BidiyoLabarai

Sojoji sun bude wa mata ta wuta bayan sun nemi ta yi tsirara ta ki, Sheikh Ibrahim Zakzaky

Sheikh Ibrahim Zakzaky shugaban mabiya shi’a na Najeriya gaba daya ya bayar da cikakken labarin artabun su da sojoji.

A wata hira da BBC Hausa ta yi da shi, ya shaida yadda sojoji suka halaka daruruwan mutane kafin su isa dakin da yake zaune da matar sa da yaransa na cikinsa 4.

Kamar yadda ya bayar da labarin, bai san irin yawan harsasan da sojoji suka harba masa a cinyar sa ba, don sai da ta ka ga dagargajewa.

Ya kara da bayyana yadda sojojin suka nemi matarsa ta yi tsirara amma ta ki amincewa, hakan ya hassala su suka bude musu wuta.

A cewarsa:

“Sun kama maza, mata da yara. Daga baya suka saki yara da mata, sai da ta kai ga saura maza 163 wadanda suka wuce Kaduna da su.

“Daga nan suka tasa keya ta da mata ta suka nufi Abuja da mu. Sun kai mu da farko asibitin sojoji, sannan na SSS. Mun kai wata 3 a asibiti, daga Disamba zuwa March. Domin sun ragargaza min cinya ta dama da harsashi.”

Zakzaky ya ce mutane 4 ne suka tsugunna cikin falon sa suna ruwan harsasai.

Ya ci gaba da cewa:

“Suna zuwa suka ce wa matata, ta cire kayan ta. Tana cewa ba za ta cire ba sai suka ce ‘fire’, suka bude mana wuta. Sai da dakin ya turnuke da harsashin. Sai dai kauri kawai kake ji.”

Ya ce take a wurin suka harbi yaron sa dan shekara 13 a goshi wanda ya fadi ya mutu take yanke.

Akwai yaran sa na cikin sa, maza 3 da mace daya da suka halaka a wurin a cewarsa. Sannan akwai yaran riko da ‘ya’yan ‘yan uwansa masu zama a gidan wadanda duk aka harbe su.

Ga bidiyon nan ku kalla:;

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button