SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yauma dai ango tare da amaryarsa zasu wajen dinner kowa yariga daya tafi harsu Auntie Raliya kuwa….
Husnah ce riƙe da hanun Zahrah suka fito compound ɗin gidan inda motar ango ke jiransu.
Shikam gaba ɗaya kwana biyunnan salon kyawun na Zahrah namatuƙar tafiya da imaninsa babu ma kamar yau, gaba ɗaya komai na surar jikinta ya bayyana bama kamar hips ɗinta yafito raɗau acikin rigan..
Husnah ce ta buɗe murfin motar dayake zaune aciki, sai da ta tattaro ƙasan rigan Zahrah’n kafun Zahrah ta’iya shiga cikin motar ta zauna,, lumshe idanunsa yayi haɗe da shaƙan daddaɗan ƙamshin daya kawowa hancinsa ziyara, wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe,, kallonsa yakuma dawowa dashi kan tauraruwar da haskenta yacika idanunsa,,, murmushi yasakar mata me ƙayatarwa, yayinda ita kuwa kanta ke duƙe aƙasa tama kasa ɗago idanu ta kalleshi,, hanunsa ya sanya ya ɗago haɓarta, sai alokacin ta iya jefa idanunta cikin nasa idon, wani irin abu yaji acikin jikinsa, ita ɗinma hakane, da sauri ta rumtse idanunta,, abun daba ta tsammata ba, sai jitayi ya jawota jikinsa, haɓanta yakuma ɗagowa da hanunsa na dama, haɗe da sanya ɗayan hanunsa yashafi gefen kumatunta
“My Princess!”
yaƙira sunanta cikin wata muryarsa me sanyi. a hankali ta ware idanunta acikin nasa idanun, ƙasa ƙasa yayi da idanunsa haɗe da maida kallonsa ga ɗan ƙaramin bakinta dayasha lipstick, murmushi yakuma sakarmata haɗe da sake jawota ya ɗaurata akan cinyarsa.
“Kinyi kyau fiye da kullum my princess!” yafaɗi haka still yana me shafa gefen kumatunta da hanunsa, wani irin kunyarsane yakamata tunda take dashi baitaɓa yi mata irin kallon dayakeyi mata a yanzu ba, haka kuma baitaɓa jawota yaɗaurata akan cinyarsaba sai yau. Marairaice fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa,, sweet ɗin dake cikin bakinsa ya cire, haɗe da ɗago fuskarta ya sanya mata acikin bakinta, kallonsa tayi da ɗara ɗara idanunta, kansa ya jinjina mata yana ɗan murmushi, ahankali tashiga juya sweet ɗin acikin bakinta, dama kuma tunsafe babu wani abu daya shiga bakinta inbanda ruwa, sai wannan sweet ɗin daya bata yanzu,, hanunta yakama yashiga murzawa ahankali haɗe da kafeta da idanunsa wanda lokaci ɗaya suka wani marairaice…. Sauƙeta yayi daga kan cinyarsa haɗe da kama hanunta ya buɗe murfin motar riƙe da hanunta haka suka fito daga cikin motar,, kamar wata jela haka take binsa still hanunta na riƙe acikin nasa, direct wani dogon gini dake cikin gidan nasu suka nufa. Ita dai kawai binsa take cikin takunta me ɗauke da nutsuwa yayinda rigar jikinta kuwa ke share wajen, don ma wajen babu datti, wani haɗaɗɗen falo ta tsinci kanta a ciki, suna shiga cikin falon Doctor yatsaya daga tafiyan da yakeyi haɗe da juyowa gareta, murza hanunta dake cikin nasa yayi haɗe da zaunar da’ita akan kujera, kaitsaye wajen wani fridge dake aje cikin falon ya nufa, buɗe murfin fridge ɗin yayi haɗe da ɗauko kwalin fresh milk wanda bashida sanyi sosai, glass cup ya ɗauka ya tsiyaya fresh milk ɗin aciki, saida yakusa cika kofin kafun yamaida sauran cikin fridge ɗin ya aje.. Inda Zahrah ke zaune ta sunne kai ƙasa ya nufo, aje kofin fresh milk ɗin yayi akan ɗan ƙaramin table ɗin dake kusa da kujeran daya zauna, jawo Zahrah yayi jikinsa haɗe da sake ɗaurata akan cinyarsa, kofin da fresh milk ɗin ke ciki ya kawo dai dai saitin bakinta, cikin muryar lallami yace
“Anfaɗamin bakici komai ba tun safe, banaso kina zama da yunwa fa, banso tayi miki illa, kisha ko kaɗanne kinji baby na!”
Tsintar kanta tayi da kasa musa masa, saidai amma kuma gaba ɗaya a tsarge take, bata taɓa zama akan cinyar wani haka ba, hakan yasa gaba ɗaya ta takura,, a hankali take ɗan shan fresh milk ɗin wanda harkusa da bakinta Dr.Sadeeq yake kawo mata kofin, shan fresh milk ɗin take cike da nutsuwa yayinda shi kuma gaba ɗaya idanunsa ke kanta, bakinta kawai yake kallo, karo na farko kenan arayuwarsa dayaji wani irin muguwar sha’awarta na fusgarsa,,, kafun shida ita su ankara tuni hartasha fiye da rabin kofin,, ɗan ya mutsa fuskanta tayi haɗe da sanya hanu ta shafi ɗakalallen cikinta
“Naƙoshi fa!” tafaɗi haka tana me langwaɓar da kanta gefe.
