonta gareshi..
Yabuɗe baki zaikumayin magana kenan wayarsa tasoma ƙara,,
“Hajiya”
shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, dakatawa da maganar yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.. Hajiya dake zaune akan kujera cikin yanayi na ɓacin rai tace
“Kana’ina ne?”
“Ina wajen Zahrah Hajiya” yabata amsa cike da girmamawa.
“Kabar duk abun da kake kazo gida inason ganinka” tana kaiwa nan azancenta ta kashe wayar.
A hankali ya zame wayar daga kan kunnensa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya kallon Zahrah yakumayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
“Hajiya nason ganina yanzu, ki riƙe wannan saboda hidimar walimanki na gobe, maybe bazaki sake ganina ba sai bayan na angonce!” yafaɗi haka yana me miƙa mata wasu kuɗaɗe masu yawa daya ciro daga cikin wata ƴar loka dake cikin motar.
“A’a ae bana buƙatar komai don mungama duk wani abun da zamuyi, kuma komai na walima yazama ready, sannan kuma inada kuɗi a wajena ka….”
“Shiiii kinsan banason yawan musu please ki karɓa kinji baby na, ki ajiye kobazakiyi komai dasu ba nasan zasu miki amfani wani lokaci” yafaɗi haka ta hanyar katseta daga maganar da takeyi batare daya bari ta ƙarisa ba,, badon ranta yasoba ta amshi kuɗin haɗe dayi masa godiya kana ta buɗe murfin motar ta fice, shima tada motar nasa yayi yabar ƙofar gidan, zuciyarsa cike da mamakin ƙiran da Hajiya tayi masa, Allah dai yasa ba wata matsalan ne takuma kunnu kai ba, idan dai har akan aurensa da Zahrah ne tofa shikam gaskiya sai dai kowama yayi haƙuri saboda ayanzu baijin zai iya sanja muradin sa…
Fuska ɗauke da mamaki Dr.Sadeeq ke cewa “tafasa aurena kuma Hajiya?”
“Badole tafasa aurenka ba, wace uwa ce zata yarda da irin abun da katsiro dashi? tun ma ba’aje ko inaba kana nuna banbanci ƙarara, gashi abanza ka jawo zubewar mutumcin dake tsakanina da Hajiya Furaira, yanzu da wani ido kakeso nasake kallonta!” Hajiya tafaɗi haka cikin ɓacin rai.
Sunkuyar dakai ƙasa Dr.Sadeeq yayi yana me hamdala acikin zuciyarsa da aka soke batun aurensa da Saleema, dama shi Allah yasani ko ya auri Saleema ba lallaine yakamanta mata adalci ba, saboda abun a bayyane yake yafi ƙaunar Zahrah fiye da kowacce mace a yanzu idan aka cire mahaifiyarsa dakuma ƴar uwarsa ta jini.
“Dama haka kakeso ai shikenan burinka yacika, gakuma kayan lefe dakuma kuɗin auren da kakai can sun dawo maka dashi, sai kaje kayi ta fama da wacce zuciyarka ta zaɓa ma ni tashi kabani waje !”
Sumi sumi haka Dr.Sadeeq yatashi daga gaban mahaifiyartasa cikin sanyin jiki yafice daga cikin falon…
Yana shiga ɗakinsa yasaki wani irin ajiyar zuciya, wayyo Allah shikam daɗi kasheshi, dama yafi kowa tunanin yanda zaman nasu zai kasance saboda shi a tsarin rayuwarsa bai da niyar auren mace sama da ɗaya bare yanzu daya samu Zahrah yasan cewa ita kaɗaima ta’ishesa rayuwa, yaji daɗin fasa wannan auren ƙwarai…