NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

(Kuyi Haƙuri idan kunga typing error ina busy ne)
   
        

18/January/2020

          Fatymasardauna
????????????????????????????????????????

       SHU’UMIN NAMIJI !!

    Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            WATTPAD
     @fatymasardauna

Editing is not allowed????

       CHAPTER 92 to 93

Ƙiran sallan asuban fari akan kunnensa,, a hankali ya ware idanunsa akanta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da’alama zazzaɓi da ciwon kan dake damunta sun jima da kama gabansu,,  baisan lokacin da murmushi ya ƙwace masa ba, komai na Zahrah me kyau ne, har idan tana bacci kyawunta baya ɓuya, kallon zara zaran eye lashes ɗinta daya kwanto aɗan ƙasan idanunta yayi,,  ahankali ya zare jikinsa daga nata jikin, cikin sanɗa yatura ƙofar bathroom yashige, gudun kada motsinsa ya tashe ta daga daddaɗan baccin da take,,  saida yafarayin wanka kafun ya ɗauro alwala,,  tsayawa yayi yana kallon yanda taketa fidda numfashi a hankali,  badon sallah yazama dole akanta ba, to tabbas da babu abun da zai sanya ya tasheta a dai-dai wannan lokacin, zai bartane tasha baccinta ta ƙoshi,, ahankali yashiga girgiza ƙafanta haɗe da ɗan ƙiran sunanta, cikin murya ƙasa ƙasa… Da yake bata da nauyin bacci, ƙira biyu yayi mata ta buɗe idanunta,, da sauri ta sake jawo bargo ta rufe jikinta, kana tasoma raba idanu,   murmushi yakumayi mata haɗe da sanya hanu ya shafi gefen kumatunta.

“Kitashi kiyi sallah, ni na wuce masallaci”

Bata iya amsa masa ba haryafice daga cikin ɗakin,,    kallon kanta tashiga yi gaba ɗaya gashinta ya watse yayi buji buji dashi, da’alama dai tasha juyi acikin bacci,,,    tana shiga bathroom ta haɗawa kanta ruwa me ɗan ɗumi, wanka tayi itama kana ta ɗauro alwala (????Yadai dukanku wanka sai kace ????)….

Tana fitowa daga bathroom ɗin ta zura wata jan doguwar riga marar nauyi, haɗe da zura hijab ajikinta,  kan sallaya tahau  haɗe da dai-dai ta tsayuwarta……      Koda ta’idar da sallan saida tayi azkar kafun ta miƙe daga kan sallayan,,   harta zauna akan gado, maganganun Hajiya Shuwa suka faɗo mata arai inda take ce mata  “Kada ta sake ƙamshi yabar jikinta, sannan kuma idan tayi sallan asuba kullum tana shafa turare aduk wani lungu da saƙo na jikinta” batasan mene manufar hakan ba, amma dai ta ɗau maganar kuma zatayi aiki dashi.   Gaban mirror tanufa haɗe da ɗaukan ƴar ƙaramar hand bag ɗinta dake aje kan mirror’n  wani ɗan kwalban body spray ta ciro daga cikin jakar, haɗe da fesawa ajikinta, daga kan wuyanta har zuwa bayan kunnenta, sosai turaren yake da ƙamshi, take ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren,, tana shirin maida turaren cikin jakarta, Dr.Sadeeq yaturo ƙofar yashigo bakinsa ɗauke da sallama,, cikin murya me sanyi ta amsa masa sallaman nasa,,    direct inda take tsaye ya nufo, batayi tsammani ba saiji tayi ya buɗe hannuwansa ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta,,,, idanunsa ya lumshe haɗe da buɗe hanci ya shaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta cikin wata irin murya yace
“Good morning madam!”

Kunyan sane yakamata,  saikawai tayi ƙasa da kanta haɗe da cewa

“Ina kwana”

“Lafiya ƙalau, yajikinki?” ya amsa mata yana me cusa kansa acikin wuyanta..

“Da sauƙi”

Ta mayarmai da amsa cikin ƙasa da murya…

“Ƙamshinki yamin daɗi sosai, kinyi sallah ne?”

Kanta ta ƙaɗa masa alamar “Eh” hanunta yakama yajata zuwa kan gado… Zama yayi kana ya jawota jikinsa,,    ɗago fuskarta yayi haɗe da jefa idanunsa cikin nata.     Sunanta yaƙira cikin wata irin murya me ɗauke da nutsuwa..

Kanta ta ɗago ta kallesa, ganin idanunsa tsaye cak akanta yasanya tayi saurin meda kanta ƙasa..    

“Meyasa kikejin kunya na sosai ne?”

Yayi mata tambayar da bata tsammata ba,, jijjiga kanta tayi alaman 
“babu”

Sake matseta acikin jikinsa yayi haɗe da kwantar da kansa akan kafaɗanta.

