NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Nan ɗakin hutawan kine, can kuma ɗakin aurenki ne ɗakin dana zaɓa mana ni dake domin muyi rayuwar auren mu, kodai baki yaba da zaɓin nawa bane? kokuma baki amshi kyautar danayi miki bane?” 

Ɗara ɗaran idanunta ta ɗago ta sauƙesu akan nasa idanun,  kanta ta girgiza cikin sanyin murya tace ” Ba haka nake nufi ba, kuma nayarda da duk inda kazaɓamin zanyi rayuwa aciki, kayi haƙuri idan maganata ta ɓata maka rai ban…..”

“Shiiiiii” ya katseta ta hanyar ɗaura  hanunsa akan laɓɓanta,  jawota jikinsa yayi , haɗe da sanya yatsarsa yashiga zagaye ɗan ƙaramin bakinta,,  ƙasa tayi da’idanunta domin kuwa bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba,  sake matso da fuskarsa yayi daf da tata har numfashinsu na’iya gauraya waje guda, yayinda dogon hancinsa ke gogan nata hancin,  atare suka lumshe idanunsu,   ahankali laɓɓansa suka sauƙa akan nata laɓɓan, baikai ga soma yin kissing ɗinta ba ƙaran wayarsa ta karaɗe cikin kunnuwansu, da sauri ya sake ta,haɗe da sanya hanu acikin aljihunsa ya ciro wayarsa dake ta faman ƙara, katse ƙiran yayi haɗe da kashe wayar baki ɗayanta ya kuma maidata cikin aljihun rigansa.

Hannayenta dake cikin nasa hanun ya murza haɗe da ɗanyin ƙasa da murya   “Kibani aron 1 hour inaso in ɗan fita”

Batasan lokacin da ta ɗago kanta ta kallesa ba,  mamaki ya bata wai ta basa aron 1 hour shida ƙafarsa ae bazata ɗaure saba, 

Baijirayi abun da zatace ba yakama hanunta suka fice daga cikin ɗakin, direct asalin falonsu suka dawo,  matsawa kusa da’ita yayi ya manna mata kiss akan goshinta, haɗe da cewa “Sainadawo” adawo lapia tayi masa cike da kunyar sunbatar da yayi mata agoshinta,, tanajin tashin motarsa ta sauƙe ajiyar zuciya haɗe da zama akan kujera tamaida hankalinta ga tv, a zuciyarta kuwa hamdala take da Allah yasa bai sumbaceta ɗazu ba,  itakam matuƙar kunyarsa takeji, sosai yakeyi mata kwarjini acikin idanunta…..


GERMANY

Tunda suka iso cikin ƙasar suka kuma sauƙa ababban asibitin dake cikin birnin Germany ɗin Zaid bai buɗe idanunsa ba, duk da kuwa irin kulawan da ƙwararrun likitotin asibiti’n suka basa,   bawai baya cikin hayyacinsa bane,  sarai yana a cikin hayyacinsa, ƙunci da kuma tarin damuwa me tsanani ne suka hanasa buɗe idanunsa,  baison ya buɗe idanunsa kunnuwansa su jiye masa labarin cewa anɗaura auren Zahrah, baya buƙatar yin tozali da fuskar kowa acikin duniyar nan idan ba fuskar Zahrah ba,, yagama yarda da hukuncin da zuciyarsa ta yanke masa, lallai kwanciyarsa haka baida wani amfani, yakamata ne yatashi yayi yaƙi don samo soyayyar Zahrah,  idan har bai manta da date ɗin daya gani ajikin katin auren ba, to jiya ne ɗaurin aurenta,  wasu irin hawaye masu zafin gaske ne suka silalo daga cikin idanunsa haɗe da gangarowa tagefen kumatunsa,, a hankali ya ware idanunsa da suka jima da rikiɗewa suka zama jajur dasu,  baya tunanin zaisake samun farinciki acikin rayuwarsa matuƙar yarasa abar ƙaunarsa Zahrah,  tashi yayi zaune haɗe da rumtse idanunsa, ƙuna yakeji acikin ƙirjinsa sai dai kuma zafin wannan ƙunan baikai zafin ƙunan da soyayyar Zahrah keyi masa azuciyarsa ba,,,  Alhaji Ma’aruf dake tsaye a wajen ɗakin da Zaid ɗin ke kwance, ta cikin makeken    glass ɗin daya zamewa ɗakin window ya hango  Zaid ya tashi zaune, da sauri yaje ya ƙira Doctor domin kuwa tunda suka zo Zaid ɗin bai motsaba sai yanzu,,  ƙa’idansu ne idan zasu duba marar lafiya babu wani me shiga kansu harsai   sun ga babu wani matsala sannan zasu bar ƴan uwansa suje kansa,,  hakan yasa dole Alhaji Ma’aruf ya dakata daga waje likitan shi kaɗai ya shiga..    Bayan kamar wasu mintuna likitan yafito yabawa Alhaji Ma’aruf daman ganin Zaid ɗin, ae ba’iya Alhaji Ma’aruf kaɗai ba hadda Mum suka rankaya zuwa cikin ɗakin,,  har gabansa dukansu suka ƙarasa, hanu Alhaji Ma’aruf ya ɗaura akan kafaɗan Zaid haɗe da cewa “Ya ƙarfin jikin naka?”

