SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zahrah kuwa tana gama goge gashin nata tayi amfani da hand dryer wajen busar dashi mintuna kaɗan gashin yabushe tashafa masa mai,,, wani lotion me ƙamshi ta shafa ajikinta haɗe da murzawa fuskarta hoda da kuma kwalli, light pink lipstick tagoga akan leɓenta, take fuskarta ta tasake yin kyau,, gaban makeken drower’n dake kafe ajikin bangon ɗakin taƙarasa haɗe da buɗewa, kayane jere reras acikin drower’n kala kala sai wanda ranka yaso zaka saka, wata jar atamfa taciro wacce taji ɗinkin pencil gown,, tana sanya doguwar rigan yayi mata kyau haɗe dayi mata ɗas ajikinta, daga kan guiwanta harzuwa ƙafarta atsage yake ta bayan rigan, tanason atamfar sosai saboda tana ɗaya daga cikin kayan da Maman Husnah ta bata, Husnah ce kuma takai akayi mata irin wannan ɗinkin duk da kuwa irin tsadar da atamfar take dashi, kallon kanta tayi acikin madubi, murmushi tasakarwa kanta saboda ita kanta ta yaba da yanda rigan tayi mata kyau ajiki, wani ɗan madaidaicin vail me kalan ja ta ɗauka haɗe da rufe jikinta, duk da kuwa cewa kayan yana da ɗan kwali, sai dai bazata iya tafiya daga ita sai wannan rigan agaban Doctor ba saboda sosai hips ɗinta suka bayyana, ga shi breast ɗinta sun bayyana kansu ta saman rigar kasancewar wuyan rigan yana da ɗan faɗi. Da turaruka masu daɗi ta feshe jikinta… A hankali ta buɗe murfin ƙofar ɗakin tafito, ɗan tsayawa tayi tana kallonsa,, kwance yake akan kujera yayinda idanunsa ke a lumshe, yasha adonsa cikin wata bugaggiyar shadda blue colour. Murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau, sosai kuma hasken fatarsa yasake bayyana acikin blue ɗin kayan. A hankali tashiga takawa har zuwa tsakiyar falon, ƙarewa falon kallo tashiga yi, ita dai haryanzu bata gamsu da cewa wai nan ɗin falon ta bane, koda wasa ma bata taɓa tunanin zata shiga cikin daula irin wannan ba,, bata ankara ba saiji tayi anriƙe mata hanu, da dauri ta juyo don batayi zaton idonsa biyu ba,, Murmushi yasakar mata haɗe da cewa,
“yaushe kika tashi?” yayi tambayar kamar bashi yaganta ɗazu ba..
Zama tayi akan kujera haɗe da cewa ” banjima da tashi ba”
Tashi yayi daga kan kujeran haɗe da kama hanunta, kaitsaye haɗaɗɗen darny area’n dake cikin falon yanufa da’ita, jawo kujera ɗaya yayi daga cikin kujeru huɗu dasuka ke waye wani babban table, zaunar da’ita yayi haɗe da buɗe wani babban food flask, plate ya ɗauka yazu ba mata soyayyen dankalin turawa’n dake cikin kulan (Chips) wata food flask ɗin yasake jawowa pepper chicken ne dayasha albasa, shima zuba mata yayi haɗe da haɗa tea acikin wani cup, turo mata duka plates ɗin dakuma cup ɗin tea ɗin yayi gabanta,, saurin ɗago kanta tayi ta kallesa, kansa ya jinjina mata alamar koma me take tunani hakane, take ta shagwaɓe fuska haɗe da cewa “Bazan iya cinye duka wannan abincin ba yamin yawa”
“Bakomai kici sosai, nasan kinajin yunwa” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin barin wajen.