“Mallakarki danayi wata babban nasara ce dana samu acikin rayuwata Zahrah, inasonki ne da duka zuciyata,  dakuma iya gaskiyata, banda niyar cutar dake acikin rayuwar zaman aurenmu,   abu ɗaya nakeso kiyi mini shine, ki rage yawan tunani da kuma kukan nan dakikeyi, inajin tsoro kada su haifarmiki da wata cuta, yanzu nasan kina da buƙatar hutu ko, ki kwanta ki huta, kafun anjima sai kiyi break fast”   

Miƙewa tayi daga jikinsa haɗe da hayewa  kan gadon ta kwanta, amma kuma bata ɗauke idanunta akansa ba,    bayan kamar mintuna biyar da kwanciyarta shima yatashi daga zaunen da yake, kan gadon ya hau, har Zahrah taji bugun zuciyarta yasoma ƙaruwa, sai kuma taga ya lulluɓe mata duka jikinta da blanket, agefe da ita ya kwanta haɗe da juya mata baya… Shiru ɗakin ya ɗauka babu abun dake tashi sai sautin fitar numfashinsu,,,  bayansa ta kafe da idanu, yayinda a cikin zuciyarta take wani tunani na daban, haƙiƙa duk duniya babu wani namiji daya dace yazamo miji agareta sama da Dr.Sadeeq, ya cancanta ƙwarai, shi mutum ne  wanda zaiyi wahala asamu kamarsa, Dr.Sadeeq kuwa lumshe idanunsa yayi bawai don bacci ya ɗauke sa ba,,  shima wani tunanin yakeyi daban,   baisan meyasa aduk sanda idanunsa zasuyi masa tozali da Zahrah yakejin matsanancin sha’awarta ba, wanda ada kuma ba haka abun yake ba, bazaice da bayajin sha’awarta ba, yanaji sai dai kuma bakamar wanda yakeji  yanzu ba, jiya bakaɗan ba ya’iya daure zuciyarsa, amma daba haka ba tabbas da baisan wani irin aika aika zaiyi mata ba,   a hankali yaji idanunsa sun soma rufewa da’alama dai shima bacci bai ishesa ba, ae dole ma jiya sunsha gajiya sosai,, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauki ma’auratan biyu,  yayinda kowanne daga cikinsu da irin samfurin tunanin dake cikin zuciyarsa…. 


10:00 am dai-dai ta buɗe idanunta, haɗe da waresu akan haɗaɗɗen zanen POP’n da ya cika  saman ɗakin,   kallonta ta mayar ga inda take tsammanin ganinsa, amma sai dai taga wajen wayam babu shi babu alamarsa.  Da sauri ta tashi zaune haɗe da maida kallonta  ga wani ɗan madaidaicin agogon bangon dake saƙale jikin ginin ɗakin.

“ƙarfe 10 nakai ina bacci?”

ta tambayi kanta cikin yanayi naɗan mamaki..  A hankali tazuro ƙafafunta ƙasa, haɗe da miƙewa tsaye, ɗakalallen cikinta daya soma mata kukan yunwa ta shafa, haɗi da ɗan yamutsa fuskarta, direct  ƙofar bathromm ta nufa, ɗan tsayawa tayi ta kasa kunnenta ajikin ƙofar, koda zataji ƙaran ruwa, amma saitaji shiru da’alama dai bakowa acikin bathroom ɗin, murɗa handle ɗin ƙofar tayi tashige ciki,, ruwan wanka ta haɗa yayinda ta cika turaren ƙamshi acikin ruwan,    wankanta tayi cike da nutsuwa…  Sanye da wani  ɗan madaidaicin towel pink colour ajikinta tafito daga cikin bathroom ɗin, hatta gashin kanta ajiƙe yaƙe, still ƙaramin towel ne kuma riƙe ahanunta tana goge gashin kanta dayake ajiƙe,,  daidai lokacin Dr.Sadeeq yaturo ƙofar ahankali yashigo, suman tsaye yayi ajikin ƙofar yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasanta, yayinda ita kuwa batasan ma da zuwansa ba, kanta kawai take aikin gogewa, saboda bataji motsin buɗewar ƙofar ba, shikuwa dama yabuɗe ƙofar ne ahankali gudun kada ya tasheta a baccin daya barta tanayi,,   wani yawu ya haɗiye, haɗe da jan ƙafansa a hankali yafice daga cikin ɗakin batare daya bari ta ganshi ba,, yana fita yajingina bayansa da ƙofar haɗe da sauƙe wani irin ƙaton ajiyar zuciya,, lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanunsa acikin tulin sumar kansa yashiga shafawa a hankali,, ashe haɗuwar Zahrah yawuce yanda yake zato yake kuma tunani, wannan wace irin haɗaɗɗiyar surace Zahrah’n sa ta mallaka,, lallai Zahrah mace ce cikakkiya tagaban kwatance,, da ƙyar ya’iya jan ƙafansa ya koma cikin falo, kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa da suka sauya launi lokaci guda…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button