Bai amsa musu ba saima kallonsu daya shiga yi kamar wani wawa… 

  “Ina Zahrah?”  shine abun daya iya fitowa daga cikin bakinsa kawai, saboda shine abun dake cikin zuciyarsa..

Kallon Kallo Alhaji Ma’aruf da Mum suka shiga yiwa juna, sukam dai basuda wani amsa da za su bashi domin kuwa sarai labarin Auren Zahrah ya isa ga kunnensu,  yanzu haka itaɗin matar wani ce, babu amfanin  ɗago zancenta…

Alhaji Ma’aruf ne yayi ta maza haɗe da sauƙe ajiyar zuciya  cike da lallashi  yakuma dafa kafaɗun ɗan nasa        ” Yanzu ba lokacin damuwa bane Zaid, bakuma lokacin daza ka sa kanka acikin ƙunci bane,  kabar maganan Zahrah, yanzu samun lafiyarka yafi komai a wajen mu, idan kasamu lafiya sai ayi abun daya dace amma maganar Zahrah abarshi” Alhaji Ma’aruf yaƙare maganar cikin kwantar da murya.  

Laɓɓansa ya cije haɗe da girgiza kansa
” Bazan taɓa samun nutsuwa da salama ba  Dad har sai Zahrah tazamo tawa,  Inasonta Dad,  so ba irin na wasa ba,  samunta ayanzu yafiyemin komai, taɓa kaji Dad, zuciyata takusa bugawa akan soyayyarta, ba irin bugawan da kasani ba Dad, Bugawa zatayi tayanda bazata sake aiki ba har abada kuwa!” Zaid yaƙare maganar yana me ɗaura hanun Dad ɗinsa akan ƙirjinsa dai dai saitin da zuciyarsa take….

“Baka da hankaline Zaid? ka kosan mekake cewa? wani irin mahaukaciyar soyayya ce wannan? anya kuwa Zaid baka zautu akan wannan banzar soyayyarba?” Mum ta tambayesa cikin yanayi na ɓacin rai, sosai abun nasa yanzu yake sosa mata rai..

“Mutuwa zanyi Mum akan Zahrah zan iyayin komai wallahi dagaske ni mahaukacine akan soyayyarta inason….”

“Kanasonta ko, shikenan tunda baka gujewa saɓon Allah saikaci gaba da sonta idan zaka sameta, domin kuwa yanzu ta riga da tayi maka nisa, saboda matar wani ce!” Mum tafaɗi haka ta hanyar katsesa daga maganar dayake…

Tamkar sauƙar guduma aka haka yaji sauƙan maganganun mahaifiyartasa acikin kunnuwansa,, kallonsa yamayar ga Dad ɗinsa,,  kai Alhaji Ma’aruf  ya jinjina masa alamar kalaman mahaifiyarsa gaskiya ne..

“Zahrah zata dawo gareka idan har Allah ya rubuta cewa itaɗin matarkace, amma yanzu kacireta acikin zuciyarka, saboda ahalin yanzu Zahrah tajima da zama mallakin wani,  kasani kuma tunata da kuma cigaba da sonta zai iya jefaka cikin halaka”  Dad yafaɗi haka ga ɗannasa cikin tsananin tausayawa…

Dafe ƙirjinsa yayi da sauri haɗe da cije laɓɓansa,  da ƙyar ya’iya motsa laɓɓansa  aniyarsa yafurta wata kalma, sai kuma labari yasha banban, tarine ya sarƙesa, take jini yasoma fitowa daga cikin bakinsa,  ƙoƙarin riƙesa Dad yasomayi amma kuma kafun yakai ga riƙesa tuni yafaɗo daga kan gadon, Mum kuwa tuni tafice aɗakin taje taƙira Doctor’s,,  kafun Doctors ɗinma suzo tuni Zaid yayi mugun fita acikin hayyacinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata gaban rigar dake jikinsa, idanunsa ne suka juye   wani irin numfashi yaja me sauti, saikuma komai  na jikinsa yasake alokaci guda, daidai lokacin Likitoti suka ƙaraso cikin ɗakin ….  Taimakon gaggawa suka shiga bashi don ceto rayuwarsa cikin ikon Allah kuwa suka samu numfashinsa ya dai-dai ta, allurai suka narka masa wanda zasu sanyasa bacci…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button