SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana shiga cikin gida Inna tayi yo kanta tana washe baki, sakamakon ganin leda da tayi ahanun Zahrah, wafcar ledan Inna tayi haɗe da cewa “ɗan albarka yaukuma mai yakawo mana ?” kwalin danƙareriyar iphone 11 pro max Inna tafara cirowa, a je kwalin tayi a gefe haɗe da zazzage ledan a ƙasa, kayan snacks dasu choculate ne suka zubo, saikuma mai gayya mai aiki wato farare bugun Abuja, dariya Inna tayi haɗe da buga shewa, itakam Allah yakashe ya bata, lokacin yin arzikinta yayi,, jin shewan Inna yasa Baffa dake cikin ɗaki fitowa, “lafiya kuwa…. ” kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen da ke gaban Inna da yayi……..
(Readers maikuke tunanin zai wakana tsakanin Zaid da Zahrah ? Zahrah zata amince da soyayyar Zaid kuwa ? kokuwa zata ɗauki Jabeer ne tabar Zaid ? kuci gaba da bibiyata don sanin mai zai faru anan gaba…)
19/October/2019
MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written by*
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Lovely Brother Khabeer
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*WATTPAD*
@fatymasardauna
Editing is not allowed ????
Chapter 12
( INA MAI BAKU HAƘURI DOMIN KUWA KWANA BIYU, ZAKUJINI SHIRU BA NEW UPDATE, WATA ƘILA NAYI 1 WEEK BANYI TYPING BA, WATAƘILA KUMA BAZAN KAI HAKANBA, HAKAN YAFARU NE SABODA WANI DALILI NAWA, INSHA ALLAH AMMA ZAKUCI GABA DA JINA IDAN KOMAI YA DAI DAI TA, NAGODE….)
Kuɗanyi manage da wannan ????????
Kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen dake gaban Inna da yayi, cike da tuhuma yake kallon Inna yamakasa ce da’ita komai, ganin haka yasa Inna ta washe baki, haɗe da soma tattare maƙudan kuɗaɗen, cikin hanzari Baffa yasanya hannayensa duka biyu ya wawashi kuɗin, haɗe da cusawa cikin aljihunsa, da sauri Inna tayo kansa tana muzurai, haɗe da cewa “Haba Malam yazakayi haka, aidai katsaya nayi maka bayani kafun ka kwasa rabonka ko” harara Baffa ya watsamawa Inna haɗe da taɓe baki yace ” ba abun da bansani ba, nasan duk wani abu dakike shiryawa, kuma wallahi daga yau idan aka sake kawo kuɗi cikin gidannan ba ki jira dawowata munraba ba, ninasan matakin da zan ɗauka, yarinyace dai ƴar wa na ne, don haka babu wanda ya’isa ya gwadamin iko da’ita, kuma shima saurayin zaizo yasameni haka ake zuwa hira babu wani tambayar izini ba komai” Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar fita daga gidan, yana fita Inna ta buga tsuka haɗe da cewa ” shikenan kuma ae tunda yagano abun danake shiryawa, bazai taɓa barina naci arziki ni ɗaya ba, mcheeew !” taƙare maganar tana mai tattare ƴan ragowan kuɗaɗen da Baffa ya bar mata, raba snacks ɗin biyu tayi taɗauki rabi, yayinda tabarmawa Zahrah rabi, waya kuwa danƙamawa Zahrah abunta tayi, domin ita keypad ma bawani iyata tayi ba, balle kuma shafa shafa (touching screen)… Jigum haka Zahrah tayi zuciyarta cunkushe take da tarin tunani kala kala, da zaran ta kulle idanunta, mood ɗinsu na ɗazu ne ke faɗo mata, wanda hakan yasanya takejin gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, batasan dame zata ƙira wannan yanayinba, saboda batasan ma da akwaishi acikin duniyar nan ba, duk dacewa bawani abune yashiga tsakaninsu ba, amma kusancin da sukayi da juna duk ya dagula mata lissafi, ga fitinannen ƙamshin turarensa daya kama jikinta, tamkar wacce tayi wanka da turaren,daga wani ɓangare na zuci yarta kuwa kaico takeyi da mummunan hali irin na Inna da Baffa, wato su baruwansu da koma waye zaizo wajenta, sudai kawai abasu kuɗi suka sani, koda ma iskanci takeyi su baidame su ba kuɗi kawai suke so, haƙiƙa rashin iyaye babban matsalane arayuwar ƴa mace musamman ma idan batayi dace da iyayen riƙo nagari ba, sai kuga rayuwarta nashirin lalacewa, akan abun da bai kai yakawo ba, Allah ka zama gatan mu aduk inda muke Ameen,,, a hanakali taciro wayar daga cikin