“Kai kuma fa?” batare da ta shiryawa fitowar tambayarba, saikuma bakinta yayi saurinfurtawa,, tsayawa yayi da tafiyar haɗe da juyowa, murmushi yayi mata haɗe da cewa “Ni bayanzu zanci ba” harya fice daga cikin falon bata ɗauke idanunta daga kansa ba,, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da ɗaukan fork tasoma cakan chips ɗin tana kaiwa bakinta, dama yunwa takeji sosai,, sosai taci chips ɗin saidai tea ɗin sama sama tasha shi, naman kuwa ko taɓa shi batayi ba, domin ita gaba ɗaya naman kaza baiwani dameta ba, tafison gasashshen naman sa, fiye da na kaza, sai da taji cikinta yayi haniƙan kafun ta kimtsa wajen haɗe da miƙewa takoma cikin falon,, haryanzu dai idanunta basu ƙoshi da ƙarewa falon kallo ba, rayuwa kenan wai yau ita Zahrah ce zaune acikin wannan katafaren gida dasunan gidan aurenta, ita da ko gado bata dashi akan zallan ƴar katifa take kwana sai gata yau ta kwana akan haɗaɗɗen gado harda lallausan bargo da ta rufa dashi,, a hankali ya turo ƙofar falon yashigo, wayarsace riƙe a hanunsa yana latsawa,, gaf da’ita ya zauna har kafaɗunsu suna gogan na juna, hanunsa ya sanya ya shafi ɗa kalallen cikinta, “Wannan ɗan ƙaramin cikin baiƙoshi ba”
Murmushi tayi masa haɗe da waro idanunta “Dan Allah kayi haƙuri wallahi na ƙoshi” tafaɗi haka tana me ɗauke hanunsa daga kan cikinta.. Kallonta yashigayi yana me karantar yanayinta yayinda ita kuma tayi ƙasa da kanta, batason haɗa idanu dashi kwata kwata, “taso muje” yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, babu musu ta miƙe, hanunta ya kama suka nufi wata ƙofa dake cikin falon, key ya sanya ajikin ƙofar ya murɗa, tura ƙofar ɗakin yayi, still hanunta na riƙe acikin nasa hanun suka kutsa cikin falo’n, falone ma dai-dai ci wanda aka kewaye tsakiyansa, da wasu kujeru dark purple masu kyau, yayinda tsakiyar falon kuwa aka cike sa da wani ɗan madaidaicin chanies carpet dark and light purple colour, wasu labulaye masu kyau kalan light purpule su suka ƙawata jikin ƙofa dakuma windown falon, wani ɗan ƙaramin plasma ne maƙale ajikin bangon falon, su kenan iya abun dake cikin falon amma kuma duk da haka falon yayi kyau, kasancewar kalan kujeru da labulayen kalane me ɗaukar hankali, ga kujerun sunsha pillow ƴan ma dai-dai ta gwanin ban sha’awa, yana riƙe da hanunta suka kuma shiga cikin wani ɗaki dake cikin falon,, gadone me kyau irin na zamani da drower’nsa me ɗauke da murafe shida, sai kuma su dressing mirror dakuma abun aje takalma da jaka,, kayan furnitures ɗin bawasu masu tsada bane daga kujerun har gadon bazasu wuce dubu ɗari huɗu ba, amma kuma anyi kayan da kyau da kuma inganci,, kallon sa Zahrah tayi alamar tanason ƙarin bayani,, murmushi yasakar mata haɗe da sa hanu ya shafa kumatunta, yace da’ita
“Kayan ɗakin da Baffa yayi miki ne”
Daɗi da farinciki ne suka cika zuciyar Zahrah take tacigaba da wurga idanunta tana kallon kayan, Allah sarki Baffa ashe haka yayi mata ƙoƙari batasani ba, lallai Baffa yafaranta ranta sosai, bata taɓa tunanin zata samu kaya haka ba, ashe dai Baffa yanasonta yana kuma ƙaunar fitar da’ita kunya, lallai wannan kaya sunfiye mata komai, saboda koba komai zata tsallakewa gorin wasu mutanen, wani irin tausayin Baffan nata ne taji ya sake ɗarsuwa aranta,, duk da cewa shiba mawadaci bane amma yayi ƙoƙari ya wadata ta da kayan ɗaki masu kyau dai dai da me rufin asiri, babu abun da zatace da baffanta sai godiya,, kan gadon taje ta zauna tana murmushin jin daɗi, sai taji tafi ƙaunar ɗakin ma fiye da wanda aka kaita daga farko, duk daɗin kyauta dai baikai ace da kuɗinka kacire ka saya ba.
“Yanaga kin wani zauna madam? taso muje nunamiki kawai nayi, bawai nace anan zaki zauna ba” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa alamar takama sutafi,,
Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da kwantar dakanta gefe
“Nidai nafison nan please kabarni anan!” taƙare maganar cike da zallan shagwaɓa..
Takowa yayi yazo gaf da’ita haɗe da sanya hanunsa ya ɗago kafaɗunta.