SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Meyasa ku kazamanto mutane masu tsananin son kansu? Zaid rayuwarsa kawai zai rasa, amma ni gani da raina ta sanadiyarsa ne kuma narasa farinciki na, rayuwata tazamo marar amfani a gareni, ya katsemin farinciki dajin daɗi na, yakawo kansa gareni alokacin dayaga dama, yakuma sanyamin soyayyarsa alokacin dayaga dama, sannan yakuma ketamin haddina alokacin da yaga dama, yayimini duk wani abu da ransa keso alokacin dayaga dama, nima kuma yanzu nadawo mutum zankumayi duk wani abun daya dace alokacin dana ga dama, idan shi ne ya aikoka da waƴannan yaudararrun kalaman to kaje kasanar masa cewa kalaman naku basuyi aiki akai na ba, zaifi kyau kubarni nayi rayuwar aurena cikin farinciki da salama, domin kuwa gobe iwarhaka najima da zama matar wani insha Allah, inaso kuma kasani cewa najima da barin Zaid da Allah, haƙiƙa ya cutar dani, amma kuma dama hakan yakasance rubutaccen ƙaddarata ne wanda Allah ya rubuta, kaje kawai Abid bana tunanin sake burin haɗa rayuwata da ta Zaid!” hanu tasanya ta sharce hawayen da suka silalo daga cikin idanunta haɗe da juyawa tasoma tafiya…
“Komai yana hanunki Zahrah idan har kikace afasa aurenki da wanda zaki aura aɗaura da Zaid nasan iyayenki zasu amince, shin maiyasa bazaki cika muku burinku ba? kinasonsa shima kuma yana sonki, ki amince ki aure sa, wallahi namiki alƙawari ko nawa kikeso aduniyar nan zan mallakamiki shi koda kuwa duka dukiyata kika buƙata nabaki zan baki, amma bazan tilastaki ba sai dai inaso kisani idan Zaid ya rasa rayuwarsa a yanzu kece SANADI” Abid yana kaiwa nan azancensa yabuɗe murfin motarsa, wata ƴar madaidai ciyar jaka ya ɗauko, takawa yashigayi harsai da yazo kusa da’ita kafun ya tsaya… “Ki amshi wannan jakan idan kika buɗe laptop ɗin dake ciki zakiga yanda Zaid ya koma A SANADI’N SONKI” Abid yafaɗi haka yana me miƙa mata jakar.. Tsintar kanta tayi da kasa ƙin karɓan jakar, yana bata jakar ya juya yayi tafiyarsa,,, har motar Abid ta ɓule Zahrah na tsaye sororo hanunta riƙe da jaka,,, saurin share hawayenta tayi, haɗe da nufar cikin gidan su,,, sumi sumi haka ta shige cikin ɗakinta, abun yayi mata daɗi sosai data iske Husnah hartayi bacci,, mayafinta ta cire haɗe da neman waje ta zauna, kanta ta kifa akan guiwowinta, damuwane cike azuciyarta, takasa sanin wani hali take ciki, kanta ta ɗago takalli jakar da tashigo dashi, da sauri tajawo jakar haɗe da buɗeta, a hankali ta zaro laptop ɗin dake cikin jakar, saida ta ƙarewa laptop ɗin kallo kafun ta buɗeta, tana danna wani madanni laptop ɗin takawo haske take kyakkyawan hoton fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin, mamakine yakamata ganin hotonta wanda batasan ma dashi aduniya ba, balle tasan yaushe ko wace ranace aka ɗauketa hoton ba, ƙurawa hoton nata idanu tayi tamakasa yin komai, bata ɗauke idanunta akan hoton ba har saida hasken screen ɗin laptop ɗin ya gaji dan kansa ya ɗauke.. Ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe haɗe da sake kunna laptop ɗin, batasan inazata shiga ba, bata kuma san mezata fara dubawa ba, hakanan ta ji zuciyarta ta ingizata da tashiga ɓangaren hotuna,, tana kutsawa ɓangaren hotuna, hotunantane suka farayi mata wellcome, mamakine yasake kasheta ganin hotunanta kaca kaca babu adadi acikin laptop ɗin, wanda ita a iya tsawon tarihin rayuwarta ma bata kasance mace meyawan sonyin hoto ba, yanzu haka ko hotonta ƙwaya ɗaya bata dashi acikin wayarta,,,, bata da me amsamata tarin tambayoyin dake ranta dan haka kawai saita shiga wuce hotunan nata, hotunan Zaid takuma cin karo dasu wanda saida gabanta yayi wani irin faɗuwa yayinda ƙirjinta yashiga dokawa da sauri.. da ƙyar ta’iya view ɗaya daga cikin tarin hotunan nasa, sanye yake da wandon jeans baƙi dakuma wata farar riga saikuma hular sanyi daya sanya akanshi yayinda kunnensa ke sanye da farin earpiece, yayi kyau matuƙa a hoton domin kuwa fuskarsa ɗauke take da wannan ƙawataccen murmushin nasa wanda yake ƙara masa kyau ako da yaushe… Ƙura mawa hoton nasa idanu tayi, saitaga tamkar shiɗinne da kansa agabanta, batasan sanda wasu hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan ƙuncinta ba,, tajima tana kallon hoton nasa, haka kuma hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta, ɓangaren vedios takuma kutsawa, sai dai vedion farko da ta gani shine wanda yakusa tarwatsa mata zuciya, yakuma ɗaga mata hankali,, Zaid tagani kwance akan gadon asibiti ansanya masa oxygen, yayinda aka dasa masa wasu ƙarafan na’urori akan ƙirjinsa dai dai saitin zuciyarsa, da badon ɗan abu kamar computer’n dake gefensa wanda shike nuna alama yana da rai ba, to tabbas da saidai ace dashi gawa,,, wani irin sarawa taji kanta yayi, yayinda wani irin kuka yazo mata alokaci guda, saurin sanya hanu tayi ta toshe bakinta haɗe da rumtse idanunta, a hankali ta jingina bayanta da bango,,, hawayene suka shiga gudu wani na koran wani akan fuskarta,, duk yanda taso daurewa kasawa tayi saikawai tafashe da wani irin kuka me sauti, kuka take sosai yayinda ta rungume wannan laptop ɗin akan ƙirjinta,,,, kamar amafarki Husnah kejin gunjin kuka natashi acikin ɗakin, dayake ita ba me nauyin bacci bace yasanyata buɗe idanunta ahankali, aikuwa dagaske ba amafarki bane, kukan Zahrah taji raɗau acikin kunnenta, da sauri ta tashi zaune haɗe da dawo da kallonta inda sautin kukan ke fitowa,, sake waro idanunta tayi ganin da tayiwa Zahrah na kuka tsakaninta da Allah. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Zahrah meyafaru kike irin wannan kukan?” Husnah ta tambaya cikin ruɗewa… Jin muryar Husnah acikin kunnenta yasanya, tataso daga inda take da sauri ta faɗa jikin Husnah ae kuma saita ƙara volume ɗin kukan nata,, kai Husnah ta dafe cike da tashin hankali, “Allah yasa dai bawani gagarumin abubane yafaru” Husnah tafaɗi haka acikin zuciyarta.