kwalinta, subahanAllah shine abun da tafurta lokacin da’idanunta suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar wayar, jikin wayar ma kaɗai abun kalloce balle kuma kakai ga shafata, tabbas idan baza ta mantaba, wannan wayar itace wacce taji ƴan school ɗinsu na magana sabuwar fitowa ce, kuma burin kowanni ɗan gata da ƴar gata, shine su mallaki wayar, domin kuwa aƙalla kuɗinta zaikai dubu ɗari biyar da tamanin,, wani irin faɗuwar gaba taji ya shiga zuciyarta a lokaci guda, take kuma mugun zargin Zaid ya ɗarsu acikin ranta, tabbas akwai abun daya ɓoye acikin zuciyarsa, amma idan ba haka ba babu yanda za’ayi yasiya mata wayan dubu ɗaruruwa, batare da suna da wani kyakkyawan alaƙa atsakaninsu ba, a maimakon ta kunna wayar kamar yadda ya umarce ta, batayi hakan ba saima mai da wayar tayi cikin kwalinta haɗe da cusata cikin kayanta, taƙudura acikin ranta cewa idan yasake da wowa zata mayar masa da wayarsa, domin ita bata kai martaba da ƙimar da zata riƙe wannan zuƙeƙiyar wayarba,, sam bacci ya ƙaurace mawa idanun Zahrah kalaman Zaid ne ketayi mata yawo acikin kunnu wanta, bama kamar kalmar INASONKI ZAHRAH daya faɗa, gaba ɗaya zuciyar Zahrah kasa sukuni tayi a wannan dare, da ƙyar bacci ɓarawo ya ɗauketa……
Zaid kuwa yana barin unguwar su Zahrah guest house ɗinsa ya nufa, sai dai yau ba ya tare da kowacce karuwa, yana shiga cikin bedroom ɗinsa yasoma rage kayan jikinsa, saida yacire duk wani kaya dake jikinsa, kafun ya ɗaura towel a ƙugunsa kaitsaye ya shige bathroom,, a ƙalla ya kwashi kusan 1 hour a cikin bathroom ɗin kafun yafito, sanye da rigar wanka a jikinsa, gaban mirror ɗinsa yaje ya ɗanyi shafa, combat jeans black ya sanya haɗe da black t-shirt, sosai kyawun Zaid ya bayyana acikin wannan kayan, wayarsa kawai ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, makeken friedge glass ɗin dake cikin katafaren falon nasa yanufa, zuƙeƙiyar kwalbar wine mai tsadar gaske yaɗauko a cikin friedge ɗin haɗe da glass cup zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yayinda ya buɗe kwalbar wine ɗin ya tsiyaya a cup, kana yakai bakinsa, a hankali yake shan wine ɗin, yayinda idanunsa ke alumshe, bakomai yake hasa sowa ba sai kyakkyawar surar Zahrah wacce ke tafiya da imaninsa ako da yaushe, haƙiƙa ya kamu da tsananin sha’awar Zahrah, kuma alƙawari yaɗaukar mawa kansa idan dai har yacika SHU’UMIN NAMIJI kamar yadda abokansa ke ƙiransa, to sai ya keta mawa Zahrah rigar mutumcinta kota wani hali kuwa,, wayarsa yaɗauka haɗe da laluɓo numbern sim ɗin dake cikin wayar Zahrah, yana dialing aka sanar dashi cewa wayar a kashe take, wani irin munafukin murmushi Zaid yayi haɗe da sanya hanu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa, kashe idanunsa ɗaya yayi haɗe da cewa “My Sugar Baby bakijin magana ko ?” yayi maganar tamkar wanda yake gabanta,, sosai Zaid ya sha wine a wannan dare, da ƙƴar ma yasamu bacci ya ɗaukesa bayan yagama kwarara aman giyan da yasha …….
21/October/2019
*MRS SARDAUNA*
????????????????????????????????????????
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*WRITTEN by*
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated to my lovely brother Khabier
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*WATTPAD*
@fatymasardauna
Editing is not allowed ????
{{ Dan Allah kuyi haƙuri, kubarni na cigaba dayin littafina a yanda natsara, banson ƙorafi kokuma cece kuce, haka labarin Zaid da Zahrah yake, bakuma zan sauya ba, baikamata ace tun bakuji mai zai wakana gaba ba, kunsoma yanke hukunci, inyi kaza kar inyi kaza, kada Zaid yayi kaza, ????????♀ Please kudaina haka ba daɗi, inaso kusani a yanda na tsarashi ahaka zanci gaba da tafiya dashi, babu wani kwana kwana, kuma abu na farko da nakeso ku fara sani shine, kowa a duniya da irin tasa Ƙaddarar, so komai kuka gani sai ku ɗaukeshi a matsayin ƙaddara....}}