SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

(Kada kuga laifin Zahrah dan ta ci gaba da son Zaid, haƙiƙa Zaid ya cancanci Zahrah taƙisa mugun ƙi mawa kuwa, amma kuma SO bazai taɓa barin haka yafaru ba, wallahi Soyayya tawuce gaban kwatance, so babu ruwanshi da wai ancutar dakai ko ba a cutar dakai ba, shi so kaitsaye yake abunsa batare da yatambayeka shawara ba, nikam bana ganin laifin Zahrah dan taso Zaid domin shi so baya fita acikin sauƙi, sannan kuma zafinsa yanada matuƙar illa, ba’akanta aka fara ba, sau da dama zakuga namiji yana zagi dakuma dukan matarsa amma kuma duk da haka tanazaune dashi saboda tana sonsa, haka kuma saudadama zakuga Saurayi yayi amfani da soyayyar da budurwarsa takeyi masa ya yaudareta sun aikata zina, daga baya kuma idan ciki yashiga jikinta sai kuga yagujeta, saboda yasamu abun dayakeso daga wajenta, amma kuma idan harson gaskiya takeyi masa saikuga bata daina sonsaba duk dakuwa irin girman abun dayayi mata,, wallahi soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa koda kuwa girman laifin da mutum ya aikata maka bazai misaltu ba, haƙiƙa idan banda sharrin SO babu wata mace da namiji zaiyi mata fyaɗe kuma ta dawo tacigaba da sonsa, wannan sharrin SO ne kawai wanda bashida magani???? nidai nace ko guba baikai so hatsari ba, wallahi so mugune, inkun ganshi kukamaminshi kumai duka????)
Ƙarfe 2 na dare ciwon Zaid yatashi sosai, abun gwanin ban tausayi, zuwa yanzu kam ciwon nasa yasoma fin ƙarfin tunanin Doctor’s domin kuwa sai anyi tunanin cuta tayi sauƙi saikuma tadawo, yanzu haka bincikensu yanuna musu cewa zuciyarsa ce takumbura, gaba ɗaya hankalin Alhj Ma’aruf yakai ƙololuwa wajen tashi, Mum kuwa yanzu bata da aiki saina kuka dare da rana, hakanne ma yasanya Alhj Ma’aruf yanke hukuncin tattara Zaid ɗin sutafi Jermany, saboda ya ga abun yana nema yafi ƙarfin likitotinmu na nan, saboda koda yaushe Zaid cikin aman jini yake, lokaci ɗaya ya lalace yayi wani irin rama, kamar ma ba
Zaid ba…..
Washe Gari (Asabar)
ƊAURIN AURE
Tun ƙarfe 8 na safe gidansu Zahrah yake acike yayinda ƴan uwansu na nesa suka soma hallara don ɗaurin aure,, hayaniya ne ke tashi kota ina acikin gidan…
Ɗakin Zahrah na garzaya don inga awani hali take ciki…
Kwance take akan katifarta yayinda duka jikinta ke rufe da bargo, amma duk da haka bargon bai ɓoye rawan da jikin nata keyi ba, karkarwa kawai takeyi acikin bargon yayinda jikinta yaɗauki zafin zazzaɓi zau..
“Kitashi kisha maganin nan dan Allah Zahrah, kinga fa babu amfanin zama da ciwo batare da kinsha magani ba” Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da lallami..
Kai kawai Zahrah ta’iya kaɗawa alamar “A’a bazata sha ba” komagana ma yanzu bata iyayi saidai kawai ta kaɗa kai, hakan yafarune kuma saboda ciwon kai me tsanani da ta tashi dashi a safiyar yau ɗin,, duk yanda Husnah takaɗa ta buga akan Zahrah tatashi tasha magani ƙiyawa tayi, sai ruwan hawaye dake ta fita daga cikin idanunta, dole haka Husnah ta ƙyaleta..
