NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaid

Gaba ɗaya jikinsa yaƙi daɗi duk yanda yaso koda a daddafene yaje yaga Zahrah hakan yagagara, saboda wunin yau ma gaba ɗaya  baiyishi cikin daɗi ba, kasancewar ciwon zuciyarsa yatashi yasanya Dr.Bilal ya dinga basa magani masu sanyasa bacci gudun kada ya matsantawa kansa  da tunani, haka dai yanaji yana gani tashi zaune ma yagagaresa, haka ya kwana yana begen ganin Zahrah….

Friday

Kowa dake gidansu Zahrah shirin zuwa wajen walima kawai yakeyi, yayinda amarya Zahrah tasha kyau cikin wani haɗaɗɗen sari da aka ɓata lokaci wajen naɗa mata shi ajikinta,  yauma dai meckup aka tsantsara mata akan fuskarta nagani na faɗa, take fuskar amarya Zahrah yaci gaba da walwali,,  motoci Dr.Sadeeq yaturo suka kwashesu har zuwa inda za’a gudanar da walima,,,   walima fa ya ƙayatar saboda Malami aka ɗauko na musamman yagudanar da wa’azi akan yanda ake zamantakewar aure, sanan kuma yaƙara da wa’azi me ratsa jiki  harsaida amarya tayi  kuka,,  bayan anƙare walima ne kuma aka soma rabon abinci  haɗe da kyaututtuka kamar su memo da kuma jaka wanda Dr.Sadeeq ne duk yayi su, sai dai babu hoton amarya da ango ajiki sai dai sunansu kawai.  Walima fa yaƙayatar kowa sai dai yace Alhmdlh haka  aka tashi a taron walima kowa yanacikin farinciki,, yayinda gobe asabar  kuma take ɗaurin aure????.

(Maza kuzo fa, mata kuma ku faɗawa Mazajenku su je ɗaurin auren???? ????Nidai baruwana Team Zaid kada kuga laifina Dr.Sadeeq ne yace ingayyaci kowa da kowa ????????????)

       Fatymasardauna
????????????????????????????????????????

        SHU’UMIN NAMIJI !!

     Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            
           WATTPAD
    @fatymasardauna

(Wannan fejin baki ɗayansa nakine My KHAIR74  kinasani nishaɗi sosai, kiyi farinciki marar iyaka kiji daɗinki akullum inayinki sosai KHAIR74) 

Editing is not allowed????

NOTE: Masoyana masu cece kuce inagaisuwa agareku, sannan ina mai baku haƙuri, idan akwai wacce wannan hukuncin baiyi mata daɗi ba tayi haƙuri dama shi Aure nufine na Allah, kuma ance matar mutum ƙabarinsa, abun danakeso ku fahimta shine, balallai ne koda yaushe mutum yasamu abun da rai dakuma zuciyarsa keso ba,   SO baƙarya bane haƙiƙa so gaskiya ne, amma kuma bako da yaushe bane  burin so ɗin ke cika ba, ita rayuwa dama haka take tana iya sauyawa ako da yaushe akuma kowani lokaci…..

    CHAPTER 88 to 89

Yauma dai kamar jiya agajiye take matuƙa,  suna komawa gida ta yi wanka da ruwa me zafi sai alokacin ta ɗanji ta samu nutsuwa a jikinta.  Kwanciya tayi luf akan katifarta  haɗe da jawo wayarta tasoma buga game, tayi hakanne  gudun kada tunani ya samu daman bijiro mta acikin zuciya…

“Kinada baƙo a waje fa Zahrah” maganar da tafito daga bakin Husnah wacce shigowarta ɗakin kenan..

“Baƙo kuma Husnah?” Zahrah tatambaya cike da mamaki.

“Ƙwarai kuwa amma sai dai gaskiya inaga ba ya ɗaya daga cikin abokan Doctor, yakamata kije ki gansa dan naga kamar yamatsu dason ganinki” Husnah tafaɗi haka bayan tayi mawa kanta masauƙi akan katifar da Zahrah take kwance…

Cike da mamaki Zahrah tamiƙe tsaye haɗe da ɗaukar mayafi ta rufa ajikinta, hakanan taji  tamatsu da taga waye ne ke neman nata…..

Tana fita waje tasoma raba idanu ko zata hango wanda akace yana ƙiranta, sai dai kuma bata ga kowa ba…

“Zahrah” taji anƙira sunanta daga bayanta,, da sauri ta juya don ganin kowaye.

