SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani Turare ta bata tace inji Hajiya Shuwa, sannan kuma tayi mata bayanin yanda zatayi amfani dashi…
Zahrah tana fitowa a wanka Husnah ta shafa mata powder haɗe da lipstick, wani riga da sket na material marar nauyi Husnah ta bata tasanya, take tafito ɗas da’ita, a tsakiyar gado Husnah ta zaunar da Zahrah haɗe da rufe mata kanta da wani irin haɗaɗɗen mayafi me sheƙi da walwali, wasu turaruka masu ƙamshi Husnah takuma feshi jikin Zahrah dasu, take ɗakin yakuma ɗumamewa da ƙamshi,, sake matsowa kusa da Zahrah Husnah tayi cikin murya ƙasa ƙasa tace
“Dan Allah Zahrah karkice zaki ci gaba da wannan kukan naki, ki ɗan daure zuciyarki kinji ƙawata, kuma sannan kada ki hana Doctor haƙƙinsa, nasan zakiji tsoro amma please ki daure kinji ƙawata, banaje falo na amsa waya ” Husnah taƙare maganar tana me miƙewa tsaye, idanu tayiwa Auntie Ladi suka fice a tare….
Tun Zahrah na jiran dawowan su Husnah hartasoma jin tsoro, domin kuwa gaba ɗaya gidan yaɗau shiru babu alaman akwai motsin wani mutum bayan ita,,, abun da Zahrah bata sani ba shine su Husnah wayo sukayi mata suka tafi suka barta, sunyi hakanne kuma saboda taƙaitamata wahalan kuka, domin sun san sunace mata zasu tafi zata ƙara fawan kukanta…..
Gyangyaɗine yasoma ɗaukarta, dan haka saita jingina bayanta ajikin saman gadon haɗe da lumshe idanunta da suketa tsiyayar hawaye…
A hankali yaturo ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, yasake shiga cikin wata farar shadda sabuwa ƙal sai sheƙi takeyi, ƙamshi ne kawai ke fita ajikinsa, daganinsa kasan yana cikin matsanancin farinciki,, ledan dake hanunsa ya aje, haɗe da takowa zuwa wajen datake zaune ta jingina bayanta da saman gado,, zama yayi akusa da’ita haɗe da ƙiran sunanta,, cikin murya me sanyi da kuma alamar bacci ta amasa masa,, ahankali yasanya hanunsa ya ɗan jaye mayafin dake kanta, hawaye yagani kwance akan fuskarta, hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa, hanu yasanya yashiga share mata hawayen dake kan fuskarta.
“Ki daina kuka kinji my wife, bacci zakiyi ne?” yatambayeta yana me ƙaremawa fuskarta kallo,, fuska ta kuma kwaɓewa, haɗe da kaɗa kanta, cike da shagwaɓa tace
“Ina Husnah?”
Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da sanya hanu yashafi lallausan gashinta dayasha gyara
“Husnah kuma Zahrah?” yatambayeta cike da mamaki..
“Eh tacemin zata amasa waya tana zuwa kuma haryanzu bata dawo ba!” yanzuma dai asangarce tayi maganar,, murmushi yayi mata haɗe da cewa
“Kada kidamu Husnah zata dawo gobe, taso muje kiyi alwala idan munyi salla saikici abinci ko”
Jitayi gabanta yayi wani irin faɗuwa amma kuma yazatayi da rayuwarta babu yanda ta’iya haka tabisa kamar jela harcikin bathroom,, saida yayi nasa alwalan kafun yabata waje itama ta ɗauro alwala,, tana fitowa daga cikin bathroom ɗin ya miƙo mata wata lufaya, a ɗaɗare tasanya lufayan daya bata, hanunta yakama suka hau kan sallaya, shi yajasu salla raka’a biyu, suna idarwa yayi musu addu’o’i haɗe da kama kanta itama yayi mata addu’a… A tsorace ta zauna akan gado haɗe da sake takure jikinta waje ɗaya…
Wani ɗan madaidaicin carpet Dr.Sadeeq yashimfuɗa haɗe da cika tsakiyar carpet ɗin da kayan ciye ciye, hanu ya miƙawa Zahrah alamar tataho garesa, cikin ɗari ɗari haka ta shiga takowa zuwa inda yake, hanunta yakamo yazaunar da’ita acikin jikinsa, hijabin dake jikinta yasoma ƙoƙarin cire mata, da sauri tasake ƙanƙame jikinta, ganin haka yasanya shi yin murmushi, ya fasa cire mata hijab ɗin,, juice ya zuba acikin kofi haɗe da kai kofin bakinta, babu musu tabuɗe bakinta ta kurɓi kaɗan, aje kofin yayi, haɗe da yago gasasshen nama yakai bakinta,, kanta tashiga girgizawa alaman bazataci ba.