10:30 tuni ƙofar gidansu Zahrah yasake cika da jama’a bamasaka tsinke, hayaniya ne kawai ke tashi tako ta ina, yayinda tsala tsalan motocin ango suka ƙaraso,, hmmm Dr.Sadeeq yasha kyau sosai cikin wata haɗaɗɗiyar gezina milk colour me matuƙar kyau da tsadar gaske, ɗinkin rigane da wando saikuma gare, amma kuma sunyi masa kyau sosai, yayinda ya ɗaura tsadadden agogo a hanunsa na dama, takalmin ƙafarsa kuwa ƙirar kamfanin GUCCI ne me matuƙar kyau,, ango fa yasha kyau iya kyau, sai yau nima nasake tabbatarda cewa shiɗin ma wani Handsome guy ne mezaman kansa, domin kuwa duk ƙwaƙwan mutum babu ta’inda zai kushesa, yahaɗu iya haɗuwa sonkowa ƙin wacce ta rasa????, bakin ango fa yaƙi rufuwa sai murmushi kawai yake, yayinda abokansa keta tsokanansa,, shidai kawai murmushi yaketa zubawa, bazai taɓa iya misalta irin tarin farincikin dayake ciki ba, haƙiƙa yau yana cikin nishaɗi dakuma jin daɗi, yau takasance babban rana agareshi ranar da duk wani gauro da gauruwa suke jira, ranar da duk wani mai hankali da nutsuwa yake biɗar zuwanta wato RANAR AURE, shikam sai dai yace Alhmdlh yagodewa Allah mai kowa me komai daya nuna masa wanann rana… Baffa na hango shima yau cikin farinciki yake, yasha adonsa cikin farar shaddansa riga da wando dakuma gare, su uban amarya manya,,, 11:00 am dai dai dandazon jama’a suka shaida ɗaurin auren SADEEQ KHABEER SARDAUNA (Dr.Sadeeq) da amaryarsa FATIMA ADAM (Zahrah) akan sadaki naira dubu ɗari,, masha Allah ana kammala ɗaurin aure aka soma taya ango murna da Allah yasanya alkhairi, ae kuwa fuska asake haɗe da tarin annuri Dr.Sadeeq ke amsawa, hamdala kawai yakeyi acikin zuciyarsa shikenan Zahrah ta zama tasa mallakinsa halaliyarsa… Bayan angama musabahane kuma aka ɗunguma zuwa wani babban hotel wanda anan za’a gudanar da receiption….
Lokacin da labari ɗaurin auren ya’isa ga kunnen Amarya wani irin faɗuwar gaba wanda bata taɓa jin irinsa ba taji ya rusketa, shikenan yanzu tazama matar Doctor, zuciyar tane tashiga bugawa da sauri sauri yayinda har ƙirjinta yasoma amsawa, take taji wani abu maikama da tsananin tsoro ya lulluɓe mata jiki,ae kuwa sai neman ɗan kuzarinta tayi ta rasa,jitayi gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mutu laƙwas kamar ansassare mata su,, sake duƙunƙunewa tayi acikin bargo tashiga rera kuka marar sauti, ita bata tsani Dr.Sadeeq ba ko kaɗan, amma kuma tarasa meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarta….
(Kuyi haƙuri Team Zaid wallahi nima Allah jikina gaba ɗaya yayi sanyi sai dai kuma kunsan ita ƙaddara bata taɓa sanjawa dole saitazo a yanda Allah ya aikota???? yanzu haka jinake kamar ruwan jikina ya ƙare????)
Ƙarfe 2 dai dai jirginsu Zaid yatashi daga cikin garin Lagos Nigeria zuwa Jermany saidai shi Zaid sam baisan wainar da ake toyawa ba saboda baya cikin hayyacinsa kwata kwata, tunda suka baro Abuja har suka iso Lagos baisan inda kansa yake ba….
Ɓangaren ango kuwa reception aka gudanar gangariya, anci kaji ansha fruits juice kowa cikin sa yayi haniƙan sai dai godiyar Allah da sanya albarka…
Amarya kuwa koda ruwane takasa sanyawa acikin cikinta, rashin lafiya sosai ya tsananta a gareta, zuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sundaina fitowa, sai numfashin wahala da take fitarwa ta bakinta kawai,, kasancewar anata hidima yasa babu wanda yadamu da cinta kokuma shanta, Husnah ce kaɗai ke tsaye akanta tana bata kulawa.
“Dan Allah Zahrah ba danniba kitashi inrakaki toilet kiyi wanka kizo kisamu koɗan sabon kayane kisanya kingafa zuwa anjima za’a zo ɗaukarki!” Husnah tafaɗi haka tana me ƙoƙarin tada Zahrah dake kwance zaune.
Da taimakon Husnah Zahrah taje banɗaki tayi wanka, koda tafito wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa Husnah ta bata tace ta sanya, babu musu tasanya saigashi kuwa rigan tayi matuƙar yi mata kyau ajiki, da ƙyar Husnah ta lallaɓata tashafa mata powder haɗe da man leɓe, sai kace wata ƙaraman yarinya,,, komawa gefe Zahrah tayi ta takure bayan Husnah tagama shiryata, still Husnah maganar abinci tayi mata amma Zahrah tasake bushe idanunta tace ita sam bazataci abinci ba batajin yunwa (Ninaga jarfa saikace wanda aka mawa auren dole ????)…
Ƙarfe 5 tsala tsalan motocin ɗaukar amarya suka shiga fakawa a ƙofar gidansu Zahrah motocine reras masu kyau har guda 15 suka zo don ɗaukar amarya yayinda motar da amarya zata shiga ta banbanta da duka sauran motocin don tafi duka sauran kyau..