Wani kyakkyawan saurayi handsome guy tagani tsaye a bayanta yana ta zuba murmushi,  kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikekken ɗan gaye ne, kuma ɗan hutu, domin kuwa fatar jikinsa da kuma kayan dake sanye ajikinsa kaɗai sun isa tabbatar maka da hakan..

Takowa yashigayi  gareta, har saida yazo kusa da’ita kafun ya ja ya tsaya,  kallon kallo suka shiga yiwa juna,  Zahrah kallon mamaki da kuma al’ajabin me ya kawosa wajenta take yayinda shikuma yakeyi mata kallon ƙurilla,, wani yawu ya haɗiya a maƙoshinsa bayan yagama ƙare mata kallo daga samanta har ƙasanta…    “Zahrah ko?” yafaɗi haka yana me nuna ta da yatsarsa…

Kai kawai Zahrah ta’iya jinjina masa alamar “Eh” still amma kuma idanunta nakansa..

Murmushi yakuma yi mata haɗe da gyara tsayuwarsa  “Naji daɗin ganinki ƴan mata, sunana Abid, nasan baki sanni ba amma kuma idan babu damuwa me zai hana muje mota sai muyi maganan, saboda nazomiki da wata magana ce  me mahimmanci”  yafaɗi haka yana me sake dubanta da kyau…

Kallon sa itama ta sakeyi sosai kafun ta ce. “Kafaɗi duk abun da zaka faɗa anan inaji, amma bana buƙatar shiga cikin motarka” ta ƙare maganar tana me ɗage kanta sama.

Murmushi Abid yakumayi akaro na barkatai “lallai ba’a banza ba Zaid yakasa magance matsalarsa yarinyar akwai taurin kai” yafaɗi haka acikin zuciyarsa…

“I’m sorry bacutar dake zanyi ba, kada kiji tsorona, nazo miki da magana ne me matuƙar mahimmanci, nasan abune me wahala amma kuma keda kanki  zakiso ace kinzamo silar ceto rayuwar da take shirin gushewa, nasan bazakiso ace ta sanadiyarki Zaid ya rasa rayuwarsa ba,  kina da tausayi Zahrah, me yasa bazaki yarda ki aure sa ba?” abunda ya fito daga bakin Abid kenan..

Kallon baka da hankali Zahrah tashiga bin Abid dashi, da ƙyar ta’iya cewa   “Bansan maganar Zaid bace takawoka wajena ba,  da bantsaya ɓata lokacina wajen saurararka ba, don bazan ɓata lokacina abanza ba, dan Allah kufita a rayuwata, kacewa Zaid ya ƙyaleni  na huta, domin kuwa  ko maza sun ƙare a duniya bazan taɓa auren Zaid ba!” Zahrah tafaɗi haka cikin dakiya dakuma ɓacin rai…

“Ba gaskiya bane Zahrah, wannan maganar da kika faɗa ba daga cikin zuciyarki tafito ba daga bakinki tafito, kobaki furta ba raunin kalamanki sunnuna cewa kinason Zaid har yanzu, me yasa bazaki yafe masa ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, dan Allah Zahrah ki taimaka ki auri Zaid, haƙiƙa nida Zaid muna biyewa zuciyarmu muna aikata abunda baidace ba, amma kuma ina me tabbatar miki da Zaid ɗin dakika sani a yanzu bashine wanda kika sani ada ba, soyayyarki ta sanjawa Zaid tunani, soyayyarki ta juyamasa ƙwaƙwalwa, wallahi ke kaɗaice muradinsa acikin duniyar nan, Zaid baisan damuwa ba sai akanki Zahrah, yayi nadama me tsanani akan abun daya aikata miki,  akan ki Zaid yafara sanin menene ƙunci, akanki yafara sanin menene  ɗacin soyayya dakuma zaƙinta, haka akanki Zaid ya kasa fuskantar gabansa dakuma bayansa, akan kine kuma dalilinkine Zaid yakamu da ciwon zuciya me tsanani, ahalin yanzu Zaid yana acikin wani hali, Zahrah ke kaɗaice zaki iya sanjasa ki kuma ceto rayuwarsa please koba don nida Zaid ba kodan ceton rayuwarsa ki taimaka ki auresa!” Abid yaƙare maganar cike da raunin murya sosai yake matuƙar tausayin Zaid musamman ma dayaje yagansa yau, gaba ɗaya yafita hayyacinsa…

Murmushi me tsananin ciwo Zahrah tayi haɗe da sanya haƙoranta tacije lips ɗinta, kallon Abid tayi kana ta girgiza kanta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button