“Kiyi haƙuri kici kinji Baby na, kaɗan zakici bamai yawa ba!” yafaɗi haka cike da lallami,,, shida kansa yake bata kazan, bata wani ci me yawa ba tace masa ta ƙoshi, dakansa yatattara wajen yakai kitchine,, yana dawowa ɗakin yasameta tsaye ajikin mirror tayi jigum,, fargabane yacika mata zuciya, wani irin tsoro ne taji ya ɗarsu acikin zuciyarta wanda bazata iya misaltashi ba,,
Kaitsaye drower ɗin dake cikin ɗakin ya nufa, wata doguwar rigan bacci sleeping dress yaciro haɗe da ƙarasowa gareta,, “Kije kiyi brush, wannan kayan kuma kisanya kizo kiyi bacci” hanunta na rawa haka ta amshi kayan sumi sumi ta wuce cikin bathroom, tana kammala brush tasoma cire kayan jikinta, warware rigan da Dr. yabata tayi tashiga ƙaremawa rigan kallo, doguwar rigace na bacci me net, amma kuma tana da faɗin wuya sannan kuma rigan irin me nuna jiki ɗinnan ne,, badon tasoba haka ta sanya rigan ajikinta, hmmm sam bazata iya fita da wannan rigan gaban Dr. Sadeeq ba, saboda gaba ɗaya rigan ta bayyana breast ɗinta, yayinda komai nata yafito fili, hijabin da tayi salla dashi ta ɗauka ta sanya,, a ɗaɗare ta fito daga cikin bathroom ɗin,, zaune tagansa akan gado tuni yasanja kaya zuwa farar jallabiya, murmushi kawai Dr.Sadeeq kejifanta dashi, cikin zolaya yace “Meye narufe jikin da hijabi?”
Ƙasa takumayi da kanta, yanzu kam ko ɗan shagwaɓan ma takasayi masa…
Sarai ya fuskanci halin da take ciki, “Zoki kwanta” yafaɗi haka yana meyi mata nuni da kan gadon dayake zaune,, kamar wacce ƙwai yafashewa haka Zahrah ta zo ta kwanta akan gadon, gaba ɗaya ta takure kanta waje ɗaya,,, miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da kashe wutan ɗakin ya kunna na bacci, Zahrah najin takusan alamar yakusa zuwa kan gadon taji bugun zuciyarta ya tsananta, yayinda ƙirjinta yashiga wani irin luguden duka,, kwanciyarsa akan gadon yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta,,,, da ƙyar ta’iya ƙwato numfashinta, haɗi sa soma sauƙe ajiyar zuciya a ɓoye, kusan minti goma da hawansa kan gadon amma kuma taji baiyi mata wani abu ba, hakan yasa taɗanji zuciyarta tayi sanyi. Shiru tayi tana me jin sauƙar numfashinsa ahankali, wani irin mugun tausayinsa ne taji yaɗarsu acikin zuciyarta amma kuma ita bata da yanda zatayi, tunaninta ne ya katse alokacin da taji sauƙar hanunsa a bayanta,, ahankali ya juyota tadawo tana fuskantarsa,, kallon fuskarta yashigayi batare dayace da ita komai ba, kusan mintuna 4 yayi yana kallonta, cikin wata irin murya wanda batasanshi da ita ba yace
“kicire hijabin nan saboda kiji daɗin baccinki ko”