“Kiyi shiru dan Allah Zahrah, kinga dai yanzu dare ne sokike kowa saiyaji gunjin kukan ki? kiyi shiru kisanar dani meke faruwa” Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da damuwa… Yau Zahrah tsintar kanta tayi da kasa daina kuka, ji ma take tamkar Husnah ingizata take da ta ƙara volume,, sororo haka Husnah tayi ganin Zahrah taƙi daina kukan, zame ta tayi daga jikinta haɗe da nufar inda aka aje musu ledan ruwa na pure water, guda ɗaya ta zaro acikin ledan haɗe da fasawa ta tsiyaya acikin cup,, dawowa tayi ta zauna haɗi dakai kofin ruwan bakin Zahrah, babu musu Zahrah ta amshi kofin takai bakinta, gaba ɗaya ruwan dake cikin kofin tashanye tas haɗe da aje kofin agefe, ajiyar zuciya tasoma sauƙewa akai akai amma na kuka,,, kwanciya tayi luf haɗe da sanya hanu ta dafe kanta dake matuƙar sara mata,,, idanu kawai Husnah ta zuba mata tana me mamakinta, gaba ɗaya aƴan kwanakinnan talura Zahrah ta maida kuka abinci da kuma ruwan shanta, ita yanzu hartama fara tunanin ko aljanune suka shiga jikin Zahrah’n,, bayan kamar minti goma Husnah taƙira sunan Zahrah,, amma kuma saitaji shiru Zahrah bata amasa mata ba, hakan ne yasanya tayi tunanin cewa Zahrah’n tayi bacci, raɓawa gefen Zahrah’n itama tayi ta kwanta, mintuna kaɗan bacci yakuma surarta, Zahrah na jin sauƙar numfashin Husnah nafita a hankali ta tabbatar da cewa Husna’n tayi bacci, ahankali ta ware idanunta dasuka cika tab da ƙwalla, sarai tanaji sanda Husnah taƙira sunanta, taƙi amsawa ne gudun kada ta tonawa kanta asiri, saboda batason wannan sirrin yafita daga cikin zuciyarta, har abada tafiso ta bunneshi ita kaɗai batare dakowa yaji koya gani ba, ada tana ganin cewa ita mahaukaciya ce datakeson wanda ya zalunceta, sai ayanzu ta sake tabbatarwa kanta cewa shi so babu ruwansa, idan zai shiga jikinka baya duba wani cancanta ko matsayi haka nan yake faɗa ma, ashe da fari tayi ƙarya da tace zatayi yaƙi da soyayyar Zaid a zuciyarta, ashe ba’a iya yaƙi da soyayyar da take acikin jini da tsoka,, ada tana tunanin cewa zuciyarta bata kyauta mata ba, ashe itace bata kyautawa kanta ba, yanzu ta gamsu cewa so ne ya lalata mata rayuwa ba wai Zaid ba, ashe so shine ya yaudareta, ashe so shine yaci amanarta, ashe Zaid bai aikata mata wani babban laifi ba So ne ya aikata mata laifi me girma, inama da ana ganin so, to da tayi masa roƙo takuma yi masa magiya akan cutarwar da yayi mata daya barta haka,, itakuma SO shine ƙaddaranta, ada ta ɗauka idan tafaɗawa mutane cewa tanason mutumin dayayi sanadiyar rugujewar rayuwarta, kowa zai ɗauketa mahaukaciya wacce batasan me takeyi ba, amma kuma ayanzu tagane cewa wanda duk ya mata kallon mahaukaciya akan soyayyar da takeyia Zaid, to ko kaɗan baisan menene SO ba, SO shine wanda ke sauyawa mutum tunani alokaci ƙanƙani batare daya shiryawa hakan ba, SO shine wanda ke makantar da idanun mutum yazamanto bayaji baya gani, haka kuma tasanadiyar SO wasu ke salwantar da rayuwarsu, SO shike sawa kabi wanda baidace dakai ba, SO shike sawa amaka wulaƙanci amma kuma gobe ka koma inda aka wulaƙanta ka, SO shike sawa mutum yazalunceka amma kuma bazakaga laifinsa ba,kuma koda ma kagani bazaka iya juya masa bayaba, SO yana da matuƙar haɗari sannan yafi kowani abu saurin ɗaiɗaita tunanin meyinsa, SO shikaɗaine abun da zafinsa ke narkar da zuciya,,,,SO shine babban jagoran zuciya haka kuma shine raunin ta,, hanu ta sanya takuma dafe kanta wanda takeji kamar zai zazzago ƙasa,, hmmm kamar dai yanda Zahrah taga rana haka taga dare bacci sam yaƙauracemawa idanunta…..