“Um’um ban yarda ba nasan kinajin yunwa sosai, ki ɗan ƙarasha ko kaɗan ne kinji MY WIFE!”
Kalmar nan ta_MY WIFE_ daya ƙirata dashi shiyasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi mata wani iri,,, bakinta ta turo gaba haɗe da cewa
“dagaske ni na ƙoshi, gashi kuma duk kasa janbakina ya goge!” taƙare maganar akasalance.
Wannan shagwaɓan da takeyi masa shiyake sanyawa yaji gaba ɗaya jikinsa ya mutu, har wani rufewa idanunsa keyi,, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, kobai ɗaga ba yasan dalilin ƙiran, yanzu haka yasan anacan antaru a wajen dinner su kawai ake jira, miƙar da’ita yayi tsaye bayan ya aje cup ɗin dake hanunsa,, amaimakon ya riƙe mata hanu su tafi kamar yanda suka zo sai gani tayi ya ɗagata caɗak yayi hanyar waje da’ita,, a tsorace tanemi sauƙa daga jikin nasa amma kuma kyakkyawan riƙon dayayi mata yakasa bata daman hakan….
Bai direta ako ina ba sai acikin mota, yanashiga driver yaja motar suka fice daga cikin gidan… Kwanciya tayi luf ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunta gaba ɗaya sanyin AC’n da motar ke busawa ne ke damunta, sam batason sanyi yacika yawa a waje. daga wani ɓangare kuwa amatuƙar takure take, saboda yanayin yanda yake murza hanunta dake cikin nasa. sosai hakan kesawa taji wani iri acikin jikinta, gani tayi gaba ɗaya yau ɗin ya sanja mata, yanayi mata wasu irin abubuwa da baitaɓa ƙoƙarin kwatanta yi mata shiba acan baya, ada sam baya taɓa yunƙurin kama hanunta sai dai idan yazama dole,kuma koda ma ya kama hanunta bawani jimawa zai sake, sannan kuma sam baya yawan jawota jikinsa kamar yanda yakeyi mata ayau, gashi gaba ɗaya taga yanayinsa ya sauya, idanunsa sunyi wasu kala tamkar wanda yakejin bacci… Zuciyarta nayi mata lugude haka suka iso wajen dinner inda mutane suka cika maƙil zuwansu kawai ake jira… Suna isowa waje yaɗauki sowa yayinda mc yasake musu daddaɗan kiɗa me daɗi ta romantic… kamar dai yanda kamu ya ƙayatar haka dinner ma yaƙayatar sosai Dr.Sadeeq yayiwa Zahrah ɓarin kuɗi lokacin da aka ƙirasu tsakiyan fili, sunsha liƙin kuɗi kam sosai, su Auntie Raliya ma sunzo sun liƙa musu, amma duk yanda akaso amarya tayi rawa kasawa tayi, saboda bata iyaba, bakuma al’adarta bane yin rawa agaban mutane, kunya ma bazai taɓa iya barinta ba,, saida Dr.Sadeeq yariƙe hanunta yashiga juyawa da’ita afilin rawan, take aka hau musu tafi yayinda wasu daga cikin abokansa suka ci gaba da yi musu ɓarin kuɗi,, suna komawa kan kujeransu mc yasanya musu daddaɗan waƙar Ed sheeran, shiru Zahrah tayi tana sauraran waƙar sosai dama takeson waƙar domin kuwa duk waƙan Ed sheeran yanayi mata daɗi… Koda aka yanka haɗaɗɗen cake ɗin da aka ƙawatashi da sunan ango da amarya, da ƙyar Zahrah ta’iya bawa Dr.Sadeeq cake ɗin abaki, gaba ɗaya nauyi da kunya sun isheta gawani zazzaɓin daya sake kawo mata ziyara lokaci ɗaya,,, lokacin da aka tashi a dinner tuni amarya Zahrah tayi laushi, hartakai bata iya dogon tsayuwa da ƙafafunta, ƙarfe 10 na dare aka tashi a dinner Aunty Ladi da kuma Husnah su suka sanyata a wata mota, direct aka wuce da’ita asalin gidan da zata zauna wato gidan aurenta…. Gidane me matuƙar kyaun gaske wanda aka kashe kuɗi sosai wajen ƙawatasa, baginin gidan sama bane amma kuma yanayin yanda akayi ginin yayi kyau sosai, wata haɗaɗɗiyar ƙofa suka nufa, suna buɗeta kuwa suka tsinci kansu cikin wani ƙawataccen falo me kyaun gaske. haɗaɗɗen falone wanda yasha kujeru light orange and milk colour, yayinda aka ƙawata jikin ƙofa da window’n da wasu irin haɗaɗɗun labulaye masu kyau, tsakiyar falon kuwa mamaye yake da wani haɗaɗɗen carpet Orange colour,, ga wani irin ƙaton tv plasma dake aje kan wani haɗaɗɗen glass,, falon dai ba’acika masa kayan ado ba amma kuma yaƙawatu sosai komai na falon me tsada ne,, direct wani ɗaki dake cikin falon aka wuce da Zahrah,, ɗakine me kyau wanda yaji royal furnitures milk colour, yayinda aka lailaye kan makeken gadon da wani irin zanin gado pink me kyawun gaske… Akan gado sukayimawa Zahrah masauƙi, Husnah dakanta ta haɗawa Zahrah ruwan wanka, koda tafito a bathroom ɗin hannayen Zahrah dake zaune kan gado ta kamo, haɗe da janta har zuwa cikin bathroom inda ta haɗa mata ruwan wanka…