babu musu ta cire hijabin daga jikinta sai dai kuma bahaka ranta yaso ba, bargo yaja ya rufa musu hanunta yakamo ta cikin bargon yariƙe acikin nasa, “Ki kwantar da hankalinki, nasan kingaji, kiyi addu’a, kiyi bacci me daɗi” yafaɗi haka cikin muryar raɗa, hanunta yasake damƙewa acikin nasa hanun haɗe da lumshe idanunsa, zai bartane kawai saboda tausayinta dayake ji, amma bawai don baya sha’awarta ba, hasalima baita ɓa jin matsanancin sha’awarta irin nayau ba, hakan yafarune kuma saboda baitaɓa samun kusanci me tsanani da ita irin na yau ɗin ba, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa,,,, Zahrah ma dai baccin ne yaɗauketa batare data shiryawa hakan ba,, ƙarfe ɗaya na dare wani irin zazzafan zazzaɓi yarufe jikin Zahrah take tasoma karkarwa haƙwaranta har haɗewa suke, suna ba da wani sauti, hakan yafaru ne kuma sakamakon sanyin AC wanda yayi mata yawa, acikin baccinsa yakejin hucin numfashinta nafita da sauri, a hankali ya buɗe idanunsa ya sauƙesu akanta, da sauri yatashi ya zauna haɗe da kamo kafaɗunta,, “Zahrah!” yaƙira sunanta a hankali,, tanajinsa amma bazata iya amsa masa ba domin kuwa ba iya zazzaɓi ba hatta kanta jinsa take tamkar anɗaura mata gungumen ice, yamata nauyi Da sauri ya sauƙa akan gadon, AC’n yafara kashewa, kana ya buɗe wata ƴar drower maganin ciwon kai da zazzaɓi ya ɗauko haɗe da goran ruwa,, yana zuwa ya ta data zaune, ɓalle maganin yayi yasa mata abaki haɗi da kafa mata goran ruwa, babu musu ta haɗiye maganin, ajiye goran yayi haɗe da hawa kan gadon, hanunsa yasanya akan wuyanta, zafi yaji zau kamar wuta, ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da cire rigan dake jikinsa, cikin bargon yakoma, haɗe da jawota kusa dashi, ahankali yasanya hanunsa a bayanta yayi ƙasa da zip ɗin doguwar rigan dake jikinta,, cike da nutsuwa ya cire mata rigan,, Zahrah tana jinsa amma kuma ayanzu babu wani abu da zata iyayi wanda zata kare kanta,, bashi kaɗaiba har ita kanta saida ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi alokacin da zallan fatar jikinsu suka samu haɗewa waje guda. lokaci ɗaya yaji tunaninsa yasoma sauyawa, nutsuwarsa tafara gushewa, haka kuma idanunsa sun soma rufewa,, haɗewar jikin Zahrah danasa jikin baƙaramin feeling me girman gaske ya sauƙar masa ba, tunda yake aduniyarsa yau shine karo na farko, da ya fara haɗa jikinsa dana mace haka, yasan yataɓa rungumar Zahrah amma ba runguma irin wannan ba,,,, Zahrah kuwa baƙaramin jin daɗin jikin nasa tayi ba, jitayi gaba ɗaya nutsuwa yasoma sauƙar mata, sake maƙalewa ajikinsa tayi haɗe da cusa kanta acikin faffaɗan ƙirjinsa har yazamana laɓɓan ta suna gogan fatar wuyansa,, jin yanda take ƙara shigewa jikinsa shiya ƙara taimakawa wajen ƙara masa wutar sha’awarta, hannayensa duka yasanya a bayanta yasake riƙeta gam, numfashi kawai yake fitarwa akai akai shi kaɗai yasan meyakeji acikin jikinsa,, yana cikin wannan irin yanayin yaji sauƙar numfashin Zahrah ahankali yana fita da’alama baccine yakuma ɗaukarta,,, haka yarungumeta ƙam acikin jikinsa yayinda yacusa kansa acikin gashin kanta yana shaƙan daddaɗan ƙamshinta dake ƙara rikitasa,, bakaɗan ba ya yi jarumta wajen ganin ya ƙyaleta baiyi mata komai ba, haƙiƙa bakowani irin namiji bane zai haɗa jiki da mace ace ya iya daure zuciyarsa baiyi mata komai ba, balle ma mace irin Zahrah wanda irinsu basu da yawa acikin mata,, da ƙyar bacci ya’iya ɗaukarsa…….